Sashe 12
Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Daidai yana parking awajen parking wayan Amina nashigowa fitowa yayi daga motan yana daukan wayan yace “okay ku jirani a arrival din gani nan zuwa” wucewa yayi tun kafin su ganshi ya hangosu, wata tsohuwa ce fara mai zanen kalangu a fuskanta zaune kan wheelchair dawata budurwa da akalla zatai tsaran Ummi ke gungurawa ga akwatinan su kan cart a gefe tareda mutumin dake turawa, ahankali tsohuwan matan tadago idanunta dan taji alamun danta ajikinta hakan yasa sai waige waige take, ta baya yazo yahada idanu da Amina daya mata alamun kartai magana sannan yataho kawai Hajiya ganinshi tayi agabanta ya tsaya bai damu da airport sukeba tsugunnawa yayi yasa guiwowinshi akasa yana kallon fuskan mahaifiyar tashi data washe baki ganinshi tace “me haka tashi tashi kayanka zasu baci, yanzu kasan banda karfi balle na wanke maka” ahankali yakai duka hannayenshi yatallabo fuskan mahaifiyan nashi yace “bance kada ki kara ciwo ba eh Hajiya?” Cikin barkwanci tace “ai dazai tasomin saida nace kai rashin lafiya ka manta kashedin da Nura yamaka ne kakeso kadawo kuma” dan murmushi yayi duk rashin lafiyan Hajiya bakinta is always there baya fatan tai rashin lafiyan dazai hanata magana har abada In sha Allah. Rungumeta yayi ahankali yace “barka da zuwa Mamana, Allah yabaki lafiya Hajiya, Allah yasa kaffara ne” bayanshi ta shafa tace “Ameen Ameen ai naji sauke Amina ai bata kyautamini ba banso ta tadamaka da hankali ba wlh, tashi daga kasa kaga jama’a sai kallemini d’a suke yasa guiwa akasa” batare daya saketa ba yace “albarkan mahaifiyata nake so” murmushi tayi tace “Allah maka albarka Nura, Allah ya lura dakai kaman yanda kake lurada ni, Allah yasa yaranka sumaka yanda kamini Nura, yanzu tashi mutafi kaji dan albarka” anatse yace “to Hajiya” sannan yadago yabama mai cart hannu suka gaisa sannan yakalli Amina hannu yabude mata dasauri ta rungumeshi tace “Yaya ina yini” kanta yashafa yace “lafiya lau Autan Hajiya” wheelchair ya karbe yashiga tura Hajiya da kanshi har mota saida ya zaunar da Hajiya tazama comfortable sannan ya sallami mai cart suka shiga mota suka tafi, Hajiya sai kallonshi take ta madubi tanamai hira tace “amman kai rashin lafiya ne ko Nura? Naga kafada sosai”? Dan murmushi yayi yace “aiki ne wlh Hajiya” ijiyan zuciya tasauke tace “to Allah yabaku sa’a kadinga hutawa kanacin abinci akai akai kaji ko” “to Mamana” ya amsa yana murmushi, tace “nataho maka da danderu” baki yabude yadan juyo zai kalleta dasauri tace “kul maida hankali tuki kake” dan dariya yayi yace “Meenah ya akayi akabar Hajiya tawuce da danderu”? Dan dariya tayi tace “ba anga batada lafiya ba babu wanda yayi musu da ita” murmushi kawai yayi yace “inason Mamana Ameena sosai” Hajiya data washe baki tace “nima inason d’ana sosai” Ameena ta turo baki tace “Hajiya nifa” dan dariya Hajiya tayi tace “Inason ku duka akwai wanda ma yasamu soyayyata irinki Auta na” ahaka suna family hira sukakai gida Nura yace “specialist danai consulting yace zai ganmu by 12 yanzu zakici abinci kihuta anjima saimuje asibitin ko” yayi maganan tareda yin Parking yafito da ita sabida dakali da kafanta tayi tafiya tana rikeda shi suna tafiya ahankali Ameena biye dasu tana kallon hadadden gidan, bude kofa sukayi suka shiga ciki wani lafiyayyen kamshi yamusu sallama dasauri Ummi tafito daga kitchen tazo har tsakiyan falon ta duka tace “sannu da zuwa Mama, ya hanya ya jiki, Allah yabaki lafiya Mama, Allah yasa kaffara ne” washe baki Hajiya tayi tana kallon Ummi tace “waye wannan yarinyar mai ladabi ba irin su Auta ba