Sashe 28
Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaman bazata daga wayanta ba saikuma ta daga tace “Ya akayi Hadiza”? Dan shiru Hadiza tayi saikuma chan tace “Anty Jams kinga ko akwai wani kalan silent bakin and cool mugunta da Nuri ya iyamin dake cimini zuciya, yake kuma bakantamini rai” yanayin yanda Anty Jamila taji muryanta yasa tace “yanzu kuma meya faru?” Cikeda damuwa sosai kaman Hadiza zata fashe da kuka tace “tun bayan sakin nan Nuri ya chanza gabaki daya, wlh bana gabanshi at all baya kulani, yau 5days kenan daya kwashe su Amal da Aman I have no idea inda yakaisu, ranan yadawo ya kwana agida to tun ranan bai kara kwana agida ba yau 4days kenan baya kwana agida, kuma bai sanar dani zaiyi tafiya ko zaije wani wajeba, ranan danai noticing bai kwana gidaba I called him da asuba ina tambayanshi yana ina ke kinji yanda yake amsani ne kaman ba Nuri na ba, yana gayamin banda right na in sani daganan ma kashe wayan yayi Anty Jams har yau nakira wayanshi akashe, wani zubin kona kira naji call waiting yana gama wayan dazaiyi saiya kashe, i WhatsApp him, namai dropping imessage, namai sako a IG duka babu wanda bai duba ba yaki kulani, bakiji yanda kirjina kemin daci ba wlh jikina nabani wani abu ina yake? Ina yaje yana kwana? Yana ina?” Duk sauraron ta Anty Jamila tagama tace “meya jawo ya barmiki gidan?” Danshiru Hadiza tayi tace “nasan ina gayamiki zakihau mini masifa but please understand me Anty Jams this is Abuja city of wealth, this is how we roll, Anty Jams kinsan menene yar aikina Ummi nan tayi tafiya zuwa kauyensu an kirata wai kanka ta ba lafiya bla bla bla shine ta tafi, ranan dana dawo kaman yaran nan zasu kasheni da aiki haka na dafa mana indomie Anty Jams wlh ni nama manta yanda ake girki yanzu I can’t even stand heat din kitchen ai sai fatana ya kode bayan uban kudin danake zubawa a skin care dina” “sannu diyar qaruna, idan akaji kina magana wani zai dauka Obasanjo ne ya haifeki ko Bill Gates, Hadiza nasan ni yayar ki ce i oath to support you but listen wlh wlh bazan iya supporting wannan rayuwan dakikeyi ba ayanzu, Hadiza this is not you ba tarbiyan nan Mama tabamu ba, ni kafin kigama bani labarin nama gane karshen nasan kinki yin komine ya kwashi yaranshi yakai inda za’a kula dasu, Hadiza you’ve failed as a wife already, yanzu kuma you are failing as a mother ace yaranki just su biyu bazaki iya kula dasu ba Nura ya kwashesu yatafi dasu wani waje” rai abace Hadiza dake fama da bakin cikin Nura tace “Anty Jams I think this is the last time zan kara kiranki nagaya miki damuwata for crying out loud when will u drop all this sentiments da mentality kusayawa yan kano and just look at me like an educated smart lady data zagaye kasashen waje? Eh fisabilillahi fa, kinzo abujan nan infact kinada friends ma acikinta, kinga yanda muke rayuwa maisa bazaki fahimce ni ba Anty jams? Menakeyi that is wrong eh menakeyi? Ba’a taba kwana agidana babu abinci ba inada mai dafawa, yarana basu taba kwana basu sami wankan safe da dare ba before bed, kome sukeso dafa musu ake, sau nawa ina cire kudi nai order expensive kids wears bama da kudin Nuri ba na sayoma yarana kaya? Bawai ina cewa Nuri baya saya musu kaya bane zai daukeshi da kanshi yakaisu different kids stores kome sukeso ya saya musu but ni kwaso musu uban kaya nake na kyalekyale different things sai kinje wardobe nasu zaki gani, headbands, ribbons menene menene I know how much nake kashema yarana, Aman nada every single collection na kids shoe da gucci suka fitar this year, Little Amal nada birkin ga receipt na handbag din worth millions duk da kudina na saya musu da zinarai, dan kunnen diamond stud ne yanzu haka a kunnen Amal ninai order shi, menene ban musu? I buy heaven and earth for them duk yar aikin dazan dauko da basaso koranta nake straight cus I wanna make my kids comfortable sune life dina, I gave them the best yar aiki dasukai approving, sukeso kuma Ummi can Babansu do that for them?? Nuri baida time na kallon yan aiki na ma balle yasan wanne yaranshi sukafi so I did all that on my own to akanme zakice I failed as a mother ko as a wife? Anty Jams Nuri yataba gayamiki yadawo daga office babu abinci agidan nan? Ba abinci about kala biyu akan dinning cikin warmers?? Ko yadawo yaga dakinshi ko bayinshi da datti ko singlets da boxers nashi ba’a wanke ba? Bazaki taba shigowa gidana ki ga datti ko daya ba akasa ko ki taka kasa, ko issues damuka samu this time kan Mamanshi sabida rainin dayamin ne sai bayan yace suzo zai sanar dani amman tunda mukai aure nataba samin matsala da uwarsa? No, mukaje kano mu sauka agidan nadan wuni daganan na gudo gidanmu so menayi? Police