Sashe 40
Mijin Matacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Abban Aryan...." Ta fada bakinta na dan rawa,juyowa yayi ya jingina ya harde hannuwanshi akirji yana kallon ta bayan yayi crossing legs dinsa kamar yadda ya saba tsayuwarsa,kallonshi take yi daga sama har kasa kamar yaune tafara ganinsa, bakin dogon wando ne ajikinsa na sport sai farar t shirt ta kamfanin Adidas kafarshi sanye da takalmi slippers dama shigarshi kenan kullum fari baida kayan da suka wuce wadannan ko meyasa oho,
"Abban Aryan yaushe kazo nan?" Ta bukata bayan ta rufe bakinta da hannayenta,
"Kina can duniyar tunani...... Tunanin saurayinki wanda na rabaku kike yi ko?"
Sake rufe idanuwanta tayi da dukkanin tafukan hannayenta tana girgiza masa kai alamar A'a,
"Fada min gaskiya karki yimin karya...."
"Hmmmm" tafada tana gyara tsayuwarta,
"Nasan zafin rabuwa da masoyi.... Nasan irin radadi da azabtuwar da zuciya kan shiga aduk lokacin da ka rasa wanda kake so..... Nasan kema acikin wannan yanayin kike rayuwa ahalin yanzu..... Har yanzu kina kukan rabaki da masoyinki da nayi...."
Lumshe idanuwanta tayi take wasu hawaye suka gangaro mata wanda ba na komai bane face na tsantsar soyayyar da take yimasa,inama zata iya,inama tana da dauriya da kwarin gwiwar da zata iya duban kwayar idonshi ta fada masa ita shi take so shi take kauna ba waninsa ba,inama,zata iya kallonsa cikin ido ta sanar dashi akansa ne zuciyarta ke shiga duk wadannan abubuwan da ya zayyana,
Ganin hawaye na bin kumatunta ya sake tabbatarwa da kansa cewa abinda ya fada ko kuma yake hasashe gaskiya ne domin gashi nan har kuka take yi saboda fama mata raunin dake zuciyarta da yayi,
"Hmmmm...... Wai meyasa masoyi bai fiya kasancewa da masoyinsa ba har tsawon lokacin da yadace?..... Me yasa aduk lokacin da kake tare da masoyinka sai wata k'addara ta rabaku?...... Meyasa yawancin masoya basa samun happy ending?......"
Kawar da kansa yayi ya furzar da wata zazzafar iska kwayar idanuwanshi har ta sauya daga launin fari zuwa ja, karfen wurin ya dafa yana jin tamkar ya fashe da kuka,ita kuwa Hanan dama kukan take wanda zata iya kiranshi da kukan bakin ciki wai Khalil shi duk azatonsa kukan soyayyar wani take yi ba soyayyar shi ba,meyasa yakasa ganewa cewa ita shi take so? Wanne irin makaho ne shi da ya gagara gane tsantsar soyayyar da take cikin idanuwanta wanda take yimasa?
"Kiyi hakuri kowa da yadda Allah ke tsara masa rayuwar sa.... Wasu masoyan sukan kasance da juna tamkar tif da taya ko kuma kamar wata da zara amma lokaci guda sai wata k'addara ta rabasu.... Babu abinda yafi zama da masoyi dadi nasani..... Sannan babu abinda yafi rabuwa dashi daci,tashin hankali da shiga damuwa.... Nasan kina cikin damuwa amma ki kara hakuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo karshen zamanki atare damu...."
Wata faduwar gaba ce tasoma ziyartarta jin abinda yafito daga bakinsa wai karshen zamansu,ita da take fata da burin kasancewa tare dasu har karshen rayuwar ta amma yana yimata maganar rabuwa da ita,bata san lokacin da kuka ya subuce mata ba.... Dagowar da zatayi taga wayam babu Khalil babu alamarsa har yabar wurin,da kuka ta koma dakinta ta fada kan gado taci gaba da rusar kuka.
