← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 97

Sashe 38

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Da kyar Anty Jams tayi shiru takalli Hadiza dake kuka har lokacin tace “bawai baki nake miki ba but ace yau Nura yarabu dake wlh harki mutu Hadiza bazaki kara samin miji kaman shi ba, kuma idan zakiyi aure dari haka za’a dinga sakoki cus bakene matsalan ba halinki konace sabon halinki ne matsalan, namiji da mace ba daya bane, a man and a woman are not equal stop believing in that stupid theory! A house belongs to a man, gidanshi ne, shiya auroki shiya saki aciki, bakida right or whatsoever kice saida permission naki baki zasu shigo Hadiza, dafa abinci is traditional da globally mata aka barma wannan tradition na girki agida, tundaga upbringing ba’ayin rainon maza to be entering kitchen mata akema wannan training din so akanme zakice shiya shiga kitchen? Ya iya girkin ne? Kula da yara aikin mace ne idan mijinki yatayaki is fine idan baitayaki ba kada kice dole saiyayi dan shine ke fita kullum cikin rana yaje yanemo muku abinda dagake har yaran zasuci, Hadiza dan mijinki yace tashi bani kaza, yimin kaza, zonan, zauna, matsa, baya nufin ya rainaki bane No ya isa ne saisa yabaki umarnin kuma dole kibi, idan bazaki iyabiba idan u can’t subject kanki to follow umarnin mijinki maisa kika aureshi to??? Eh” cikin kuka Hadiza tace “wlh Anty Jams zan chanza nagayamai zan chanza amman yasaki Ummi mucigaba da rayuwan mu mukadai” dan murmushi Anty Jams tayi tace “Hadiza kenan u can’t eat your cake and still have it! Yanzu ace Nura yashigo nan kifadamai maganan nan agaban idanunki zance Nura kada ka saki Ummi” Hadiza nawani kalan kallon Anty Jams tana kuka mai tauna zuciya, Anty Jams tace “Hadiza a rayuwa one cannot always win, tunda kikai aure yau shekara goma going to 11 you’ve been winning akomi nakeda Nura, yanda kikeso haka ke faruwa agidan ki, kika fitini bawan Allah he let u have it ur way, wannan ma ishara ce Allah ya gwada miki dan trust me, Allah ne ya kwadaita ma Nura son ya auri yarinyar nan Nura da bayama kallon mata, rana daya yaga Ummi yaje har kauyensu ya aurota, inaso nagaya miki is too late for you amman I can’t because is not too late for you” Anty Jams tadanyi shiru tace “is too late for you cus Nura yariga ya auri Yarinyar nan ba gudu ba jadabaya, so kike yakoma karamin mutum ya auri yarinya sabida ke da bakimai biyayya ba yasaketa angayamiki batada iyayene? Wasu iyayene zasuso su aurar da Yarinyar su asakota bayan kwana biyu so maganan Nura yasaki Ummi ki manta dashi kawai” taushe bakinta Hadiza tayi dan ihu ne yakeso ya kufcema bakinta, ijiyan zuciya Anty Jamila tasauke tace “abinda nake Nufi is not too late for you shine Nura har yanzu yana sonki sosai, cus namijin dake tsananin sonka ne zaiga halin dakake ciki yabukaci wata yar uwanka tazo just for your comfort, Hadiza har yanzu Kece keda ragaman zuciyan Nura forget ya auro wata Ummi koda tanada wani abu axuciyanshi to akalan zuciyan ne, bazaka iyajan akala abu ya motsa ba amman mai ragama shine keda ikon komi, so Hadiza idan zaki gyara halinki from today ki koma asalin Hadiza da Nura falls for deeply lokacin nan kowa yasan labarin soyayyan ku a kano ki koma i assure u, u will come me to tell me wonders, is not too late for you Hadiza” Hadiza na kuka tace “to mezanyi? Yanzu haka zan zauna yadinga yanda yaga dama dani?” Yayarta na kallon