← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 97

Sashe 95

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai around 11 Gwaggo takado Nura da karfi da yaji yabar asibitin badan yasoba flat din Ummi yawuce duk idanunsu Hajiya biyu basuyi bacci ba yadan zauna yana hira dasu Hajiya tace “tashi kaje ka kwanta kahuta Nura” baiyi musu ba yawuce bayan yamusu sallama yafita yawuce flat din Hadiza falon a gyare tsaf, Hadizan yagani zaune afalon ga laptop dinta tasaka reading glasses sai yau take duba harkan shagonta tana ganinshi ta ijiye laptop din ta mike saikuma ta tsaya tace “sannu da zuwa” dan murmushi yamata ya maida kofan yarufe yatako anatse zuwa inda take ahankali yace “lemme hug my wife da warin asibiti” sai kawai ya rungumeta murmushi tamai tace “my husband smells good” yadanyi one minutes ahaka sannan yasaketa zai wuce sama da sauri tace “akwai dinner zakaci ko zakasha tea”? Ahankali yace “make tea for me cus it’s late ki kawomin dakina bari na watsa ruwa” sama yawuce direct dakinshi dan kowani flat yanada dakinshi yafada bayi wanka yayi damuwa yamai yawa daurewa kawai yake fitowa yayi daure da towel yaga Hadiza takawo tea pajamas yasaka ya feffesa turare sannan yataho gently yazauna kusada ita yadauki mug na tea din yace “thank you Didi” murmushi tamai tana kallonshi yanashan tea ahankali harya gama tashi tayi tace “bari nakai kitchen” shima tashi yayi yace “bari naduba yarana” tare suka fito dakin Aman yafara shiga dake bacci ya duddubashi yamai addu’a sannan yawuce na Amali itama yamata addu’a yafito saiya bude dakin Hadiza ganinta yayi ta kwanta agado ahankali yace “taso muje mu kwanta” batai musu ba tasowa tayi tana tafiya yana binta da kallo har saida tazo dab da shi hannunta yakama yatayata kashe wutan dakin sannan suka wuce dakinshi kashe wuta yayi ita tafara shiga cikin gadon shima yahayo ya kwanta tareda jawota jikinshi faduwa gabanta yayi tanaso tayi gyara kafin wani abu ya shiga tsakanin su she prays bazai mata komiba.
Ijiyan zuciya yasauke ahankali kafin yakai hannunshi yasa a tsakiyan nata suka hade murya Chan kasa yace “my Didi” ahankali itama tace “my Nuri, menene? Meke damunka? Menene matsalan Mijina? Talk to me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yasake shigewa cikin jikinta da kyau kaman bazaice komiba chan yace “I haven’t told anyone but inaso nakai Ummi either Egypt ko India duk Wanda yarıga fitowa what do you think?” Ahankali tace “yes nima zanso hakan sabida a dubata da kyau and manage her harta haihu” Ijiyan zuciya yasauke yace “zaki dagamin kafa?” Dasauri tace “of course Nuri” murmushi yayi yace “I love you my stubborn wife” dan murmushi tayi tace “ai ka horani bazan karaba” saitai dan shiru kafin chan tace “Nuri” ahankali shima yace “Didi”. Labarin Zeenah tabashi tundaga kan case na kotu har karshe tace “Nuri I’ve been a fool, is just like abinda Anty Jams tace I am just a fool wawiya mara wayau all abinda na iya is ihu da zagi Zeenah ta cutardani Nuri she made me believe in feminism kaman an juyamin brain na zauna kan abin kaman nina kawo feminizm duniya amman nida feminizm har abada Nuri I sincerely apologize for all the pains I’ve caused you can u find a place in your heart to forgive me?” Ahankali yakai hannunshi saman fuskanta dudda baiji karan kuka a yasan hawaye yazubo dağa idanunta ahankali yace “komi daya faru between us is destiny, haka Allah ya kaddara, duk Wanda zaiyi kuskure yagane ya gyara mutum ne, babu wanda yafi karfin jarabawan ubangiji nayafe miki itakuma Zeenah Allah zaiyi maganinta ki barta da halinta delete her number bansonki da any kawa again, and your business kicigaba but anything 3 daga yanzu nakeso ki dinga dawowa gida, and weekends that’s Saturday and Sundays is for me nawane banso kina zuwa shago ranan kinji you can hire more staff to handle your work, and yarana give them your time and affection I wants Aman and Amali su soki sama da yanda suke sona make up for your mistake ki gyara tsakaninki dasu kija yaranki ajiki kinji Hadiza” gyadamai kai tayi ahankali, tace “thank you Nuri you are the best husband” ahankali yace “u are the best wife” hamma yayi, ahaka yana manne da ita bacci yayi awon gaba dashi.

Almost 1months Ummi tayi anan asibitin aka gama processing komi cikin kannin Nura Ya Aisha ne kawai bata zoba itama sabida Egypt za’a kawo Ummin nan but duka kannen Nura sunzo nan da nan aka saman ma Ummi da Gwaggo komi suka wuce Egypt itakuma Hajiya tawuce kano da kannin Ummi da Meena Nura yarığa ya barmata kudi yanaso takai yaran boarding school mai kyau yama gayama Gwaggo bazai yarda ta aurar dasu yanzu ba washe garin ranan dasukaje Kano Hajiya takaisu school hadadde akai komi suka dawo gida dan amusu shopping akaisu school zasu fara JSS1 dan Gwaggo da Ummi bazasu kara dawowa Nigeria ba sai bayan Ummi ta haihu.
Gidan Abuja yarage Hadiza kadai da yaranta.
Dudda Nura baiso yasauka gidan kanwarshi ba but mijin Ya Aisha yace bai isaba daka shi ma yadaukosu airport Gwaggo idanunta sun kuşa faduwa akasa.
Sosai Ummi tasami kulawaa asibitin da aka kaita nan ma wata daya tayi tasoma motsi da kafa da hannun ba sosai ba aka sallameta lokacin cikinta na wata biyar aka hadasu da home nurse dake managing Ummi agida 2/4/7 ga Gwaggo ga Ya Aisha shikuma Nura yabarosu yadawo Nigeria yasan Hadiza tai kokari haryau babu abinda ya shiga tsakaninsu rashin lafiya Ummi kaman ya ciremai sha’awa gabaki daya ajiki abinshi ma bai aiki yanzu dayaga tadan Soma miydi da kafa har an sallamesu yasa hankalinshi yadan kwanta.
Chapter 95 · 0% Book details