← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 97

Sashe 7

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wajajen 10 aka sallamesu da magunguna a hannu suka dawo tunkafin sukai gate na estate dinsu ya hango Aman dinshi kan kujeran security da pajamas ajikinshi da ledan popcorn idanunshi sunyi jaa, jiyayi zuciyanshi takama da wuta parking yayi yafito dasauri security dayake zaune kusada shi yace “Yallabai barka da dawowa Madam ta ijiyeshi anan gashinan yanata kuka yace yunwa yakeji shine na saya mishi Popcorn yamai jiki”? Sabida yanda ran Nura ke daci gyadamai kai yayi Aman yarike hannunshi yakalli fuskan Baban kaman zaiyi kuka gwanin ban tausayi, kaman dan maraya yace “Daddy where’s Anty Ummi am hungry she’s the only one that gives me food and play with me, Mommy never gives me food or play with me” suppressing anger dinshi yayi yaduka ahankali ya shafa kan yaron yace “muje Anty Ummi na bayan mota da princess don’t cry again okay”murmushi yayi yay bayan mota da gudu yabude yashige shikuma ya tsaya yama security godiya tareda bashi kudi sannan yazo yabude gaban mota yashiga ya zauna yaja mota ta glass na gaba yake kallonsu duka yaran sun kankame Ummi suna hira da ita, sai biye musu take kaman yarinya itama, wlh zaka dauka itane mahaifiyar yaran kawai dan ita black beauty ne yaran kuma fararene tas su kaman turawa amman kana ganinsu kaga strong affection tsakaninsu, sunma manta dashi a motan sai hira suke Aman yarike Ummi gam yanata zuba kaman bashi yayi kaman orphan dazuba, akofar gida yayi parking duk suka sauko tana rikeda Amal, Aman shima yarike mata hannu suka wuce ciki yabisu da kallo direct kitchen suka wuce zaunar dasu Ummi tayi kan kujerunsu dake kitchen din dake gaban island, tashiga yimusu girki agurguje dan Aman yunwa yakeji tana attending to them, ta dafa lafiyayyen taliya na manza fevorite dinsu da kaza ta zuzzuba musu a plate tajuye sauran kuma a kula mai kyau takai dinning ta ijiye sannan takoma kitchen tana bama Amal abaki dantaci da kyau, koda yashigo gidan dan tuntuni yana waya awaje kamshi ne yamai sallama wani kalan yunwa yaji yanaji dinning yaje yazauna kaman wanda ke tsoron wani abu bude kulan yayi daidai Ummi tafito da tray na ruwa da fresh juice a hannu dantaji zuwanshi ta ijiye kan dinning taduka tace “ko adafa wani abune daban Alhaji” girgixa mata kai yayi yace “a’a wannan yayi” tashi tayi takoma kitchen, kaman mai tsoro yadau fork yasa yadebo kadan yakai bakinshi yatauna dadin dayaji wlh saida kunnenshi yayi siiiii, baisan sanda yadauki plate yadeba ba shi arayuwan shi yanason home made food rashi yasa almost few restaurants ne baisaniba a Abuja ba yaune rana na farko dayaci abincin yar aiki and wlh yamai dadi sosai tass yacinye yatashi ga mamakinshi rawa yaga tanama Amal tana kai abinci bakinta da wayau dantaci, ga magani dayaga ta fito dasu ta zuzzuba a marfi dan an fadamata yanda zata bata asibiti, shima Aman yataso yana tayata rawan sunama Amal rawa dukansu biyun tana dariya sosai fa tana karban abincin tabata maganin ta shanye tass ba gardama ko kakarin amai suna mata waka Aman na tafi kaman suna studio, jinshi kawai yayi yana murmushi ance some yan aiki suna faking love ko sabida parents na yaran but shi all he sees ana is genuine love, kuma yaran loves her suma dearly hakanan samin kanshi yayi yana kallon Ummi sosai, yarinyar black beauty ce tanada tsayi akalla zatai 23 ko 24, yar kauye ce from her dressing but she’s kind and tanason yaran shi kuma her smile is contagious dan gashi shima yanata yi, sannan the way she dance is annoyingly cute, kaman Ummi taji ana kallonta juyowa tayi da fuskanta ta kallo falon karaf suka hada ido da Nura dake kallonta tana rawa ma Amal.

