← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 97

Sashe 11

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wuraren 7 nasafe yashigo gidan Hadiza yagani a dinning taci gayu sosai cikin wani exclusive atampa ta buga dauri tanacin lafiyayyen breakfast chips da pepper soup sai shayi agefe, itakuma Ummi na tsugunne a tsakiyan falo tana feeding Amal a baki Aman na kusa da su daduk ta shiryasu cikin kayan makaranta suna ganin babansu da gudu sukai wajenshi. “Daddyyy Assalamu Alaykum Dady ina kwana” murmushi yayi yadauki kowannensu yamusu peck yashigo dasu falon yace “ku karasa breakfast yanzun nan school bus zaizo” basuyi musu ba suka koma, anatse Ummi da kanta ke kasa tace “ina kwana Alhaji” batare daya kalleta ba yace “fine” sannan yadau remote yana chanza tasha 8 zai fita hakan yasa kawai ya ijiye remote din yawuce sama ko kallon HADIZA baiyiba itama bata kalleshi ba saima karasa cin abincinta datayi tawuce tadauki car key tace “ki dafamin couscous da daddare ke” ahankali Ummi tace “to Anty, saikin dawo Allah bada sa’a” yatsine fuska tayi bata amsaba tawuce tafita tashiga motanta tabar gidan, bata dade da fita ba motan su Amali yazo Ummi takaisu suma suka wuce tafito tana gyara wajen taje dinning ne ta gyara inda Hadiza taci abinci sannan tawuce tana duba girkin datake ma Kakan su Amal dazata zo, tana cikin tuka tuwon Alkaman taji kamshin turare dasauri ta juyo hada ido tayi da Nura daya shigo kitchen din yasa wani blue gizna shadda wlh yayi kyau na bugawa a jarida faduwa gabanta yayi dasauri ta dauke kai ta saki muciyan a tukunya zata duka yace “cigaba da abinda kikeyi” batai musu ba tacigaba saikuma tadan juyo hada idanu suka sakeyi ahankali bakinta nadan rawa tace “kana bukatan wani abu ne Alhaji”? Dan girgiza kai yayi yaja daya daga cikin kujerun dake gaban island din yazauna yace “me kike tukawa”? Atsanake tajuya takalli tukunyan tace “tuwon Alkama, kace Hajiya da safe zata iso saisa nake mata nasan basuyi kari ba suka shiga hanya, itakuma sister ka zan dafa mata abu daban” yana kallonta yace “nikuma fa” dan kallonshi tayi ga mamakinta murmushi yasakan mata dasauri tace “breakfast dinka nakan dinning amman idan kanason wani abu daban ne zaka iya fadamin namaka yanzun nan” “hmmm!” Yasauke ijiyan zuciyan dashi kanshi baisan karanta yafito ba maganan yatabamai zuciya dan wannan ne abinda matanshi bata tabamai ba just look at yanda yarinyar nan tabashi girma da daraja da kima kome yakeso yafadi zatamai that king treatment shitake mai, kawai saiya dago yakalleta yace “dafamin shayi mai kayan kamshi” dasauri tace “to” zare muciyan tayi daga tuwon tadan diga ruwa ta rufe tarage heat din tawuce ta wanke hannunta tashiga hadamai shayi shikuma yaciro wayanshi yana tabawa dan kawai tasaki jiki amman wlh kusan kome takeyi idanunshi binta suke, nan da nan tahada shayin tadauko wani hadadden flask jug tazubamai tasaka a tray tadauki cup da spoon da sugar kaga yanda take plating zaka dauka taje culinary school ne nan ko tsabagren experience ne a aikatau, tadauko tray din tazo har gabanshi ta ijiye sannan ta duka tace “nazuba maka?” Ahankali yace “yes” mikewa tayi yana kallon hannunta farcenta farare kal dogaye masu kyau tazubamai tace “sugar cubes nawa zansa ko asa zuma?” Kaman wani yaro dan he’s just enjoying the way take neman permission nashi for komi this is luxury da baya samu yace “zuma” dasauri tajuya tafita daga kitchen din taje dinning tadauko zuma takawo ta zubamai sannan tajuya tadauki cup din tadaura kan tray nashi tajuyo tabashi kallon fuskanta yayi sannan yasa hannu ya amsa yace “thank you Ummi” wucewa tayi takoma wajen tuwon tashiga kwashewa kaman daga sama taji yace “waye Mudin kauye?” Juyowa dasauri tayi takalleshi hada ido sukayi yana kurban tea juyawa tayi tacigaba da kwashe tuwon tana mamaki a ina yatabajin takira