← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 97

Sashe 21

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da asuba as usual yafito harzai wuce yasauka kasa saikuma yajuyo dan yayadata tama yaran nan abincin school ta shiryasu gaban dakinta yaje tareda bude kofan yashiga ya kunna wutan dakin, bauu dakin yayi haske yatsine fuska Hadiza dake lafiyayyen bacci tayi jin haske, tadan bude idanunta kadan ganin Nura yasa cikin muryan bacci tace “Nuri am off salat ka tafiyan ka masallaci basaika tasheni ba” yana daga wajen yace “get up fix something for the kids and get them ready for school sannan basuyi home task nasuba, and arrange the house yayi datti gidan” wani kalan ware idanunta Hadiza tayi tasss takalli sama saikuma ta tashi zaune da sauri ta kakkalli gefe da gefenta dan she wanna be sure cewa bada ita Nuri yake ba ganin bakowa adakin yasa tanuna kanta da sauri tana kallonshi cikeda mamaki tace “Nuri ni kake bama order haka kake lissafo ma ayyuka haka?” Duk yanda taso kasa rike dariyan datakeji tayi tadan kyalkyala dariya tana nuna kanta tace “wait are u mistaking me for Ummi ne or wat dakake lissafo mini abubuwan da zanyi, idanunka gizo suke maka ne Nuri? Nayi kama da yar aikin mu ne? Wait ma kai what happen da u can’t do all of this abubuwan nan daka fadi are you not mahaifinsu? Can’t u cook for them? Can’t you bathe them and get them ready for school? Bazaka iya musu homework nasu ba? Who said shirya yara, basu abinci, getting them ready for school da gyaran gida responsibility mata ne kadai?” Babu wasa kan fuskan Nura yace “ki tabbatar kin tashi kin soma aikin dana fadi kafin nadawo gidan nan daga mosque” yana maganan yajuya yafita daga dakin mamaki yasa Hadiza tama kasa zama tashi tayi dasauri tasauko daga kan gado tafito daga dakin tabiyoshi abaya tace “Nuri ni kake commanding like that are you for real? Kalleni fa” tanuna kanta tana sanye dawasu arnaye kayan bacci tace “do I look like a house help? Listen fa Nuri lemme tell u something ko Allah yasan ni ba housewife bace, I have a business danake managing, I contacted agency masu kawo yan aiki babu wasu akasa za’a nemo mini, idanma zaka zauna and be attending to this children reschedule work naka do it tunda Ummi tatafi garinsu dankai ur company is big kaine CEO kanada manager dazasu iya managing komi niko banda manager, I manage everything about business dina nikadai banda sales girls danake dashi dake attending to customers namu but I do komi dakaina dan haka Nuri attend to ur kids, babu inda aka rubuta a musulunci cewa dolen dole mama ce zata dingama yara komi yaran nan na me and you get them, gaskiya I don’t have that tim…..” ganin Nuri yabude kofa yafita yasa Hadiza ta tsaya turus da mamaki, Nuri just walk out on her tanamai magana irin baida lokacin ta wow! Tana kallon kofan kirjinta na tafarfasa, da tayi niyan ko falon ne tadan tattare suyi sharing work din amman wlh tafasa tayaya zaiki girmamata ita ta girmamashi, wani disrespect ne hakan? Wannan sabon confidence din da Nuri yake mata kodan sabida yaga yasaketa tadawo gidan da next day ne yasa yake mata Iskanci haka, ta inama zata fara all this ayyuka Allah ma yasan bazata iyaba wlh, rabon datayi aikin gida harta manta to tariga tawuce wannan level din nayin aiki dakanta agidanta Allah ma yasani, idan tayi aiki agidan mijinta menene banbancin gidan ubanta da gidan mijinta? Kana gidan iyaye ne u must work, abaka umarni kabi, but your husband house suppose to be your paradise that’s the beauty of aure, kiyi duk yanda kikaga dama agidanki, kici karenki ba babbaka, tanada kudi mijinta nada kudi maisa zata tsaya da kanta tana all this silly household chores? No Nuri u can’t subject to into doing abinda zuciyana baiso yayi, itama shegiyan yarinyar nan akan wani dalili zata sakani in this tight spot, that stupid Ummi datawani tafi shegen kauyensu wai wajen kakanta, juyowa Hadiza tayi tarike waist nata tabi falon da kallo yanda yayi datti ga kwanukan abinci tsaki da ragowan food a dinning tayi tai ihuuu. “Wayyyooooo, Goddddd! A ina zan sami yar aiki yaune ni Hadiza? Ohhhh I can’t do this, how can I start doing this chores haba dan Allah, ai abin kunya ne, niba yar aiki bace ba I can’t do this wlh, ni nama manta yaya ake girki ma, indomie nan koni nakasa ci dana dafa jiya ewww, yuck” ta yatsine fuska, komawa sama tayi dakinta tawuce bayi abinta.

