← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 97

Sashe 56

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kiran Ya Aisha tayi ringing daya Ya Aisha ta katse wayan takira Unmi back kafinma Ummi tayi magana tace “Ummi ai dama ina shirin kiranki yau nace kwana biyu bamu gaisa ba, to ya kike” cikin muryan Ummi da baya fita sosai tace “lafiya l…..” “Ummi, meya sameki kikai kuka haka har muryanki ya chanza”? Ya Aisha tai tambayan da sauri Ummi tarasa mesa aka tambayeta sai tahau kuka da kyar tace “Ya Aisha kiyakuri kada kiyi fushi dani saisa nakiraki inaso ki lallashi Hajiya itama kada suyi fushi dani amman zan tafi kauyenmu wajen Gwaggona gani nan atasha” dasauri Ya Aisha tace “mene! Ummi! Mesa zaki tafi? Meya faru? Fadamin kinsa gabana nafaduwa menene”? Ahankali Ummi ta rairamata komi daga AzuwaZ Ya Aisha zuciyanta yafara tafarfasa sosai tace “sabida yar gwal dinshi zai wulakanta ki? Ai wlh Ya Nura kaman na dakeshi wani zubin bantaba ganin kalan mutum mai zuciyanshi ba Mata tazagi mahaifiyar ka ka kasa komi haba” tayi shiru tana sauraron yanda Ummi ke kuka tace “Ummi kema saiki tashi kitafi mesa baki fadama Hajiya ba? Hajiya bazata taba bari Nura ya wulakanta kiba wlh yayi kadan yayi irin abin nan agabanta ai shi yasan waye Hajiya idan tai fushi ko duka kano zasu hadi ba’a iya lallaso ta kuma wlh bazakije Adamawa ba zai gane yamiki laifi yaje har garinku ya auroki marainiya dake shine yanzu zai fara wulakantaki wa zaki kalla kiji dadi? Zaman wa kike? Yan uwan Hadiza sumiki kinyi shiru sunzo gıda sun gaje kitchen though nagane dalilin dayasa Hajiya bata musu magana ba amman dudda haka gwara dakika barmai gidanshi dan suka dawo ma wulakancin saiyafi nada….” Ya Aisha tahau surfafa masifa kafin chan tace “Ummi kiyakuri kinji amman dan Allah kada ki rabu da Yayana but na yarda yanzu kada ki koma gidan kiyi fushi dashi amman dai kada kirabu dashi wlh zai koma gidan jiya kin tsamoshi daga kangin dayake ciki kin maidashi mutum kin rufamai asiri kuma ke Ummi kinma Ya Nura komi fan Allah kada kiyi fushi dashi yanzu kinsan mezamuyi zan kira wani kanın Mijina yazı ya daukeki ya kaiki gida zanyi arranging komi amiki international passport da visa da sauransu Mijina duk yanada hanyan da za’amiki fast saikizo wajena Ummi zan gyaraki wlh sai Nura yamiki kuka kafin ki koma wajenshi kinji dan Allah Ummi kada ki koma garinku” Ahankali Ummi tace “Gwaggo na bazata yardaba nariga nagaya mata zan dawo gida” dasauri Ya Aisha tace “kira Gwaggo hadamu conference call kin iya hada conference call”? Ahankali Ummi tace “a’a” Dasauri Ya Aisha tace “turamin number ta” tura mata number Gwaggo tayi sunyi waya mai tsaye sannan Aisha tasake kiranta tace “Gwaggo tace takirata” kiran Gwaggo Ummi tayi tana dauka Gwaggo tace “kije wajen kanwar nan nashi Alhamdulillah yan Yan uwan shi duka suna sonki, kidena kuka zamuyi magana idan kinkai gidan kanin mijinta ki kashe wayanki but kullum kidinga kunnawa kina kırana sau daya muna magana inji lafiyanki kuma nagayamata kada tafada ma kowa kina wajenta tace haba bazata fadi ba, bari Nura yadawo daidai zai gane yayi rashi, jikata daya ce tak acikin mata miliyan” katse wayan tayi Ya Aisha takira tace “me Gwaggo tace”? Ahankali Ummi tace “tace naje wajenki” murmushi Ya Aisha tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulilah kina tashan jabi ko” Gyadamata kai Ummi tayi tace “um” nan da nan ta katse wayan kafin chan tasake kiranta tace “gashinan zuwa nabashi number ki kada ki kara kuka Ummi, kinga maza wlh halin maza saisu saisa wasu ke cewa gwara kaci ubansu dan sunfison matan dake basu wahala suke basu kashi ada ban yarda da maganan ba but wlh yanzu akan yayana uwa daya uba daya na yarda, idanma tunani yake baki da gata wlh baiyi tunanin da kyau ba Ummi nadade banga Kakan dakeson jikokinta kaman Gwaggon ki ba ko ita kadai ta ishi ya Nura ai zaije kauye nemanki wlh saitaci mishi mutunci, butulu kawai gwara da kika bar musu gidan indai Hadiza ne gashi ga ita ai hali zanen dutse mai hali baya fasa halinsa ayi soyayya agama yanzu idanunshi zasu budene ya nemeki”.
Sosai Ya Aisha take mata hira awaya just to ensure bata kara kuka ba har Faisal yazo ganin call waiting na shigowa wayanta yasa Ummi tace “wani number nakirana Ya Aisha” dasauri Ya Aisha tace “shine dauka” katse wayanta tayi tadauka suka gaisa yace “ina gaban yola line kina ina”? Tashi tayi ta taho wajen harta ganshi suka gaisa yabude mata baya tashiga tazauna yabata ruwan gora mai sanyi ta karba tamai godiya suka tafi gidansu mai kyau babba ne matanshi dakeda tsohon ciki tama Ummi sannu da zuwa suka kaita daki lafiyayye matan tazauna da Ummi sannan tafita takawoma Ummi abinci da drinks da kayan sawa da yawa tasamata a sip Ummi tamata godiya.💫MATAN?? Ko MAZAN??💫

✍🏻M SHAKUR

EPİSODE 2️⃣1️⃣
Ina mata masu sha'awar koyon sana'ar saƙar kwarashi ta zamani?
Ko kina da labarin Heart Stitches kuwa?
Zata fara online classes na koyarda sakar kwarashi nan bada jimawa ba.
Ita wannan saƙar idan kin iya ta, kina zaune gidanki zaki dinga yi kina saida abun da kika saƙa cikin sauki.
Gashi kuma tana saida haɗaɗɗun handmade bags.
Ki shiga group ɗinta domin ƙarin bayani ga link din 👇🏼

https://tinyurl.com/bagsstitcheshaven

Kiyi following page dinta kisha kallo.
https://www.instagram.com/heart_stitches77
Zakuma ku iya chatting nata up ta hanyar danna this link;
https://wa.me/2347034845999
Chapter 56 · 0% Book details