sunan Mudi saikuma ta sauke ijiyan zuciya tace “tsohon miji na ne” dasauri Nura yakalleta yace “kin taba aure”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman an dade tun ina shekara sha uku-sha hudu aduniya” yana kallonta yace “meya rabaku”? Tsayar da kwashe tuwon datakeyi tayi saikuma ta kalleshi yanda ya tsareta da ido yasa ahankali tace “dukana yake, kullum kullum duka, hakanan kaman idan bai dakeni ba bayajin dadi rayuwanshi, shine…..” takasa maganan tai shiru takai hannu ta goge hawayen dasuka zubo mata dasauri tajuya tacigaba da kwashe tuwo Nura yace “shine meya faru”? Ahankali tana kwashe tuwon tace “shine rannan dayamin wani bakin duka saida na haifo bakwaini, inada cikin wata shidda lokacin, amace yafito yaron, saida nayi jinya na kusan shekara daya inata fama da yoyon fitsari, Gwaggo na ta hadashi da mai anguwa akan saiya sakeni kuma abimini hakkina dan ya illata mata jika tun bayan haihuwan dole dayasa nayi ban warkeba, to da kyar yasakeni amman dudda ina rashin lafiyan yakan biyoni har gidanmu yamin duka har suma inayi, ko baizoba kullum cikin fargaba nake zaizo, Maman mu tarasu Gwaggo mu ce kadai garemu kuma batada karfi ta tsufa, ahaka dai na warke but ina cikin tsoro kullum, saisa dataji wata mata dake zuwa kauyenmu kwasan yara aiki taje ta roka da kyar akace za’a daukeni, to aboye aka fitar dani daga kauyen mu kada Mudi yaganni, tundaga nan nazo birni tun ban gane abubuwa harna gane yanzu nima, amman inaso nakoma kauyenmu naga Gwaggo na da kannina Salamatu tai aure harta haihu Maimuna da Ikilima ne za’ayi bikinsu kwanan nan kuma inaso naje amman Gwaggo na bataso nazo tsoro take kada nakoma kauye Mudi ya kasheni, yanzu ance yafi da zama takadiri ya gagari kowa, tsoron shi ake har mai gari, amman nayi kewan garinmu da gidan mu da Gwaggo na da kannina sosai bansan ya Allah zaiyi dani ba bansan kozan kara sa kafa a kauyenmu ba” tai maganan tana kai hannunta saman fuskanta duka biyun tadanyi sheshekan kuka mara sauti, shiru Nura yayi yana kallonta tabashi tausayi sosai ahankali yace “kinaso nakaiki kauyenku kiga yan uwanki”? Dasauri tazare hannayen ta dagakan fuskanta takalleshi da rinannun idanunta yanda ya tsareta da idanu yasa gently ta gyadamai kai, murmushi yayi yace “I promise zan kaiki kauyen ku, and namiki alkawari ba Mudi ba ko mudari yake bai isa yamiki kallon banza bama balle ya dakeki kinji” gyadamai kai tayi ahankali, murmushi yadan mata yace “kada ki kara kuka bayama fuskanki kyau” akunyace tai murmushi shima murmushi yayi yace “idan Hajiya tazo dazaran nagama kata katan asibitin ta zan kaiki gida ko” gyadamai kai tayi dasauri, tashi yayi yakalli agogon hannunshi yace “bari natafi daukosu nasan jirginsu yatashi yanzu kafin nakai airport sun sauka, kinason nasayo miki wani abu”? Yamata tambayan da saida ta kalleshi da mamaki ganin ya tsaya yakuma tsareta da ido tace “Amali tadameni tun jiya zatasha yoghurt babu yoghurt agida” jinjina kai yayi irin yaji din nan yace “ke me kikeso”? Sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “slippers wannan yakatse dazu na naneshi da wuka mai zafi saisa na iya sawa” yanda takejin kunyanshi na burgeshi sosai, anatse yace “to” yajuya zai wuce dasauri tace “Nagode Alhaji Allah kara girma, saika dawo Allah ya tsare” juyowa yayi yace “Ameen Hajiya Ummi” dasauri takalleshi wucewa yayi yafice yana murmushi mota yashiga, saida yafara tsayawa a super market yayi sayayya harda cream da shower cream mai kyau yasa mata da su turaruka da wasu abaya daya gani a super market din da idanu ya gwada tsayinta haka yabiya kudi yafito, haryakai airport labarin Ummi yake tunani yaushe kauye zasu dainama yara Auren wuri ne haka, yanzu sabida wani katon mugu aka koro yarinyar nan aiki, yayi traumatizing nata tun tana 14, small girl fa, hmmm Allah ya kyauta.
Chapter 11 · 0% Book details