← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 97

Sashe 2

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Parking yayi agaban wani babban gida wajajen 2 nadare. Sauka yayi yana kallon wata sabuwar red 2024 Toyota grand highlander dake pake akofar gidan duka duka last month ya chanza mata mota 2023 Toyota Camry hybrid wato bai mataba shine maybe ta saida tasayo wani, dan murmushi yayi yawuce yana ciro key dinshi yabude kofan yashiga ciki yamaida kofan yarufe yajuyo yakunna wuta lafiyayyen hadadden classic falo ne, ijiye key yayi kan tray dasuke ijiye key yaduka yacire covershoe kafanshi yasake juyowa yabi falon da kallo dayake tsaf tsaf banda motan Aman dake kan kujera hannu yasa yakashe wuta sannan yawuce yahau stairs harya fara tafiya yaji kukan Amal chak ya tsaya cus badaga sama yakejin kukan nan ba and dakin Amal na upstairs, shiru yayi jin magana kasa kasa. “sorry Amalulu, Amalilin Mommy, Amalilin Aman, Amalulu na Amalulu yar lukuta, kiyi bacci zakiji sauki gobe kinji, zazzabi ne saina zane zazzabin nan dake damun mini yarinya na” muryan Amal yaji tafashe da kuka sosai cikin muryan yara tace “Momyyy” dasauri yajuyo yashiga saukowa daga staircase direct hanyar dakin yar aikinsu yayi dake kusada store room na gidan, tsayawa yayi gaban dakin yasa hannu yakunna wutan wajen sannan yayi knocking kofan tareda bude kofa atare dasauri sabida yanda yakejin kukan Amal, wata yar budurwa ce doguwa tsaye tagoya yar yarinya dabazata wuce 2yrs ba abayanta, wata yar karaman katifa ne adakin ta yan boarding sai ganamasgo saikuma kwalayen magunguna da flask na ruwan zafi da gwangwanin cerelac da bowl da spoon duka akasan dakin, adan tsorace yar budurwan ta duka kasa goye da Amal abayanta ganin maigidan dabai taba zuwa nan ba tace “ina yini” gabanta na faduwa dan yaune rana da farko da Baban su Amal yataba zuwa wajen nan, sosai yake kallonta baima tsaya amsa gaisuwanta ba yace “me Amal keyi anan da daddaren nan”? Tana duke akasan still jijjiga Amal dake kuka take abayanta tace “batada lafiyane Alhaji” “Mamanta fa”? Dasauri tace “Anty tadawo daga aiki tagaji bacci zatayi” ranshi abace yace “ita tace ki kawota nan dakin”? Gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tace “eh” “bani ita nan” batai musa ba tashiga kwanto Amal dasauri, yarinyar was looking so weak sai kuka take ta yarda zanin tadauketa ta taso ta taho har inda yake tsaye agaban dakin takawomai ita, itama Amal tana ganin babanta takara fashewa da kuka tace “Daddy” zafin dayaji ajikinta saida yadan firgita ya rungume yarinyar da sauri ajikinshi yace “my princess” yakalli yar aikin dahar takara dukawa anan gabanshi yace “wani magani tasha”? Dasauri tace “Anty tace nabata wayanchan”? Tanunamai magungunan dake gaban katifar ta, Ibuprofen suspension ne dakuma Tuxil D na mura da tari, jiyayi ranshi na tafasa dan yaranshi are his life, cikeda takaici yace “how many mil ma kika bata? Tun yaushe take wajenki”? Dasauri tace “tun wajajen 9 Anty takawomin ita, cikin marfi Anty tace nababbata zatai bacci” “maisa baki kaita da jikinta yayi zafi haka ba akaita asibiti tun 9 har 2 nadare” kanta na kasa still da zuciya daya tace “Anty tace karna kawota bacci zatayi tagaji ta kwana awajena” kallon yar aikin yayi takaici yasa kawai yajuya yawuce yahau staircase rikeda Amal dake kuka sosai ajikinshi, direct dakin Maman yawuce bude kofan yayi kai tsaye yasa hannu ya kunna wutan dakin, wata kyakkywan faran mata ne kwance kan wani makeken lafiyayyen gado tarufa dawani beautiful bargo AC na aiki dan dakin sanyi tana bacci mai dadi, wucewa yayi gaban gadon ya bubbuga filon da kanta kekai yace “Hadiza, Hadiza” firgigit tabude idanunta dasukai ja cikin bacci tabishi da kallo tana mika tana kallon Amal dake kuka sosai tana miko hannu kaman zata kamata, cikin muryan bacci tace “Nuri lafiya zaka kawomin Amal ina bacci batana wajen Ummi yar aikinmu ba pls kamaidata I need to sleep na bala’in gaji wlh” tai maganan tana hamma zata kara jan bargo azuciye Nura ya fizge bargon ya yaye yace “wai what’s is your problem Hadiza? Kinyi neglecting your responsibilities towards me yanzu ma yarana wulakanta mini su zakiyi, this girl is sick baki kaita asibiti ba, baki kirani kin sanar dani ba, kin barma yar aiki ita da magungunan acika marfin idan tai overdosing yarinyar nan fa”? Hamma Hadiza tasakeyi tarufe bakinta sannan tadan yunkuro kadan takalleshi tace “look Nuri banda lokacin fada dakai yanzu Allah ma yasan I don’t have time, dare mahutan bawa ka maidama Ummi yarinyar nan tasan yanda zata kula da ita, she’s great da yara bakaga duk cikin yan aikin danayi tafi dadewa ba almost a year take nema yanzu agidan nan, and my children loves her sosai” wani kalan kallonta Nura yake yace “da ace bani nakaiki asibiti kika haifi yaran nan ba danace banaki bane Amal is just 2 she’s sick crying for you jibi yanda take kuka take miko hannu ki dauketa kina cewa akaima yar aiki, what kind of woman are you da bakijin tausayin yaranki”? “oooohhhhhhhh! Ohh-ho-hooo!” Hadiza tabuga uban ihu tana daura duka hannayenta saman kanta irin ta shiga uku din nan, cikeda gajiya tace “wai all this while so kake muyi fada naki biyemaka cus am busy da work dina baka gabana what’s the meaning na zuwa tashina tsakar daren nan kana neman bala’i na eh? Nace ka maidama Ummi yar aikina Amal for Godsake this is her job we pay for it ba kyauta take mana ba, idan bazaka maidata ba I can call her da wayana tazo sama ta dauketa sutafi, please pls banson problem Nuri, banso, just get out of my room pls katafi dakinka, haa’a kawai katasheni tsakar daren nan da bala’in ka wannan wani kalan neman rashin zaman lafiya ne iyye? Pls kafitan mini daga dakina nace and nagaji nadawo daga aiki ka maidama Ummi Amal she’s good with kids zatasa yarinyar nan bacci pls go away from here” kawai tsayawa Nura yayi yana kallon Hadiza yanda take magana zaka dauka itane mai gidan nan ko itane take putting food on the plate jibi yanda take cemai yafitan mata daga daki kaman itace ke aurenshi ba shi ke aurenta ba, ganin ya tsaya kallonta yake yana jijjiga Amal dake kuka sosai barinma yanda taga Mommy ta na masifa yasa ta buga tsaki. “Mtswwww, kada Allah yasa kafitan nina barmaka dakin, kajika da ruwa kasha” ta tashi fuuu azuciye tasauka daga gadon tawuce tafita daga dakin tana mita,
yana ji tashiga wani daki ta bugo kofan tarufe tana murza key jiyayi kaman an dauramai dutse a kirji kallon Amal dake ihun kuka yayi tana kokarin sauka daga hannunshi tana kallon kofa tana mika hannu tanaso tabi mamanta Ya jijjigata yace “sorry Amal, Daddy’s princess stop crying, muje” wucewa yayi yafita daga dakin dakinshi yaje da ita ya ijiyeta kan gado yawuce bayi yatara ruwa yadawo kayan jikinta yacire mata da pampers yadauketa zuwa bayi wanka yamata tsaf kana ganin yanda yake kasan mutum ne mai tsananin son yara fito da ita yayi daure a towel yawuce yafita yaje dakinta hadadden daki komi pink ga zane komi organize wani shimi yadauko yasamata da pampers yace “zakisha tea Princess”? Girgizamai kai tayi a’a, yace “juice, cheese balls, rice, omelette” gyadamai kai tayi dasauri daya fadi omelette hakan yasa yadauketa sukaje kasa ya kunna wutan falo ya shiga kitchen da ita baimasan ta yanda zai fara mata omelette dinba, tsaki yayi yafito yaje gaban dakin yar aikin yayi knocking bude kofan tayi adan taushashe yace “danzo ki soyama Amal kwai” Amal na ganinta tamika mata hannu dan tadauketa dasauri Nura yace “wait Princess aiki zatayi” dasauri yar aikin Ummi tace “ai na iya aiki ina dauke da ita kawota” dan kallonta yayi sai kawai yabata Amal din ta karbeta tana murmushi ya matsa gefe fitowa tayi tana tafiya tana kallon fuskan Amal tace “namiki omu omu”? Dasauri Amal ta gyada mata kai tace “omu omu” Ummi tace “to muje namiki mai dadi ko”? Amal tasake jinjina mata kai.
[9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: MATAN??? Ko MAZAN???💫