Shima Khalil cike da damuwa yashiga sashensa ya yada zango a falonsa ya zauna cikin tsantsar damuwa da radadi,wai ma meyasa yabi ta son ran Aryan ya auro yarinyar nan? Meyasa ya rabata da masoyinta wanda take so dan kawai biyan bukatarshi alhali kuma yasan zafin radadin rabuwa da wanda kake so? Shi dai gashi Ramlat bata raye amma kullum cikin damuwar rashinta yake wani lokacin har zubar da hawaye yake yi to inaga Hanan wacce ita masoyin yana raye amma aka rabata dashi ai dole tayi kuka idanma akwai abinda yafi kuka dole tayi,
Zamewa yayi ya kwanta kan doguwar kujera idanuwanshi suna kallon sama, tambayar kansa yake shin menene mafita?
"Ka saketa kawai...."
Zuciyarshi tabashi amsa tana sake karfafa masa gwiwar aikata hakan domin hakan shi kadai ne mafita kawai,sabanin haka kuwa zai sa yazama azzalumi mai son kansa kuma marar tausayi,tashi yayi dakyar ya nufi cikin daki zuciyarsa na raya masa wani abu..........................âœï¸
*_Ummi Shatu_*👌ðŸ»
8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: 36
***Tafiya yake yana hada hanya har yasamu ya cimma lafiyayyen gadonshi wanda yasha shimfidu masu laushi sannan ga pillows nan sama da guda goma manya da kanana kuma kaloli daban daban,
Zama yayi akai sannan ahankali ya zame ya kwanta yana jin jikinsa duk asanyaye, agogon dake ajiye kan bedside drawer dinshi ya kalla nan yaga karfe 11:30 yasan dare yayi amma yazama dole ya kira Khalid acikin daren nan ba sai zuwa gobe ba,yana da bukatar neman shawarar sa da kuma jin ta bakinsa kafin ya zartar da hukuncin da yake ganin shine daidai.
Kiran layin Khalid yasoma yi yana jin zuciyarsa kamar zata fashe dan tsabar nauyin da tayi masa,cikin dan magagin bacci Khalid ya daga wayar,
"Khalid zan saketa...." Shine abinda kunnuwan Khalid suka jiye masa ai bai san lokacin da ya wartsake ba yayi zunbur ya tashi yabar cikin bedroom dinsu gudun kada ya tada Muneerat,a falo ya zauna sannan cikin damuwa yace,
"Khalil what are you saying?...... Me ya faru?"
"Khalid zan saki yarinyar nan kawai inaga hakan zai fi...."
"Wai meya faru? Wani abun tayi maka mai girma har haka?"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi zaune ya dafe kanshi da hannunshi guda daya,
"Babu abinda tayi min kawai dai naga kamar na shiga hakkinta ne kuma na zalunceta domin na kawota gidana na rabata da wanda take so...."
"Itace ta fada maka haka?" Khalid ya bukata,
"Ba ita ta fada minba amma dai kamar alamun hakan sun bayyana atattare da ita...."
"Kaga malam wannan ba hujja bace, bai kamata ka yi haka ba kaifa babban mutum ne Khalil karka manta, yanzu gaba daya idanuwa akanka suke da zarar kayi abinda bai kamata ba za afara yadawa ana yin yamididi da kai.... Ai gara ka ci gaba da zama da ita har zuwa ranar da zata mance da masoyin nata akan ka saketa ka mayar da ita yar karamar bazawara..... Khalil kasan zawarci kuwa? Kasan radadin da iyaye ke ji aduk lokacin da aka sakar musu yaya? To Wallahi duk amincin da ke tsakaninku da mahaifin ta daga ranar da ka sakar masa 'ya shikenan sai wani kadari na Allah kuma.... Kayi tunani"
Shiru ya dan yi na wani lokaci tabbas yasan abinda Khalid yafada gaskiya ne to amma ya zaiyi da halin damuwar da ya jefata? Idan har ya zama silar rugujewar farin cikinta bazai taba yafewa kansa ba,
"Kayi hakuri ka kwanta ka manta da kowacce irin damuwa ka samu bacci brain dinka ta huta inyaso gobe sai mu karasa magana....."
