← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 97

Sashe 6

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani babban asibiti suka tafi wannan karan shiya sauko yabude musu baya da kanshi yadauki jakan yabar mata Amal dayaga tai lakur ajikinta suna shiga aka karbesu sukai ciki office na Dr suka shiga, wani baturen Dr ne yace “meke damunta”? Kallon Ummi Nura yayi yace “meke damunta” ahankali tace “zazzabi take tun kwana biyu bata iyacin abinci, but nafada ma Anty tadubata tace chanjin yanayi ne, jiya tanata tari sai zazzabi, kuma idan tashiga flowers na gidanmu jikinta na kaikayi, idanunta namata kaikayi shima, jiya batai bacci ba kagani kuma yanzu batada karfi ko kadan” tanuna Amal dake jikinta kaman zatai kuka, sosai Nura ke kallonta saikuma yadauke kai yama Dr bayani da turenci Dr yace “za’a basu gado cus tana running temprature da yawa kafin a debi jininta aga meke damunta, tashi yayi zai debi jininta da sabuwan alluran daya bude dasauri Ummi takalli alluran tadan kankame Amal ajikinta, ahankali Nura dake lurada ita yamika mata hannu yace “kawota” batai musu ba bashi Amal tayi Dr yadebi jininta hawaye taruwa yayi a idanunta yabda Amal ke kuka nan da nan aka kwantar dasu awani private room sai kuka Amal take tana mikama Ummi hannu, kasa zuwa Ummi tayi ganin Babanta natare da ita tashi Nura yayi yakalli Ummi yace “zo ketake nema” kaman jira take dasauri taje rungume Amal Ummi tayi tace “likitan nan ko saimun kaishi wajen police yama Amal allura da zafi”? Gyadamata kai Amal tayi a shagwabe, Ummi tace “sannu ko, zakisha Capri ri”? Dan yatsine fuska Nura yayi irin menene Capri ri kuma, Gyadamata kai Amal tayi, dasauri Ummi tabude jaka tadauko caprisone tace “tadaaaaa” wani kalan murmushi Amal tayi dashi kanshi Nura saida yayi murmushin yadan tabe baki yaciro wayanshi aranshi yace “omelette Omu Omu, Caprisone kuma Capri ri ikon Allah” tana cikin bata juice din wayanta dake pocket din jakan kayan Amal yashiga ringing da sauri tasa hannunta daya taciro wata screen touch Vivo ne dataji jiki sosai ganin Anty yasa ta amsa takai wayan kunnenta cikeda girmamawa tace “Hello Anty ina kwana” daga ta dayan bangaren Hadiza tace “kina ina Aman yatashi”? Cikin kwantacciyan murya tace “Uhmm Anty munzo asibiti da Amal ne, jikinta ya rikice” Hadiza najin haka tasan mijinta ne yakawosu asibitin cikeda masifa tace “to yanzu wazai yima Aman brush da wanka yabashi breakfast eh? Ko nine danake shirin fita aiki yanzu zan tsaya nayi all of this, maza maza ki bar Amal wajen Babanta ki kira bolt yazo ya maidoki gida ai nakoya miki yanda ake yin bolt dan nasan nace kifita kije kibi mota along bacewa zakiyi babu inda kika sani, maza maza kira bolt and come back home kima Aman wanka kibashi breakfast ki shiryashi yatafi school kafin school bus yazo keko school bus yazo idan sun tafi ki kira bolt ki kaishi school din dakanki, kina jina tunda ke mahaukaciya ce dakikiya yar kauye dayace kizo kutafi asibiti bazaki iya gayamai zakiyi aiki ba kika bishi, nabaki 3min karki bari su cika ban ganki agidan nan ba, sabida jakanci da dakikanci irin na yan kauye ina biyanki danki kulamin da yara da gida akanme zaki wani asibiti bayan babanta natare da ita, idan kinsan kin gaji da aikin ne bazaki iyaba ki gayamin na sallameki wata tazo ha’aa nida kudi na ko yan aiki guda dari nakeso zan samesu wlh yau yau din nan, zan koreki wlh kika batamin rai” da sauri Ummi tace “kiyakuri Ant……” dip ta