dana dauko is because Shegiyar kanwarsu had the audacity tashigo har gidana ta nemeni da fada tana zagina takuma yakusheni da kumbunan vampires nata, I need to show them no one can bully Hadiza in her house, so Anty Jams menene kike fadamin? Inada damuwa which kinsan bazan iya fadama friends dinaba sumin dariya bayan cika bakin danagama yi na inada karfi da iko agida suga abinda mijina kemin, I called u cus kene sister na and look at wat u are telling me eh, nayi deserving abinda Nuri kemini? Ya dannamini saki daya yanzu kuma ya maidani thrash ya kwashe yarana, shima yabar gidan yabarni ni kadai inata kwana agidan nan kaman mayya, sannan ina kiranshi yana kashe waya kuma nasan yana kunna wayanshi dan nasan dole yakira mamanshi kuma yaga messeges dina yayi ignoring, ina gayamiki kina mini masifa that i failed as a mom and a wife what have I done? Menayi? Eh”? Duk yanda taso ta daure ta rike zuciyanta kartai kuka takasa sai kawai tafashe da kuka awayan ita karan kanta bazata iya misilta kalan zafin datakeji ba na yanda Nuri ke soyata a pan dinan, ance dama blood is thicker that water wani iri Anty Jamila taji hakan yasa cikeda lallashi tace “Hadiza kinfi kowa sanin yanda nake sonki, tun kina yar karama you’ve always being my DiDi, Hadiza mun taso cikin tarbiya mai kyau muke aikin gida I remember lokacin idan yau nine da shara to kene da wanke wanke, the next day nine da wanke wanke kene da shara same goes for girki, Hadiza Baba da Mama nada rufin asiri mun taso bamu rasa komiba but we were trained muma kanmu komi muke wanki, muje aike bamu da yar aiki Hadiza, mun taso munga yanda Mama kema Baban mu girki tabashi, tamishi komi, Nura ya nuna shi girkin ki yakeso yaci how many minutes zai daukeki kimai? Is just breakfast and dinner da rana yana office, Hadiza Nura ba dan Abuja bane that’s wat nakeso ki gane bazamfare ne girman kano, ya nunamiki he doesn’t want the Abuja lifestyle dole ne saikinyi lifestyle din to please your friends and co? This is peer pressure Hadiza, must u do abinda kikaga anayi agarinku? Anyi magana kice feminism you know your rights Nura yafiki sanin rights naki tunda har mutumin nan zai bude miki kasuwanci ya daukeki kuje garuruwa ki samo contact na suppliers ki saro kaya, Hadiza Nura na mugun sonki how many men zasu iya ma matansu abinda Nura yamiki yet baki da wanda zaki cima mutunci sai shi sabida kinganshi shiru shiru baida hayaniya kuma yana sonki saikikai abusing simplicity nashi” hawaye Hadiza ta share cikin muryan kuka tace “Anty idan baka rikema maza wuta ba cin ubanka suke, ga Baraka nan mijinta juyata yake kaman lagwani, yahanata business kudi sai wanda yaga dama zai dan yammata, gashi da mata ihu agaban kowa haka kikeso Nura yamaidani? Ya takani duk sanda yaso? Noo bazan yarda ba wlh, fire for fire yanzu shine new system na zaman lafiya tsakanin mata da miji agidan aure” Anty Jamila tace “Noo fire for fire is never option, look at you yanzu jibi yanda kike kuka kina bala’in son mijinki but girman kai da al’adan yahudu da nasara yasa you are gradually loosing him” dasauri Hadiza tace “I reject it Anty Jams, bazan taba loosing Nuri na ba, yana bala’in sona, duk yan uwanshi ne da Mamanshi suka gama zugashi, Nuri baitabamin hakaba, Nuri kome zanmai baya fushi dani, baida riko ko ijiye mutum azuciya, he will still come back to me and talk to me and call me, Nuri na baitaba shareni ba, wlh all this aikin Maman shi ne da kanwarsa kuma muzuba da ni da su” girgiza kai Anty Jamila tayi zatai magana Hadiza ta tareta tace “karki damu you’ve said enough Anty Jams ko’ina Nuri yaje zaizo har nan har gidan nan yasameni bawai ina kukane sabida abin yawani dameni ba, kukan danakeyi na bakin ciki ne cus nine yakamata na dinga cusama namiji kalan bakincikin nan ba namiji ya dinga cusamin ba ninefa Anty Jams is still me Hadiza bakatakani bama nabaka hot-hot balle kuma katakani, wlh Nuri zai gane ni yagasama aya a heart, saida safe” bama ta jira amsan Anty jams ba ta katse wayan ta ijiye wayan tanabin dakinta da kallo gidan gabaki daya bayamata dadi sabida yanda ba kowa ciki, mutum rahama ne hayaniyan yaranta is something, kawai she’s not enjoying komi, mamaki take take kuma karayi itane Nuri bazai returning call nataba, lallai Nuri don get liver, tasaba saidai ita ta katsemai waya amman wai itane ya katsema waya tun ranan yaki kiranta back, yaki replying messege nata, hmmm takasa yarda ita Nuri zaima haka cus baitaba mata iskancin maza haka ba tunda sukai aure sai yau, da wannan abin har gwara ya mareta ma eh tasan mari ne bakaramin shiganta wannan silent da ignoring attitude din da Nura yamata ke damun zuciyanta ba.
****
****