← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 97

Sashe 45

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Hadiza tana kaiwa gaban kofan ta tsaya tai jim saikuma takai hannu ahankali zata bude kofan Ummi tarigata budewa hada ido sukayi da sauri Ummi tasauke kanta kasa ahankali tace “Anty yakuri ina cikin bayine dakike kirana ina kwana, gani” Hadiza dake kallonta daga sama zuwa kasa hijabine ajikinta jitayi kaman ta shaketa tadai daure iya daurewa tace “bismillah zomuje muyi break” dadan sauri Ummi tadaga kanta takalli Hadiza, Hadiza tace “muje mana, kosaina kama miki hannu”? Dasauri Ummi ta girgizamata kai Hadiza tajuya zata wuce dan she can’t stand looking at the girl dasauri Ummi takama hannunta ahankali tace “Anty” tsayawa chak Hadiza tayi batare data juyoba, fitowa Ummi tayi daga dakin gabaki daya tareda jawo kofanta tarufe ahankali Ummi tace “Anty dan Allah kiyakuri kome namiki ki daina fushi dani, gidan nan gabaki daya ba dadi idan ranki yana abace, wlh niba muguwa bace ko butulu bazan taba cutardake ba, bansan dawo da magana baya amman ban auri Babban su Amal dan cin amana ba na au…….” Dasauri Hadiza tace “kin aureshi dan kina sonshi ne ko?” Tajuyo tazubama Ummi idanunta dahar sun kada sunyi ja hakan yasa Ummi tayi shiru, murmushi Hadiza tasake kakalowa tace “ai kin sanar dani ranan nan wuce muje muyi breakfast” Hadiza ta fizge hannunta tayi gaba da sauri cus idan takara 2secs zata iya hallaka Ummi halan, ba karfi a guiwan Ummi tashiga saukowa har kasan Nura yabisu da kallo yanajin wani kwanciyan hankali zuwa Hadiza tayi tazauna kusada shi Ummi tazo taxauna kusada Aman bayan ta gaida Nura da Anty Jams Nura sai kallonta yake yana murmushi Hadiza na lura dashi, zubama kowa abinci tayi ta zubama Ummi ma, Nura sai mamaki yake aka shiga cin abinci, da gangan Hadiza tawani kwanto jikin Nura tana nunamai ketchup dake gefen lips nata tace “Nuri ohh noo sharemin ketchup a saman bakina” batare daya kawo komiba ya yagi tissue yakama kanta yashare mata yace “har yanzu baki daina shan ketchup ba saikace wata yar Karaman yarinya” cikeda son gumama Ummi Hadiza tace “ni ai babyn kane har yanzu right” adan kunyace Anty Jams tace “Ana kirana awaya nidai bari naje sama nasan su Batool ne” dariya Hadiza tayi tasa chips abakinta tawani yi grabbing face na Nura unexpectedly tace “haaaaam bude bakinka kaci” dan kallon yaranshi Nura yayi dake magana da Ummi datayı kaman bataga komiba tana dan hira dasu tana basu chips nasu abaki, cikin whispering cikeda kunya Nura yace “wat is this Hadiza? Children are he……” kafin yakarasa maganan tawani manna bakinta kan na Nura ta turamai Irish din ciki cikeda iskanci, wani kalan wawan kwarewa Ummi tayi dasauri Nura ya juyo yakalleta yana hadiye chips din da Hadiza ta zubamai abaki dayawa bakinshi yacika tam yace “ummm sorry Ummi” maganan shi ma baya fita da kyau, zai bata ruwa Hadiza tarigashi tace “ga ruwa Ummi sannu halan su Aman sukasa kika kware” karba Ummi tayi daidai lokacin schoolbus na zuwa kwasan yaran yazo duk suka mike from dinning kowa najan lunchbag nashi, Nura yatashi yakaisu waje suka fita Hadiza ma ta tashi daga dinning din tayi wajen kofa akabar Ummi kadai awajen atare suka shigo falo suna shigowa kaman ba Hadiza ba tawani tsalle tahau bayan Nura tana ihu kaman yar karaman yarinya tace “kaini dakina Nuri muje muyi wanka kaine zaka saukeni a shago yau I don’t feel like driving” dan satan kallon Ummi Nura yayi kanta akasa ga Irish agabanta daba wani ci takeba ba yanda ya iya yace “muje” dan baiso yace tasauko yabata kunya ga Ummi awajen suka wuce sama Hadiza na counting step, “bene one, bene two, bene threee…waiii Nuri shillani zan fadi…….” wani hawaye masu dumi Ummi taji sun zubomata daga idanu, kawai saitaji yau kaman ita bakomi bane awurin Nura ba, sai taji wani tsoro, shakku da fargaba sun dirku aranta na kada yazo yasaketa fa dama Hadiza tabata 2weeks gashinan sun shirya yasoma mantawa da ita sai wasan soyayya suke agabanta itada bata taba ganin ya goya Hadiza ba tunda take gidan nan, share fuskanta tayi da bayan hannu dasauri, tama kanta alkawari koma menene tashigo gidan nan kenan Billahillazi La’ilahaillahuwa, zatai kome zatayi Nura itama yasota sama da yanda yake jinta aranshi yanzu, duk yanda taso kada tayi kuka kasawa tayi dan wani daci daci takeji tundaga bakinta har duka jikinta kaman taci shuwaka ganin yanda Nura no even send her today soyayya da wasa sukeyi agabanta, haka ta dinga taba abincin tama kasaci sai kawai ta tashi tayi clearing table din takai komi kitchen tashiga gyara kitchen din just to forget dacin datakeji.
Chapter 45 · 0% Book details