katse wayan tashi Ummi tayi dasauri tace “ina zuwa Amal” tajuya dasauri hada ido tayi da Nura dake kallonta hakan yasa da sauri ta tsugunna daganan wajen gado tace “Alhaji zanje gida Anty tace nabar Amal awajenka zanje in shirya Aman yatafi school” kai tsaye yace “koma ki zauna bazaki ba” dasauri ta kalleshi ganin yacigaba da danna wayanshi yasa takoma ta zauna ahankali but gabanta sai faduwa yake kusan 4min da gama wayan wayanta yahau ruri hannu yamika mata yace “bani wayan” daukan wayan tayi tazo har gabanshi ta duka tabashi wani iri wayan yamai a hannu screen din dukya faffashe wannan ai zai iya yagamai fatan kunne saida wayan yakatse yay dialing number ta da wayanshi yatashi tareda ijiye wayanta kan kujera yawuce yafita dan baiso wani yanajin wayanshi da ita waje yafita wajen parking space daidai ta amsa wayan kafinma yayi magana cikin fushi da ihu tace “sabida kaike biyan salary nata kahanata zuwa ko to daga this month kadaina nizan dinga biyan salary nata lemme be in charge of her nai controlling nata to my satisfaction Alhamdulillah inada kudina, but akan mema zaka hanata dawowa ga Aman ko brush baiyiba bai wanka ba yana kuka yunwa yakeji kuma kasan zan tafi shagona yanzun nan maisa kakemin haka? What kind of man are you? Why do u always look for opportunity to belittle me kanunama kowa banda power over anything in our house eh? What is your problem dani? Bakin ciki kake inada kudi kafison kullum ina kasanka ina rokonka do this for me do that for me”? Shiru Nura yayi saikawai yaciro wayan daga kunnenshi ya katse wayan dan talking to Hadiza is impossible, ita ko kunya bataji ta haifi yara saidai wasu su tayata kula da yaran, gatada baki kaman reza talking to her is just too impossible dukan motanshi yayi ya jingina da motan yayi shiru is this how life zai cigaba da tafiyan mai? Bayagane gaba balle bayan Hadiza, ance communication is a key in Marraige but communicating da Hadiza is impossible kafin kayi magana daya tal tayi dari da hamsin, babu one single abu datakemai na mata, she doesn’t take care for him, karma aje batun girki he can’t even remember the last time da Hadiza tadau ruwa ruwan nan dai bottle water tabashi yasha, he can’t even remember wen was the last time yaci abinci agidanshi, shi bayacin abincin yan aiki itakuma batayi saidai kullum yaci abinci awaje ko agidan abokai, tun yana korafi yan aiki na shigo mishi daki harya dena dan yagane idan basu gyaraba dakinshi baza’a taba gyaramai ba, he can’t remember the last time data gaidashi, is as if he doesn’t exit awajenta whenever he tries to talk to her tace yafara fitina da bala’in da korafin da mita shi yabarta tagaji, she’s not remorseful akan abubuwan datake she feels itadashi equal right sukedashi sabida tana matanshi he can’t step and match her ko control her, sabida tana mace doesn’t mean zata kwantarmai dakai that’s just her mentality, Hadiza is very stubborn ga baki Ya Allah, wlh yagaji baison mata biyu dan ko daya bakar wahala take bashi aduniya, baison broken home dan yataso Mamanshi bata tare da babanshi he don’t want that ma yaranshi, baison neman matan banza abinda baiyiba yana yaro shine yanzu zai fara when he’s approaching 50 haba bazai tabayiba but he’s just tired yarasa ta ina zaibi ya gyarama Hadiza zama ya gwada zama waje yakai 1-2 nadare amman ko ajikinta yadawo ma tai bacci abinta he’s just soo tired of everything he’s not happy in his home.
Chapter 6 · 0% Book details