← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 97

Sashe 44

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 1️⃣6️⃣
As usual da asuba yatashi yawuce bayi wanka yayi yafito ya shirya tsaf cikin jallabiya sannan yazo bakın gadon yatadata ta hanyar dagota yana kallon her sleepy face yace “Hadiza” bude idanunta tayi takalleshi ahankali, softly yace “tashi kije kiyi wanka kiyi salla, fix something for breakfast and get the kids ready for school” dudda baccin dake idanunta but jin ayyukan daya lissafo mata saida tabude baki zatai magana saikuma tai shiru tunawa da fadan Anty Jams, ga mamakin Nura dan he was expecting her to nag sai yaga ta gyadamai kai tace “to” wani irin sweet smile yasaki baisan lokacin daya sumbaci goshinta ba yamike yawuce yafita daga dakin Hadiza tabishi da kallo wani wutan sonshi na ruruwa aranta, tana zaune awajen taji yabude kofan dakin Ummi wani irin bakın ciki taji yataso mata batasan sanda ta runtse idanunta gam gam ba, kasa motsi tayi awajen chan saitaji yabude kofan yafita ahankali ta tashi tawuce bayi tayi duk abinda zatayi tafito ta shirya cikin wani jean da riga mai kyau tasa dankunne tai salla tafito tana zuba kamshi tayi dakin yaranta Anty Jams tagani tana shafama Aman datama wanka mai, kallo daya tamata tadauke kai maida kofan Hadiza tayi tarufe tazo wajen ahankali tace “ina kwana Anty Jams” sabida Aman Anty Jams tace “fine” takalli Aman tace “greet Momy ka” batare daya kalli Maman ba yace “good morning Momy” shafa fuskanshi Hadiza tayi tace “morning Son” karasa sakamai kaya Anty Jams tayi tace “jeka wajen Amali” wucewa yaron yayi yafita daga dakin Anty Jams tamike zata fita dasauri Hadiza takama hannunta tace “Anty Jams idan kikai fushi dani rayuwan zata kara zama baki kırın agreni, the husband i have dazan iya magana dashi shine yasani in this situation, I can’t tell my friends abinda yasameni they will just laugh suce banida any influence agidana, kene komi nawa Anty Jams dan Allah kiyakuri, Anty Jams wlh, wlh naji maganan ki, I tried so hard jiyan nan na danne nakasa, look at it fa nashiga kitchen nama mutumin nan abincin dayay shekaru yana complain banamai, saiya dauka yabama wata is it fair? Nura namin mugunta da baki gani sabida anganshi shiru shiru? Anty Jams I can’t pretend to even save my own life maisa kikeso nayi pretending kaman everything is cool? Why do you want me to pretend as if is okay yadauki abincin dana dafamai, na zubamai yabama shegiyan butulun yarinyar chan eh? Why do you want me to pretend??” Juyowa Anty Jams tayi dasauri takalleta ta hanyar rage murya yanda babu wanda zai jiyosu tace “sabida as a woman dole ki koyi pretending, faking it da sauran su you have to learn ai shine kissa da kissisina, yanzu take a look at this girl ba lallai bane tanason yaranki tsakani ga Allah ba but yanzu idan zaki shekara kina gayama Nura Ummi batason yaranshi bazai taba yardaba why? Because dudda tana yar kauye ta iya wasan? Agaban babbansu zata iya nuna tafison yaran nan sama da rayuwanta, Hadiza u are educated but u lack wisdom, bakida hikima ko kadan, bakida dabara bakida wayau, waya gayamiki being real pays a zamanin nan da ake? Kowa is faking it pretending to be who he’s not, Allah kadai yasan waye mu sabida shine kadai yake duba zuwaga zukatanmu, you always allow your heart to control you baki using kanki, head is a monster while the heart is a toy very fragile, wani zubin is good to use head, idan u wanna catch Nura a palm na hannunki you need to stop showing him kin tsani yarinyar nan, and you have to stop being razz, loud and mahaukaciya like attitude nakin nan, yanzu yanda kike so hyper nan yarinyar nan bazata taba fito da true colors nata ba sabida Nura yaganta for who she is, amman idan kinaso to expose her inner aim you need to calm down make peace da kowa the ball is in your court har yanzu, wlh Nura na sonki Hadiza, I keep saying it kada ki bari soyayyan nan ya gushe, control anger naki, learn to swallow pride da kishinki sometimes not everything must be said, ki iya kissa da kisisina ki iya buga siyasa, idan kika kara all this attribute akan knowledge dinki wannan yarinyar saidai tazama yar kallo agidan nan wlh kinajina”? Ahankali Hadiza ta gyadamata kai, saikuma ahankali tace “Anty Jams yanzu yau saina bata breakfast na safe”? Gyadamata kai Jams tayi tace “da nine kema dakaina zanje nakirata bazan bar Nura yakirata ba, Hadiza show this girl she can’t play with you, Kece the real mastermind na game din nan, you set the rule, Nura is yours kinaji, ki nunama Nura love agabanta itama ta shaka, nasan hala tanachan maybe tanajin dadin kunyi fada yau Show her keda Nuri baku iya fushi da juna kinji” Dan murmushi Hadiza tayi abun na shiganta tace “to, yanzu mezan dafa for breakfast”? Anty Jams na mata wani kallo tace “Hadiza ohh Allah, da gaske kin dawo tantiriyan yar iskan yarinyar kin manta girke girken abincin safiya dakikeyi agidan ubanki ko to jeki tambaya YouTube, shegiya rubabbiyan fandararriyan yarinya” dariya Hadiza tayi tawuce tafita daga dakin tana hararan kofan dakin Ummi tadauka kasa.

