← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 97

Sashe 22

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan 2min Meena tayi adakin da Ummi take zaune ga roban farfesun zabo agabanta bama ta taba ba tayi nisa sosai tana tunani, dan ijiyan zuciya Meena tasauke ta duka ahankali ta ijiye kofin madaran shanu mai zafi dake dauke da magani da Gwaggo tabata takawoma Ummi ta ijiye agabanta sannan ta taba Ummi tace “Ummi” firgigit Ummi takalleta tace “Na’am sorry banjikibane Meena” Meena dake kallonta tace “tunanin me kikeyi haka Ummi? Kinsan sau nawa ina kiran sunanki baki jiba tunanin me kikeyi haka?” Dan shiru Ummi tayi takasa magana hakan yasa Meena tazauna da kyau agabanta tana kallonta tace “meke damunki Ummi?” Yanda Meena ta tsareta da idanu yasa ahankali tace “Meena bansan yaya zan kalli Anty ba, bansan yaya duniya zata kalleni ba nazo aiki na aurema mata miji, kawai jinayi banajin dadin dan kaman nayi cin amana ne, wani kalan rashin jin dadi nakeji azuciyana da damuwa dadai wani iri” ahankali Meena tace “shi ake kira da guilt” ahankali Ummi tace “inajin shi guilt din azuciyana sosai wlh” ganin yanda Ummi tayi yasa ahankali Meena takama hannunta tace “Ummi tsaya kiji abu na farko danake so nafada miki shine Matar mutum kabarinsa, inhar Allah yarubuta wane ko wance matarka ce saika aureta ko ana k’ak’a” hannunta Meena tasaki tace “nasan yanda za’a kalli abin amman bakida laifin komi a case din nan” dan shiru Meena tayi saikuma ta nisa tace “Ummi kinga Yaya Nura bantaba ganin namiji Mai kirki da bala’in hakuri da rashin magana irinshi ba, tun yana yaro haka yake, baida hayaniya, baida rigima, baida fada, dukanmu kanninshi mata ne dukanmu mun taso shike kula da mu, ya wanke mana kaya, har yau ina tuna yanda yake wankemin kashi da ina yarinya yamin wanka ya goyani, ba karamin taimakawa Hajiya da rainanmu yayi ba cus tun ina yar yarinya babanmu yarabu da Hajiya sai Ya Nura yazame mana uba, wannan dabi’un nashi na sanyi da hakuri yasa Hadiza ta matukar rainashi” Meena tasake sauke ijiyan zuciya tace “nasan kalolin dumbin tunanin dakike azuciyanki Ummi irin yaya zakiyi kiyi zaman kishiya da Anty Hadiza, bari kiji aure is not about how beautiful you are, ba kyau, boko, kudi dawasu ado da kyalekyalen duniya bane aure ba dan duk zasu iya karewa, hali shine aure, halinki amatsayinki na mata zaisa mijinki yaji yana bala’in sonki da girmamaki haka kuma shi wannan halin shi zaka mijinki yaji kin siremai yakuma gaji dake, and duba ga abinda ni nagani da idanuna Ummi halinki da dabi’unki yasa Yaya Nura yakamu da sonki kaman yanda aranan damuka shigo Abuja muma mukaji muna sonki” Meena takai hannunta saman kan kafadan Ummi tace “ki cigaba da halinki abinda ake cewa da turenci keep being you Ummi, the caring sweet and soft Ummi mai kulawa da kowa, ki tsarkake zuciyanki ki shiga gidan Ya Nura da zuciya daya kiyi zaman aurenki kada ki bari wata ta zageki ko taci miki mutunci dagake har ita duk zamanshi kuke, wannan kunyan ki ijiyeshi agefe Ummi kinfini sanin abubuwan da Ya Nura baya samu wajen matarshi ke kibashi dan kin zauna agidan dasu, sannan namiki alkawari zan baki wasu abubuwa karatun classes na matan aure da M shakur keyi da hausa dan kowa yagane ki karanta sannan zan biyamiki kudi ki shiga classes din kokuma ma zan biyata ko nawa zata chajeni tamiki private erotic hausa class dantanayi ma wayanda basason