Wanna talk to me about something??? Chat me up anan;
wa.me/+2347012181461
[9/18, 9:17 PM] +234 706 542 1229: 💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

Novel din nan is FREE bana kudi bane.
Chat me up don saki a group

wa.me/+2347012181461

EPISODE 4️⃣
Wuraren 7:30 Hadiza tashigo gidan gabaki daya ranta amugun bace yake, Aman da Amal sai Ummi ne afalo dukansu ukun suna zaune kan dogon kujera suna kallon videos letters sound for Amal dudda Ummi bawani boko tayiba iya kanta JS3 but ta iya all this basic things na school shima sound din dan bata iyabane zamanin su da ABCD sukai karatu ba da sounds ba saisa suke koya tanan youtube yanda Amal ke koya itama haka take koya dan sabida koya musu, jin an bude kofa kai tsaye ba sallama yasa suka jujjuyo dukansu hada idanu Ummi tayi da Hadiza dake mata wani kalan kallo dayasa dasauri tamike tsaye daga kan kujeran ta duka kasa danta gane kallon me take mata cike da girmamawa tace “barka da dawowa Anty, ina yini” Hadiza da dama ta shigo da mugun bacin rai dan tun kiran da Nura yamata ashago ranta yake abace tace “ke ban gayamiki koda wasa kada duwawunki yazauna akan kujerun gidana ba, ke kinada darajan dazaki zauna inda nake zama ne yar aiki dake, ubanwa yagaya miki yan aiki nada matsayin zama akujerun gida” Ummi da kanta ke kasa ahankali tace “kiyakuri Anty mancewa nayi Amal muke koyama karatu” baki Hadiza tabude zatai magana daga Aman da Amal da duk suka tashi suna kallon Maman nasu Aman yace “stop shouting at Anty Ummi Mommy” dasauri takalli yaron ta ballamai harara, turo baki Aman yayi yace “u are always fighting and screaming Mommy our school teacher tace anger causes sickness” hararanshi Hadiza tayi bata tace “nakusan fasa bakin nan naka mara kunya kawai” turo baki yayi dan haushin Mommy shi yakeji sosai sabida yanda koda yaushe fada takema Anty Ummi su, bata sake cewa komiba tun maganan Aman tacire heels din dake kafanta awajen tawuce dinning straight taja kujera ta zauna tana sauke jakanta kan table din tace “idan kinga dama kizo kibani abinci” tashi Ummi tayi da sauri ta taho dinning din Aman kuma yakoma kan kujera yayi zamanshi yadauki IPad itakuma Amal tayi hanyar dinning din cikeda shagwaba tace “Mummy babuuuu, ki goyani zanyi bacci” cikeda masifa Hadiza ta nunata da yatsa tunkafin takarasa dinning din tace “don’t even come here wuce kitafi wajen Aman kiyi karatu yanzun nan nadawo zaku fara damuna, goyon kaniyanki zan miki, jeki jira yar aikinku tazo tagoyaki, Oya go back” juyawa Amal tayi tafashe da kuka dasauri Ummi takalleta kaman tadaina serving Maman taje ta dauketa, ta tsani taga yaran na kuka wlh har cikin ranta, ahankali tawuce wajen Aman tafada jikinshi rungumeta yayi yace “stop crying Amali Anty Ummi is coming yanzun nan kinji” Gyadamata kai tayi yana share mata fuska yace “let’s play game”.
Chapter 7 · 0% Book details