kwayar idanunta tace “kwarai idanma takaki zaiyi yayi ke har kinada baki mutumin daya miki komi, the journey might be tough on you but inhar kika dage mijinki nakine Hadiza” sosai take kallon yayarta, ahankali tanuna zuciyanta tace “anty Jams inaso na tsani Nura so bad sabida auromin Ummin nan dayayi amman nakasa sai kace yamin asiri yanzu nema naji wani kalan sabuwar soyayyanshi nakamani danaga ya auro wata ina masifan jin zafi da kunci ko dakinta da dazu yashiga agabana wlh kaman ana yankani alive mesa nakeji haka? Maisa nakasa fushi namabar shi da yar aikin gabaki daya afterall bana bukatanshi inada kudina dazan iya kula da kaina aduniya, why why why maisa yanzu ne nakejin sabon soyayyanshi araina da inji na tsaneshi?” Anty Jams tace “sabida yanzu ne kikasan menene kikai loosing kokuma nace menene kika bari ya kufcemiki a hannu, all this while ai ina fadamiki kina mugun son mijinki amman kaman bake nake fadamawa ba sai yanzu dayay aure kikejin kina sonshi kawai da hankalinki da karatun ki kin cuci kanki abanza a wofi Hadiza, Hadiza Allah yabaki perfect husband, kinsan maza nawa kenan aduniyan nan da basa ciyar da matayensu sabida sunga matan na sana’a? Kinsan maza nawa ke bama matansu 200 kullum kudin cefane and matan su karba and fix something with it? Kinsan mata nawane da sunma manta when was d last time mazajensu suka musu dinki tun na akwati? Hadiza kinsan maza nawane a zamanin nan da bama su damu da yaran cikinsu da suka haifaba sun barma matayensu yaran sune cinsu, shansu, suturansu harma school feees nasu mazan na nan kuma bawai sun rasa kudin biya bane, Hadiza kinsan mata nawane yanzu that are going through domestic violence, bullying, torture damuwa da rashin sukuni agidan mazajensu from both mijin da yan uwan shi? And all this matan despite everything suna zaune agidan mazajensu despite ba sabulun wanki bana wanka, ba kudin kitso ba kudin kayan salla but ke kinsami everything, banda doraki dayayi akan business yasan kinada kudi baitaba kallon kudinki ba, for once baitaba cewa kuyi sharing bill ba, baitaba kin sayo wani abu ba, yan uwanshi ko mahaifiyarshi basu taba takura mikiba saina girmamawan Matan yayansu dasuke miki not until ranan da kika zagi mahaifiyarsu agaban Meena ta dauki action which I support dan banabin karya, kinsan mata nawa ke neman wannan jindadin dakika samu agidan mijinki? Kinsan how many women out there are dying to be in this position u are?Hadiza jibi rahama da baiwa daban daban da Allah yamiki, which of the favors of Allah can you deny??”Hadiza tai shiru tana goge idanu, Anty Jams tace “all abinda Nura ever wanted from you is just care, care for him care for his kids, attend to him and attend to his kids yataba demanding for more than this?” Girgizamata kai Hadiza tayi tana kuka komi nadawo mata fresh tundaga farko rayuwansu, ijiyan zuciya Anty Jams ta sauke tace “like I said is not too late for you cus Nura namiki wani special so azuciyanshi maybe sabida kene first love dinshi dan haka maza maza ki gyara before u lost him for good kısan inda dare tamiki and I will tell you this again kishiya fa yarıga yamiki, kidauki hakan amatsayin kaddara dakuma hukunci da Allah yamiki abisa laifinki Hadiza ki tuba taubatan nasuha kikuma chanza inba hakaba kindaisan haka nake gaya miki gaskiya baki yarda saiya kwabe miki, inba hakaba Hadiza wlh wlh zaki rasa Nura for life” dasauri Hadiza