group, ki koyi abubuwa ki ijiye kunyan nan ki farantama mijinki sama da yanda yar birni wayayya ma zata iya, ke ba budurwa bane kin Riga kin wuce level din nan, ba wani kwana kwana ki shayar da Yayana dadi da kwanciyan hankali and kiso mijinki sama da komi is not a crime kinji” Gyadamata kai Ummi tayi ahankali tanajin wani kalan kwarin guiwa Meena takai hannunta ta share mata dan guntun hawayen daya zubo tace “maza saki jiki kiyi walwala kisha magungunan ki da kyau ana miki gyaran jiki dan ki mantar da Yayana damuwanshi kuma ba kunya ehe kinajina” akunyace Ummi na murmushi ta sunnar da kanta dariya itama Meena tayi tanason kunyan Ummi ta tashi tafita, kofin Ymmi tadauka tafara sha saikuma ta kalli wayanta kewanshi kawai taji tanayi wlh ahankali tadauki wayan dailing numbershi tayi Kunya kuma saiyasa ta katse dasauri daga aurensu jiya dazu kuma yakirata dasafe saitayi ta damunshi ijiye wayan tayi agefenta dasauri tadauki cup din zata sha wayanta yahau ringing dasauri takalli wayan ganin shine yasa takai wayan kunnenta asanyaye tace “ina yini” cikin murya kaman batasaba yace “lafiya lau Ummi na kewana kikayi kikemin flashing”? Rufe fuskanta tayi kaman yana wajen baki tabude zatace a’a murya ciki ciki tace “eh” dasauri tazaro idanu taredakai hannunta ta rufe bakinta saikuma da karfi tace “wayyoo Allah ni a’a fa zance nace eh” hahahha Nura ya kyalkyala dariya wani kalan dadi yaji bana wasaba yanda she’s missing him din nan, cikeda so yace “kada kidamu nakusan zuwa na daukeki nima nagaji wlh kewan Hajiya Ummi nake sosai” adan kunyace cikeda son abar maganan tace “kaci abincin rana? Kun dawo daga asibitin da Hajiya ya jikinta”? Dan shiru yayi ko Allah yasan yanason yanda take tambayan jikin mahaifiyanshi da yanda take tambayan yaci abinci cikeda so yace “naci abinci tareda Hajiya Ummi, munje asibiti taga duka tests nata sun fito Dr yabata magani zatasha na 2weeks saimu kara komawa” dan ijiyan zuciya Ummi tasauke tace “Alhamdulillah Hajiya zata warke kaman ba itaba in sha Allah tayi ta tafiya da kanta batare da taimakon wani ba, akwai wani mai da Gwaggo tabani dana gayamata wai tadinga shafawa akafan zasuyi sauki” murmushi yayi yace “bari naduba jirgi nazo na amsa” dan zaro idanu Ummi tayi tace “aikin fa”? Yana murmushi yace “zan ijiyeshi agefe nazo naga matata wai nazo na amsan ma Hajiya maganin ta” kyalkyacewa da dariya Ummi tayi dayasa yayi shiru yana sauraran dariyanta dakema kunnuwanshi dadi kaman busan algaita, ahankali yace “ina sonki Ummi, Nura na sonki” akunyace ta sunnar da kanta tana boye kanta acikin guiwanta tana dariya kasa kasa hakan yasa murya chan kasa yace “bazaki gayamin kina sona ba? Maimaita abinda kika fadamini a wasikar nan” lankawshemai kai tayi saikuma ta kwanta anan kasan dakin datake ciki ta lumshe idanu kawai shitake gani cikeda shauki dakuma sautin wake dawani irin taushashiyan murya tace “banjin zugar kawaye a soyayya kaina dauka, ka sharemini hawaye, kasa nadaina kuka, indai ina araye Sam bana gudun ka, Allahu ya kiyaye banison waninka, kaine dai daya, acikin zuciya, mai sakani dariya sannu masoyinaaaaaaaaa” “Ummiiiiii haka kika iya wakan soyayya”? Cewan Gwaggo datagama jin komi, dasauri Ummi tace “wayyo Gwaggooo” ta katse wayan tana boye fuskanta bakaramin kunya taji ba ganin Gwaggo na jinta sai dariya take tana kwalama su Shatu da Meena kira suzo wakan soyayya Ummi takewa mijinta.