da basu gaida mutane da kyau, ga iya addu’a, waye ita”? Dan murmushi kadan Nura yayi yace “Ummi sunanta” daidai Hajiya na zama, Hajiya tasauke ijiyan zuciya tace “jiki Alhamdulillah Ummi, sannu kinji Allah miki albarka tashi tashi ki zauna, ina Hadiza? Nasan jikoki na ana makaranta ina Hadiza?” Hajiya takara tambayan da zuciya daya tana waige waige neman Hadiza, cikeda hikima Ummi tace “tadanje tadawo wani uzuri yakamata amman tace na kula dake da kyau kome kikeso namiki” sosai Nura ke kallon Ummi yanda yarinyar keda hikima baitaba sanin zata iya fadan magana hakaba, dariya Hajiya tayi tace “ayyooo” kallon Amina data shigo da jaka Ummi tayi gateman biye da ita da kayansu da sauri ta tashi tace “kawo nakai miki daki jeki zauna kihuta kinsha hanya” murmushi Meena tayi tace “thanks” kai kayan sukayi sama sannan Ummi tadawo tashiga kitchen a tray tajera abincin Hajiya da ruwa a bowl mai kyau na wanke hannu tafito takawo har gaban Hajiya, Hajiya tace “Ayyah sannu da aiki Ummi, Allah dai yasa cimata ne dan yanzu bakomi nakeci ba, cuta batayi ba” tai maganan tana bude kulan ganin tuwon Alkama da miyan zogale dayaji ganye yasa Hajiya tace “laaaaaaa Hadiza tamin girkin nan kafin tafice” dasauri Ummi tabude baki zatace eh Nura yace “Ummi ta dafa miki Hajiya” kara kallon Ummi Hajiya tayi saikuma ta nunawa Meena Ummi tace “kinga girkin sa’onninki ko ke sai shegen kiwuya, wai wannan kamshi haka bari naci abincin nan akasa zan zauna ma” da taimakon Nura tazauna akasa ta wanke hannu takai abincin baki saita kalli Nura takuma kalli Ummi takara kallon Nura again tace “Ummin nan dai danake gani tai girkin nan”? Gyadamata kai Nura yayi sai kawai Hajiya tace “Allahu Akbar wlh tayi girkin yanda nakeso, kaga ba gishiri ba magi, sannan bata sakamin jan nama ba hanta da Koda kadai ne amiyan, cimata tamin kuma yanda nakeso, bani jakana Meena kigani” bata jakanta Meena tayi Nura ya karba, dasauri Hajiya tace “ciro duka kudin dake purse dina” murmushi yayi ba musu yaciro dubu goma da dari biyar ne ta karba tamikama Ummi tace “ga tukuicin ki dan kin dadada mini rai kinsa natuna na diyata Aisha mai bin Nura tana aure a eygpt ita kadai kemini abinci irin wannan taste din wannan tarban da akamin bazan taba mancewa da ita ba, nagode ko Ummi amshi kudinki” akunyace tace “Mama kibar shi ni nadafa miki ne kawai wlh” Hajiya tace “laaaa ungo amshi nace” dan satan kallon Nura tayi shima kallonta yake ahankali yace “bazaki amsa kudin Hajiya ba kinsan kalan makon Hajiya kuwa? Ba kasafai akecin kudinta ba, ke kinyi sa’a tabaki” dariya duka sukayi harda Ameena, Hajiya tace “atoh dan haka karbi abinki” gently Ummi tasa hannu ta amsa ahankali tace “nagode Mama Allah ya ninka miki dubun su” Hajiya tace “Ameeen Ameeen” Ummi na murmushi takalli Ameena tace “nadafa miki shinkafa dafa duka dakuma taliya na manja wanne zan kawo miki” dasauri Ameena tace “taliyan manja” harzata tashi saikuma tadan kalli Nura dake kallonta kasa kasa tace “Alhaji mezan kawo maka bakayi breakfast ba kaima” abincin Hajiya yakalla yace “zanci abincin Hajiya” gyadamai kai tayi tawuce kitchen karaf akan idanun Hajiya yanda Nura ke kallon yarinyar amman batace komi ba, saida sukaci sukai kat Ummi takawo mata juice na cucumber kadai data mata Hajiya tasha sosai sannan Nura yakaita sama dakinsu dakin dake kusada na Hadiza inda Hadiza ta kwana ranan ta gyara Hajiya ma sai complain take ita batason sama Nura yace yafiso ta kwana inda zai dinga jin motsinta hakanan ta hakura.
Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.
Wuraren 12 suka fice asibiti Ummi tasake gyara gidan.