takalli Anty Jams idanunta sun nuna asalin fear gabanta nafaduwa, Anty Jams tace “kuma ki kara rubutawa ki ijiye again bazaki taba samun mijin dazaici kashinki kaman yanda Nura yaciba, idan zakiyi aure sau 1000 zaki fito so 1000 cus akidarki dabi’unki ne matsalan, beauty bashi ke keeping aure ba, being classy bashi ke keeping husband ba, having money ko business ko wayewa bashi ke keeping mijiba u of all people can tell people this yau bagashi Nura ya auro miki wacce batai makaranta ba, yar asalin kaune, Hadiza abinda namiji keso shine yasami mace dazatamai abinda yakeso which bakiyiba” daura hannunta Hadiza tayi akan idanunta sai kawai tahau wani kuka kai Anty Jams bata tabajin Hadiza tabata kalan tausayin data batayau ba tunda suka girma, ahankali tace “zonan Hadiza, come here” jawo Hadizan tayi tadaura kanta kan cinyanta tashiga shafa kanta ahankali tace “kidena kuka haka, ya isa ki yarda da kaddaran ki we all are humans, and yin mistakes yana kara tabbatar da yes mu fa yan adam ne we are bound to make mistakes, but what makes us special and unique is wannan ability na gyara mistake naka, trust me Hadiza is not too late u can amend all the broken relationships starting from Nura, apologize and become the good wife daya dade yana kwadayi yagani awajenki and zakiga Nuran ki zai dawo miki A man is like a little baby idan kika lallasheshi yana lallasuwa, yaranki ki karbesu, kin dauki cikin yaran nan for nine whole months, kika haifosu bar ganin baki gabansu as far as jininki ne su wlh wlh babu wanda ya isa ya chanza haka all it takes is kawai kijasu jikinsu, hug them that duminki dasuka dade basuji ba let them feel it, take them with u to kitchen cook for them and feed them da hannunki, bath them take them out to any park suje suyi wasa spend quality time da yaranki Hadiza and see idan sun kara kallon Ummi and last but not least Hajiya!” Anty Jams tadanyi shiru sanman tace “kinma Hajiya Babban laifi ta hanyar zaginta dakikayi da dauko musu police but Hajiyan dana sani is just like Nura, she’s a wise woman data haifi yara mata da yawa she knows how brain namu operate, she’s a mother trust me kikaje kika bata hakuri koda ta wayane wallahi she will forgive you and life goes on, Hadiza respect is earned baka demanding dinshi by fire by force, idan kika kama kanki kika sauke all duties naki as a wife wallahi Nura babu abinda bazai miki ba the, forget al’adun yan garin nan bakiji karin maganan nan ba idan wani yazo kasuwa yayi rawa yasami kudi wani yazo yayi duka zaici and this is exactly abinda yafaru dake, akidan wasu dakika dauka dakikaga works for them ke yajamiki saki dakuma kishiya, Hadiza u are educated I believe the only wanda ya chanchanci kayı pleasing aduniyan nan is Allah bawani ba ki manta da kawayenki and be you and win ur husband kinji” Gyadamata kai Hadiza tayi ahankali, Anty Jams tace “as for Ummi kada ki sake ki bata hurimin ta rainaki ki kama kanki babu abinda ya shafeki da ita ko harkanki trust me idan kikai haka bata isa tamiki maganan banza ba ke koma tayi gigin yi Nura zai taka mata burki I trust him kinji Hadiza” Gyadamata kai tayi, Anty Jams na shafa kanta tace “nasan da ciwo but kikai zuciyanki nesa and amend your path okay “ sake Gyadamata kai Hadiza tayi, sosai Anty Jams ke shafa mata kai tun tanajin sheshekan kukanta har wani baccin damuwa yayi awon gaba da ita ahaka.
**
Chapter 38 · 0% Book details