Dawowa gidan yayi around 7 yanda yabar falon haka yazo yasami falon sama yawuce Aman yagani da Amal duk sun zauna anan falon sama sunyi zugum kaman marasa lafiya, ganin babansu dasauri suka tashi sukai wajenshi Aman yace “Dady where’s Anty Ummi”? Amal kuma sai kawai tafashe da kuka tace “Daddy ina Anty Ummi tun jiya banganta ba she’s not in her room” tausayin yaran yaji dasauri yadauki Amal yakama hannun Aman yawuce dakin Amal yarufo kofa yace “Anty Ummi taje garinsu amman zata dawo next week I promise” dasauri Aman yace “daddy ka kaimu wajenta” shiru yayi yana kallon yaran saikuma yaga sun fashemai da kuka dukansu biyun atare dasauri yashiga lallashin su wayanshi yaciro yayi dialing number Ummi yana addu’a Allah sa akunne, kafinma wayan yayi ringin Aman ya karbi wayan yahau kan gadon Amali itama Amal tahau gadon kusa da Aman ta zauna wayan na ringing daya biyu Ummi tadauka cikin sweet voice nata data wani lankwasa ganin number mijinta tace “hello” atare yaran sukace “Anty Ummi” saikuma suka fashe da kuka atare, cikin kuka Aman yace “why did u go to kauye baki gayamana ba”? Amali tace “bakince zakije damu duk randa zaki kauyeba” Ummi jitayi zuciyanta ya tsinke dasauri cikin dabara tace “Aman wait one by one” a cartoon nasu ta koyi kalman, cikin kuka suma yaran sukace “one by one” ahankali tace “Aman daina kuka bari nafara magana da Amal” gyadamata kai yayi kaman yana gabanta cikeda lallashi Ummi jin yanda Amal ke kuka sosai tace “Amalily na, Amalily Dadynta, Yarinyar datafi duka yaran duniya kyau, ga gashi, gata yar fara, baturiya, balarabiya, Princess Amal Nura Wambai ammatana” wani kalan murmushi Amal tayi tana turo baki da saida abin yasa Nura yasaki baki yana kallon ikon Allah yarinyar dake kukane yanzun nan hartai murmushi sabida taji kirari ana cemata Ammata wai tafi duka yaran duniya kyau, gyara zama yayi yana kallonsu cikeda so. Ummi tace “banson Mudi yagane mini ke ne saisa ban gayamiki ba nazo amman zan dawo next week zan kawo miki goruba da aduwa da hanjin ligidi” dasauri Amal tace “tuwon madara fa”? Dariya Ummi tayi tace “harda tuwon madara Amal dina” wani ihu tayi tana tafi Ummi tace “tom jeki brush ba Aman wayan” bawa Aman wayan tayi tasauka dagudu tawuce bayi Ummi tace “takawanka lafiya d’a guda kuma daya tilo ga Baban shi, Mr Aman gogan zamani, matashin saurayi, dogo, yaro ga ilimi ga tausayi, yaron dayafi kowani yaro jin magana da hakuri kaman Baban shi, Amanu Aman babban yaya ga Amalily, haba ama Anty Ummi hakuri mana eh Yaya Aman” dan turobaki Aman yayi yana murmushi sosai yana juya idanu looking super cute ahankali yace “to nayi amman idan kinzo zaki mini Oumu Oumu mai cheese a tsakiya” dasauri Ummi tace “zanyi” murmushi yamata yace “bye bari naje nai brush” yana maganan yabawa babanshi waya yatafi bayinshi cire wayan Nura yayi daga Speaker yakai kunnenshi yadan lumshe idanu yace “nikuma mezan samu nida nafi kowa yin hakuri”? Dan murmushi Ummi tayi cikin wata narkakkiyan murya tace “barka da safiya Baban Aman da Amalily mijin Ummi kuma, ina kwana My Noor” wlh ko baitabajin sanyin dayakeji irin wannan dayakeji ba da gaisuwan nan datamai sai kawai yaji kanshi na kumbura, ahankali yace “Alhamdulillah ya darenki? Yasu Gwaggo? Meya sami wayanki jiya akashe” “Kowa lafiya lau, ba chaji ne, ya jikin Hajiya kuma yau zakuje asibiti?” Gyadamata kai yayi yace “eh zanje nakaita taga Dr” murmushi tayi tace “tom bari na barka kaduba Amal nasan wasa da ruwa take yanzu haka” dudda baiso ba haka yace “to zan kiraki anjima, kema kije kiyi breakfast, agaida mutanen gida” to katse wayan yayi yatashi yawuce bayin Amal shiyama yaran wanka ya shiryasu yadauki akwatin su yazuba musu kaya aciki komi dasuke bukata, yajawo suka fito falo Hadiza na zaune afalo taci uban gayu tasaka hill takada ma kanta tea tanaci da bread kadai anan kan kujera ganinsu duka da akwati yasa tace “ina zaka kaisu naga akwatinan su”? Batare daya kalleta ba yace “inda za’a kulamin dasu tunda bakida lokacin su” kofa yayi tabisu da kallo yaron ko kallonta basuyi ba, saikuma ta tabe baki ita adadinta ma atleast yau zatai zamanta ashigo without tunani su, amota ya lodasu straight gidan Baffan shi yayi dan Hajiya tacema yakawo su nan dan da ita ya tsaya yayi magana awaje kafin ya shigo gidan, akwai kananun yara agidan, anan sukaci abinci aka zuba musu abinci a lunch bag nasu dakanshi yakaisu makaranta sannan yabada addres na gidan kan anan zaa dinga zuwa daukansu sannan yadawo yakai Hajiya hospital.
***
Chapter 21 · 0% Book details