"Shikenan Khalid thank you, thank you for always being with me.... Indeed I have no words to thank you.... Sai da safe"
"Don't mention it Khalil,you are always welcome...."
Katse wayar Khalil yayi sannan cikin karfin hali yasamu yayi addu'ar bacci ya kwanta wai ko Allah zai sa yasamu bacci,duk tunane tunanen da ke zuwar masa cikin rai a daidai wannan lokaci kin yi yayi da haka yasamu bacci yayi gaba dashi.
***
Sosai sumayya taga alfanun daukar shawarar muhibba da tayi,ita kanta bata taba sanin tana da kwarin gwiwar iya yin haka ba sai yanzu,gaba daya ta fita sabgar mujahid babu ruwanta dashi wani lokacin ma shine zai yita takalarta har yasamu suyi fada,fada kam yanzu tsakaninsu kullum ne babu ranar banza da zata zo ta wuce basuyi wannan fadan nasu na sabo ba,
Sai dai kwana biyun nan yanzu ba sosai yake ganinta ba sakamakon exams da suka fara a makaranta,kullum tana cikin makaranta suna karatu bata dawowa gida da wuri,ranar da suka gama exams kuwa aranar ta tattara ta tafi katsina gidan iyayenta, mujahid duk sai yaji gidan babu dadi musamman ma idan yana son abu to sai dai yasaka yar aiki ko kuma yayi da kansa haka ma aikin nata da take yi wani lokacin mami shi take sawa yanzu yauma shi yayiwa mami guga ya goge mata kayanta duk gugar gashi babu dadi stones everywhere injishi da fada,tun yana daukar abun da wasa har yaga bafa na wasa bane,dan haka yacewa mami wai zaije ya dauko sumayya a katsina,ranar da safe ya shirya yatafi bayan yasha manyan kayansa brown colour din shadda da hularta,baisha wahalar samun gidanba saboda dama ya sanshi suna zuwa tare da mami,har ciki yayi sallama ya shiga sumayya na ta shan bacci a falo tana kan doguwar kujera,kafarta ya buga nan tayi firgigit ta juyo kamar a mafarki taganshi tsaye,
"Tashi mu tafi....."
Mutsuttsuke idonta tayi tana son gasgata shin dagaske mujahid ne ko kuwa mafarki take yi?
"Nine nan daina wani kallo na"
Dan turo baki tayi ta zuro kafafunta kasa tana harararsa.
***
Kamar yadda Khalid yafada masa washe gari wasai yatashi zuciyarsa babu wani sauran damuwa ko gurbataccen tunani haka itama murar tashi yau ya danji dama dama shiyasa ma ya shirya yafita office,ita kuma Hanan da damuwa ta wayi gari duk abunda takeyi tana yinsa ne cikin rashin walwala, wai meyasa ya kasa fahimtar ta ne? Meyasa yakasa gane son da take yimasa duk nauyinsa? Ranar dai haka ta wuni babu farin ciki dan adaki ma ta wuni taki fitowa,
Tsawon Kwana biyu basu hadu da Khalil ba gashi ita kuma gaskiya ganin gida ta ke son taje tayi domin zamanta anan bata ga abinda take tsinanawa ba inbanda zaman kashe wando babu abinda take yi. Waya suka yi da anty badi'a nan take fada mata cewa tana son ta dan shiga makarantar koyon abubuwa irinsu hada sabulai,turaren wuta da sauransu koda kuwa irin na online dinnan da akeyi ne shine anty badi'a ta hada ta da wata mata wai ita hajja hasinah kwararriya wurin koyar da mata abubuwa daban daban,kuma wani abun dadi ma kina zaune daga gida zaki koyi abubuwa masu tarin yawa matsawar kin maida hankali. Zunzuruntun kudi ta biya har naira dubu ishirin tayi registration saboda online classes ne nan hajja hasinah ta sakata a cikin group inda aka fara gudanar da lectures,irin tsarin yanda ake koyarwar abun yayi mutukar burgeta domin ana yin komai dalla dalla yanda zaka gane kuma ka fahimta,