← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 97

Sashe 57

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

21
Wajajen magrib suka shigo gidan as usual Meena direct dakinsu tawuce dan ranta amugun bace yake tun dazu darana duk wanda ya tambayeta meke damunta tace ciwon mara take, binta da kallo Hajiya tayi ta kwalama Ummi kira ganin bata afalo. “Ummi Ummi” tabe baki su Rabi sukayi suka wuce ciki Hajiya tace “hala salla take nima bari naje nai salla” mahaifiyar Hadiza tace “ina gani kam dan da yanzu tazo tamana sannu da zuwa” wucewa daki Hajiya tayi ganin Meena kan gado yasa tace “Waike lafiyanki kalau kiketa kumbure kumbure ke kadai” tana kwance kan gadon tace “cikina ke ciwo Hajiya” kanta Hajiya ta shafa tace “sannu to kinji Auta na” dan murmushi kadan Meena ta mata Hajiya tawuce tazaga bayan gida tayo alwala tayi salla tana zaune kan dadduma wanda dama haka take har akai ishai tayi tai yan addu’o’inta tashafa saikuma cikeda damuwa tace “Meena kinga je sama dan Allah ki dubomin Ummi bantaba shigowa gidan nan nakai war haka yarinyar nan batazo wajena ba, kinji muryan su Aman fa suma sai kwalamata kira suke, tashi dan Allah dubomin ita Allah sa lafiyanta kalau ba zazzabi bane ke damunta dan abinda zai hana Ummi saukowa gaisheni babban abune” daidai lokacin Anty Jams tabude kofan tace “Hajiya angama abinci kufito muci” anatse Hajiya tace “to bari Meena takiramini Ummi Jamila ganinan zuwa” tashi Meena tayi tawuce sama itama Hajiya tafito falon tasami waje ta zauna.
Dakin Ummi tashiga Meena tabi dakin da kallo yanda suka barajı dazu haka yake dasauri tace “Ummi” shirun yayi yawa hakan yasa tawuce wajen bayi tabude bayin but Ummi bata ciki dasauri tafito tashiga bude dakunan yaran ganin Aman adakinshi yasa tace “Aman have you seen Ummi”? Cikeda rashin jin dadi yace “no Aunt I can’t find Anty Ummi anywhere” dasauri dasauri Meena tafito tasauka kasa Hajiya data bita da kallo ganinta ita kadai tace “ina Ummi”? Dasauri tace “ina zuwa Hajiya” saita wuce kitchen tabude kofa taje backyard batanan dasauri tawuce wajen gateman dinsu tace “Yallabai dazu damuka fita Ummi ta dawo”? Dasauri yace “bata dawo ba babu wanda yazo gidan banda ku dakika dawo yanzu” Dasauri Meena tabude bolt na wayanta zuwa history nan taga Jabi akakai Ummi that means she changed the trip dudda haka takasa gasgatawa, part of zuciyanta nacemata Kodai bolt direban ya saceta ne nan da nan takira Number bolt driver yana dauka tamai explaining tace “ina sister na data biyoka”? Dasauri yace “Madam she was crying seriously in the car and asked me to take her to jabi garage Adamawa line” dasauri Meena hannunta da jikinta har rawa suke taciro number Ummi takira but wayanta akashe da gudu takoma cikin gidan Hajiya data kasa zaune takasa tsaye dan hakanan zuciyanta ke gayamata ba lafiya ganin Meena yasa tace “ina Ummi?” Sai kawai tafashe ma Hajiya da kuka tace “Hajiya wlh duk laifina ne” yanda gaban Hajiya ke faduwa batasan sanda tama Meena tsawa ba. “What happened what did you do Meena?” Kallon yan uwan Hadiza dake falon Meena tayi saikuma tace “Hajiya muje daki nagayamiki” ran Hajiya abace batajin zama ta iya moving kafafunta ba tace “tell me anan Meena, idan kin boye musu bazaki boyema Allah ba” Dan lumshe idanu Meena tayi tace “Hajiya naga how sad Ummi was akunshe adaki shine dazu da kuka kirani nakawo shayi naje na sameta tazo muje asibiti taki tace ba’ace tajeba shine nace kene kikace nazo da ita shine tabini………” tabama Hajiya daga farkon labarin har karshe zuwa wajen bolt Hajiya kawai ta daurama Meena mari! Saida kowa yazabura Maman Hadiza tace “assha, assha Hajiya dan Allah kiyakuri” Rabi da Hafsat zuciyanshi kaman an watsa ruwan sanyi sabida dadi, ran Hajiya yanaci bana wasaba kallon Anty Jamila tayi cikin kakkausan murya tace “tashi kitafi asibiti yanzu yanzun nan Jamila, kekuma kiramin Nura da wayanki” tama Meena dake share fuska magana azafaffe Maman Hadiza tace “Hajiya calm down bakida lafiya fushi haka baida kyau agareki” cikin tsananin fushi tace “I don’t care! Koda zan fadi na mutu awajen nan I don’t care! Kiramin shi nace!” Hajiya tafadi ranta abace kowa yaja bakinshi yayi gum babu wanda baisan labarin Hajiya ba batada kyau tai fushi Anty Jams ta tashi sun sun taje ta dauki key motan Hadiza tafice, ringing daya biyu Nura yadaga strictly Hajiya tace “kome kakeyi Nura a asibitin nan kabarshi kazo gida yanzun nan ga Jamila naturo asibiti tazo ta zauna da Hadiza” zaiyi magana Hajiya ta katse wayan takalli Meena tace “bacemin daga gani, kuma ku tashi ku kwashi abincin nan ku wuce kuje chan sama kuci” Hajiya tama su Hafsat tsawa duk suka tashi Falon yarage daga Mama sai Hajiya tazo gefen Hajiya tariketa cikin kwantar da murya tace “Nura bai kyauta ba dudda kuwa Hadiza diyata ce amman kiyakuri baya hayyacinshi kinsan ba kowa ne ya iya handling pressure ba, dan Allah kiyakuri Hajiya fushi nan baida kyau agareki” lumshe idanu Hajiya tayi sai kawai ta zauna Mama tazauna kusada ita tadauki ruwa ta bata Hajiya ta karba tasha.
Chapter 57 · 0% Book details