← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 97

Sashe 71

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya jitayi kaman akwai dutse akan zuciyanta duk yanda zatai bayani bazaku fahimta ba Nura is her only son, shine amatsayin mahaifi ga duka kannenshi mata, shine komi nasu, shine school nasu, shine kayan dakinsu, shine komi, shine abincinta, maganinta daidai da electric bill na gidan nan da swan bottle water datake sha da komi ma shine and Hadiza is trying to kill her son for her, bawai ta tsani Hadiza bane but zuciya batada kashi, datake Abujan nan taga abinda ke faruwa Hadiza ta siremata tatas daga zuciya babu uwar dazatazo matar dake wulakanta mata dan datasan zafin haihuwan shi, Hadiza fitinanniyan mata ce ta fitini danta haba! Aisha takira wacce itace gist partner Hajiya dan banda Nura itace yatta tabiyu kuma kunsan mata da iya relating to pain din maman su.
Aisha na kiran Hajiya back Hajiya tafashe da kuka tace “Aisha Hadiza zata kashemini yaro wannan wani kalan abune me d’a yamata? Aisha cikinku babu wacce kema mijinta yanda Hadiza kema Nura, kunama mazanku girki, kuna girmamasu, why is my son so unlucky da mata eh? Kashemin yaro takeso tayi? Zata haifamin waninshi ne eh? Yarona sai kuka yake all because of her, why are so women so heartless? I know babu excuse na marin mace, Nura was very very wrong daya mari Hadiza, mari ba kyau musulunci yahana amman akwai forgiveness a aure, tsakanin mata da miji yakamata akwai yafiya, jinkai tausayi wanda duka naga Nura nama Hadiza, what’s the point na makashi a kotu uban yaran dakika haifa aduniya fa, sabida ya mareki? Idan ma so take abimata hakkinta for marin daya mata she can call me wlh saina sabamai, zata iya kiran mahaifinta takai karan Nura akira amai kashedi kada ya kara taba lafiyanta, kotu all sabida mari is too harsh, so take Nura ya wulakanta aduniya dayau beda kudin bail da yana gidan yari yanzu haka, ga yarinya mai ladabi da biyayya ya aura amman hankali shi baya kanta yafison wacce ke bashi kashi wai yaya kan maza yake ne mesa sun fison abinda ke cutarda su? Hadiza ce kadai mace aduniya akan wani dalili zata dinga wulakanta min da shirun dataga nayi ta dauka tsoron ta nakeji koko ta dauka bansan darajan dan cikina bane”? Cikeda lallashi ganin ran Hajiya na tafarfasa Ya Aisha tace “Hajiya please stop crying is not good for you kada su Meena su jiki suzo suna kuka suna duk hankalinsu yatashi” cikin kuka Hajiya tace “basanan sun tafi lesson din da Meena keyi da ita da Ummi, Aisha I don’t care Nura ya haihu da Hadiza sunada yara all I know shine ko yau Allah zai dauki yara koda Ummi bata karbesu ba ku zaku amshesu bazasu taba wulakanta ba Aman da Amali, wlh wlh idan yarinyar chan takaini bango karshen auren su kenan koda Nura zai maidata saina hanashi, if she’s not ready ta zauna da yarona let her go gabaki daya” calming Hajiya down Aisha tayi sosai, tadinga bata hakuri da kyar tashawo kan Hajiya ta huce tayimata hira har saida su Meena suka dawo gida sannan tabarta tamata sallama.