Kitchen tashiga tafara aiki, bawai wasaba jitake kaman ta kurma ihu kaman zata zare haka takeji, dudda tanada kitchen tools that made cooking so easy but nahhh! She hate this cooking thing, tana cikin kwashe chips daga air fryer akai hugging nata tabaya dasauri ta juyo hada idanu sukayi da Nura da sauri ta turomai baki kaman yar yarinya tace “good morning” wani irin murmushi yamata dake kashema Hadiza zuciya yace “sannu da aiki Madam Boss Lady, Hajiya Hadiza damusan gida” murmushi tamai saikuma tace “bahaka kakeso na shiga kitchen naita wahala ba look at the way naketa zufa? Nuri why all this stress bayan Allah ya horemana baka ganin yanda business partners naka a living agidansu, why at my age and stage of life zan dinga shiga kitchen when I can hire the Guinness world record breaker Hilda tazama cook dina agidan nan ko wata or wani famous Chef, when the money is not an issue why stressing me Nuri?? Look at yanda nake zufa is it fair?” dasauri Nura yasaketa yana wani kallonta from head to toe saikuma yarike baki yace “dole nasaka miki AC guda uku a sabon kitchen dinki na sabon gida come here my lioness” sai kawai yajawota jikinshi taredakai hannunshi yana sharemata dan zufan daya keto mata daga goshi yace “bari me kikeso natayaki yi?” Bata tabajin dadin tambayanshi kaman na yau ba dudda tasan he’s just trying to block maganganunta ne yasa dasauri ta rungumeshi kaman zata shige jikinshi tace “just kaimin flask dinnan dinning kazo kaji” sakinta yayi yace “to Madam” daukan flask din yayi like a gentleman yawuce yafita dashi yakai dinning ya ijiye ya tsaya daganan yana kallon yanda take aiki a kitchen tana yatsine fuska yana fada da every tool dazata dauka he just wish Allah sa tadaure ahaka and he feels like appreciating and encouraging her, dan jim yayi saikuma ya ciro wayanshi daga Aliiyu ya shiga danne danne Hadiza na cikin aiki a kitchen taji wayanta yayi kara dasauri ta ijiye abinda tarike tazo kan island tadauki wayan kawai taga alert of 5M from Nura ansa narration as gift, dasauri tajuyo da kanta hada idanu sukayi yadan dagamata gira dawani irin sauri tazo kawai ta rungumeshi tace “Thank You Nuri na, you are just the best husband” murmushi yamata yace “and you are the best stubborn wife” dariya tayi kaman ba itaba taja hannunshi tace “kasan menene Nuri inaso nayi running sales na duka items dake shagona 30% off, nasan customers dina will rush everything zasu saye tass inaso nakawo new designs na kaya da turaruka harda kudin nan daka bani zan kara in kawo new abubuwa da yawan gaske nadan kara furnishing shagon, sales din saiya zama strictly online sales no walk in sabida muyi gyare gyaran da fentin da kyau” Gyadamata Kai yayi yace “okay Allah bada sa’a, if you need more fund along the line just let me know” murmushi tayi tare suka karasa aikin suka fito da komi yaran da Anty Jams suka sauko adan kunyace Nura ya gaidata zai wuce sama Hadiza takama hannunshi ahankali tace “Ina zaka?” Yana kallon kwayan idanunta yace “zan kira Ummi muyi breakfast” wani kalan daci taji aranta amman saita daure tajawoshi tazaunar dashi tace “don’t worry I will call her ai komi yawuce, nariga namaka alkawari dakai da Anty Jams I will never cause trouble again” Sosai Nura ke kallonta, murmushi Hadiza tamai tashafa kirjinta tace “trust me” tamike tawuce staircase Nura yabita da kallo tundaga kan staircase tafara kwalama Ummi kira, “Ummi, Ummi baki tashi bane breakfast is ready” sakın baki Nura yayi hakan yasa Anty Jams tace “Hadiza is a good person Nura kawai tana sonka ne over, and is not easy coping with kishiya but zaka gani eventually komi zai daidaita just try and be just, sannan caution duk wacce zatai misbehaving” gyadama Anty Jams kai yayi.
Chapter 44 · 0% Book details