Wallahi Nura ko at this point jiyake bazai iya ba, dudda yau anci kwana biyu kaman sati bazai juyoba haka yakeji baiso yayi abin kunya ne shiba yaroba saisa kawai yake daure wa but Ummi zata kasheshi da soyayya, watttt!!! Ba’a tabamai wakaba tun zamanin yana secondary school daya fara soyayya da all this classmate yan aji but just look at wakan soyayyan data raira mishi ga muryanta kona mawaki baijin yakai na Ummi dadi ba, tashi yaji kanshi nayi yana kumbura, abu yaji an bugamai akai hakan yasa yabude idanunshi Musa ne yashigo office din dawata katuwan jaka a hannunshi yace “waikai mehaka saikace wani saurayi sai shafa kirji kake karike waya gam a kunne kaman wanda akema wahayi, ka lumshe idanu kana cikin kogin soyayya, dalla taso kazo nan nazo na shirya abokina” Musa yayi maganan yana zama kan dogon kujeran dake cikin office din yashigan hada mishi some magunguna yace “yauwa wai ban tambayeka ba ina zaka ijiye Ummi ne? Zaka rabamusu gidane”? Girgixamai kai yayi yace “a’a bazan so yarana su taso gida daban daban ba inaso yarana su taso kansu a hade, babban gidan nan nawa nasa an fara gyaranshi kowa da flat dinta nan da 2month za’a gama aikin tass, before then anan gidana zamu zauna dakina zan cire komi naciki nayi magana dawata interior decor gobe zatazo tadauki measurement jibi za’a kawo komi, and inaso nakara siyan wani gida a Adamawa, inaso idan na daukota daga kauyensu mu zauna anan muyi hornymoon and again yarana su Aman sunaso suje kauye to irin duk ranan da zamuzo munada gida agari kagane” Musa daya bashi kofi yace “nagane but Hadiza fa kasan kar kwankwamnata su tashi ta taba Ummi fa” wani kallo yama Musa yace “duk randa tai kuskuren tabamin mata saitaga other side of me” murmushi Musa yayi yace “shegge nawa tun yanzu kafara rawan jiki haka bare kuma kasha kindirmo” bugamai filo Nura yayi yana murmushi Musa yace “Nura kalleni nan, auren nan auren hutu ne da shakatawa dakuma more rayuwanka, Allah yabaka dukiya, yabaka yara, me kake nema banda jin dadi? Matarka taki kwantar maka da hankali tunda yanzu Allah yabaka Ummi enjoy your life da yarinya danya abinka, fresh yarinyar ni irinsu Ummi I still consider them virgins wlh, to tun suna yara akai auren nan, she’s semi virgin, gata da natsuwa ga kirki, she can cook, gata she’s not expose duk inda ka juya yarinyar nan zata juyun maka meyafi haka dadi? Enjoy your self abokina our 50’s can never be boring duk wacce tace bazatai corporating ba ajiyesu kadauko wacce zata bada hadinkai kaji dadi, kagama amarci dai tukunna nima kauyen nan zan shiga na dallo amarya ita wanchan tajika farantin nata tasha tunda ta tsufa dan wlh ni ban tsufaba ina mahaukacin son farantin nan, cheers to enjoying our 50’s Nura” cheers sukayi suna buga cups na magungunan basir sha suna dariyan keta, Musa yace “wayyoo kindirmo, Nura kawa Allah kagama amarci muje kauyen nan nima na zaba na dirja, mai manyan kindirmo zan dauka” murmushi Nura yayi shima he can’t wait yasha nashi kindirmon.
***
Chapter 22 · 0% Book details