✍🏻M SHAKUR

EPISODE 3️⃣

BONUS💃
Sosai kirjinta yabuga da sauri ta sauke hannayenta kasa tadaina rawan tasauke kanta kasa shima daga kallonshi gabanta nafaduwa dumdumdum.
Wucewa Nura yayi dasauri sama zuwa dakinshi yakasa daina ganin fuskan Ummi dana yaranshi how happy all of them were, yanda itada Aman kema Amal rawa, bayi yafada dasauri ya watso ruwa yafito yashiga shiryawa dan yafita meeting din dayake dashi is by 2, cream yadauka zai shafa saikuma ya tsaya maisa ya kalleta haka smiling ya tambayi kanshi? He was lost dayana kallonta, yar aikinsu ce fa but he was finding all abubuwan datakeyima yaranshi super cute, dan ijiyan zuciya yasauke saikuma yacigaba da shafaman.

Ummi daduk takasa natsuwa itama a kitchen ta tambayi kanta maisa yake kallonta, tun yaushe Alhaji yaganota tana rawa haka? Duk wani kalan kunya kunya da nauyi nauyi taji tanaji, IPad din Aman tadauko ta kunnamusu anan kitchen din dan bazata rabu dasu ba tashiga gyaran gidan duka tanaso tana gamawa tamusu wanka, itama taje tayi saita daura abincin dare.
Chapter 2 · 0% Book details