Saida sukai magrib suka wuce gida, Nura na sallama su Amal da Aman dake wasa da yaran Alhaji Musa afalo suka taho da gudu suka rungumeshi suna oyoyo Dady, yaran Musa ma haka boye duk wata damuwarshi yayi yayi murmsuhi suka daddauki yaran suka shigo gidan cikeda girmamawa Maman Humaira ta gaida Nura ya amsa Humaira ma ta gaidashi cikeda girmamawa Nura ya shafa kanta yace “Humaira is now a big girl fa yaushe aka haifi Humaira nazo na dauketa a baby showel a hospital” akunyace Humaira ta rufe fuskanta duk akai dariya, abinci Maman Humaira takawo akaci suka fice dan yin isha’i Humaira ta wanke komi da sukai amfani dashi suna dawowa daga mosque suka tafi gidan yarage daga Nura saisu Aman dake wasa da toys akan rug, dago kanshi Aman yayi yakalli Babanshi saikuma yabar toys din yahayo kan kujeran yazauna kusadashi ahankali yace “Daddy are you fine?” Dasauri Nura yakalleshi saikuma yamai murmushi ganin yanda yaron ke kallonshi yace “yes Dady is fine” dasauri Amal itama tabar wasan ta hayo kujeran ta zauna kan cinyanshi takai hannunta ta taba fuskanshi tace “Dady you look very sad today right Ya Aman?” Gyadamata kai Aman yayi yana kallon Baban nashi shima, murmushi Nura yamusu baice komaiba sai kawai ya kama kansu ya manna musu peck cikeda so, ahankali Aman yace “Dady where is Mom? Bata dawoba” shiru Nura yayi yana kallonsu they have the right susan meke faruwa dudda yarane, anatse yana kallonsu duka biyun dake kallonshi kur kaman tv saikuma yakama hannunsu cikin tsantsan so da kamanta magana ta yanda yara zasu fahimta yace “Mommy will not be living with us again, Daddy is not together with Mommy” Sosai yaran ke kallonshi sukai shiruu dukansu biyun suna kallon fuskanshi chan Aman yace “Momy started doing those bad things again right Dad? Is that why your eyes are read”? Dasauri Amal abunku da yarinyar takai duka hannayenta kan kumatun Babanta tajuyo da fuskanshi saitin nata tawani leka idanunshi kaman wacce ke leka rijiya, cikin muryan yara tace “Mommy hurt my Dad, Aman daddy eyes are red like he criedddddd” taja cried din tana sakin kuncinshi tai kwaba kwaba da fuska zatai kuka da sauri Nura yace “no Amali don’t cry ni banyi kuka ba, Dady ai baya kuka, idanuna na ciwo ne saisa sukai ja” ahankali Aman yakama hannun Babanshi shima kaman zai fashe da kuka yace “Dady I promise I will never hurt you like Mommy does, and we will never ever yelled at you or scream or be stubborn ko Amali”? Gyadamai kai Amali tayi ashagawabe tace “I love my Dady very much Ya Aman I hate seeing my Daddy looking sad” ta rungumeshi, Aman shima ya rungumeshi yace “Dady you are my superhero and I love you alot Dad, you are the best Dady don’t be angry kaji Dady, kayakuri, Anty Ummi said Innallaha….” Dasauri Amali ta taso daga jikin Baban tace “ma’a sabireen” atare suka hada baki sukace “lalle Allah yana tare da mai hakuri, Dady kayakuri kaji” gyadamusu kai Nura yayi yanaji kaman yayi kuka maganansu ya mugun sosamai zuciya kawai ya rungume yaranshi kowanne side side gam gam, arayuwanshi yanason yaran nan, su biyun nan are his soul, yaranshi are just so adorable and sweet kuma suna sonshi sosai, sai yaji Ummi takara shiga ranshi, akwai some small small abubuwa datake koyama yaran da he so much appreciates, kaman son junansu tanunama yaran su biyu are one and Aman should always take care of Amali, wlh dawuya kaga Aman da Amal nafada ko sunyi sharp sharp zakaga Aman ya rungume Amali ya lallasheta he’s so protective of little sister nashi and is all thanks to Ummi da yan tatsuniya da labaran datake basu. Banda haka kana ganin kaman basusan meke faruwa ba they understand everything, saisa ko fada bayaso yanayi da Hadiza agabansu especially Aman dan yaron is very smart.
Sun dade ahaka saida yaji dukansu sunyi bacci sannan ya daddaukesu yaje ya kwantar da su adakinsu, wanka yayi anan bayin Aman yafito yaje dakin Ummi yadauko wani jallabiya yasaka yadawo dakin Aman ya kwanta yayi shiruuu sai chan hawaye ya gangaro daga gefen idanunshi dasauri yasa hannu ya share tareda fuzar da iska yace “enough!” Tashi yayi yadauki wayanshi yaciro number Hadiza yayi deleting, yashiga files nashi yashiga deleting komi nata messages, pics, yashiga whatsapp yayi blocking nata ta ko’ina, ya maida settings na wayanshi ta yanda unknown number bazai iya kiranshi ba, yanaso from daren yau yarufe babin Hadiza gabaki daya and just move on with his life, harga Allah he wish her well koba komi itane mahaifiyar yaranshi he wants her to get everything datakeso in this life to tayi rayuwan datakeso, he wants her to excel and attain success in business nata, but for him ya yafe Hadiza koda zai mutu he don’t wanna ever be together da mace kalan Hadiza ma balle Hadiza, he just wanna live his life yanzu da wacce keda opposite of all abubuwan da Hadiza kedashi.
Washegari as usual da wuri ya tashi yana dawowa tea yashiga kitchen yamusu yayi microwaving abincin da Maman Humaira ta dafa yayi arranging komi a dinning yaje sama yatadasu ya musu wanka brush yasa sukai salla yafito yabasu abinci tsaf suka cinye daidai wata babban mota na zuwa gaban gidan, sama yakai yaran dakinsu yabasu iPad nasu sannan yafito ya shigo da maza su 7 aka shiga kwashe kayan gidan ana fitar da su, dudda duka kayan gidan na Nura ne, dasukai aure da kayanta aka kawota gidan su na Kano dazasu dawo Abuja yasa ta kyautar da komi yamata komi sabo but he wants her to have it dan Allah yasani da sunanta yasai everything agidan kap, kayan dakin Ummi da gadajen dakin yaran ne kawai ba’a taba ba but hatta kujerun falon sama tass aka fitarda komi gidan looks empty yar kayan kitchen, frames menene menene, address na gidan iyayen Hadiza yabasu a kano yariga yabiyasu kudinsu aka tafi sosai ya tsaya yana kallon gidan da babu komi ciki banda pentin bango, kawai yawuce sama dakin yaran ya shiga yahada kayansu tsaf a akwatinan su dan idan yabar gidan nan sabon gidanshi zasu koma next time, shima ya tattara kayanshi awani akwati yasauka kasa shida mai gadi suka ijiye a boot already yaran sun gama exam badai suyi closing school ba tukunna amman yakira school nasu yagayamusu tafiya takamashi yadawo yadaukesu suka sauko yasasu amota ya kulle gidan yashiga mota office yaje yayi some ayyuka da komi yabarma manager shi aikin sannan by 2:00 suka tafi airport dan 2:45pm jirgin zai daga, yaran were so happy zasuyi tafiya they’ve missed traveling daganan sukai flying sai kano inda direban Hajiya ke jiransu already.

Kuna ganin Nura made the right decision na rufe chapter Hadiza gabaki daya in his life??

Koko kuna ganin is not the right decision daya kamata yadauka??

Me aganinku yakamata yayi??

In his statement “I want mace complete opposite na Hadiza” yana nufin wacce is not as educated as Hadiza, expose as Hadiza dadai sauran su, kuna ganin that’s the best thing for him??
Chapter 71 · 0% Book details