← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 97

Sashe 19

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tass yayi lafiyayyan breakfast sannan yazo wajen kofan yace “kawo kayanki mutafi” bude kofa tayi rike da ghanamasgo dinta akunyace kallon Ghanamasgon yayi sai kawai yajuya yace “ina zuwa” sama yakoma yadauko babban suitcase nashi yakawo har gaban dakinta ya duka yabude ya karbi Ghanamasgon baiji kunya ko kyama ba da kanshi yabude yashiga jera mata komi a suitcase din, yarinyar nada tsafta dudda kayanta sun mutu but komi awanke alinke ga dan black leather dayakai hannunshi zai taba dasauri Ummi ta duka tarigashi dauka hakan yasa ya kalleta sai kawai yayi murmushi dan yasan menene turawa tayi akasan akwatin nan da nan yagama hadawa suka kulle yaja akwatin waje Ummi na biye dashi har mota gaba yau yabude mata yana kallonta shiga tayi ahankali ta zauna yakallulle yadawo gaba shima yatada mota har Gwarimpa bakaramin addu’a Hajiya tamusu ba sannan Meena da Baffan shi da ita suka tafi airport ga mamamkin Ummi abokanshi tagani a airport already suna jiransu da Musa da engineer sunci manyan kaya sai kallo Ummi suke munafukai saijin dadi suke, jirgi suke shiga kalan tsoron da Ummi taji a ko tadauka mutuwa zatayi haka sukakai Yola motoci taga suna jiransu guda daya daya security personnel sauran nasu nan aka dauki hanyar kauyensu though sun tsaya a hanya anyi sayyaya na ban mamaki kayan abinci shopping da sauransu.
Tunda Ummi taga sun dauki hanyar kauyensu gabanta ke faduwa hannunta suka fara rawa komi nadawo mata sabi fill
Hannunta Meena tarike tace “ga dukanmu, ga mopol yan sandan chan babu abinda wani katon dan daban kauye ya isa yamiki” tafiyan awa daya da rabi yakaisu kauyensu, kauye ne da yamayi developing ga government work akwai government school, burtsatsai, primary health care da sauransu sai kallon ko’ina take komi ya chanza ta dade rabonta da garin har gidansu wanda yake babban gida ginin kasa irin na da din nan.
Wata tsohuwa sosai haka na zaune a tsakar gida tana mulmula hura taji ihuuu hayaniya a waje tace “Allah yasa ba shaidanin yaron nan ne yazo dawani bala’in ba yau” da gudu wata yarinyar mai kama da Ummi yar karama da bazata wuce 13yrs ba tashigo tana hakki. “Gwaggo Gwaggooo Ummi, Umm…..” kafi takarasa magana Ummi tashigo gidan tareda Meena, mikewa tsaye Gwaggo tayi saikuma tasa zani ta murje idanunta tasake kallon Ummi data tsaya tana kallon Gwaggo, Gwaggo tace “Kodai mutuwa ce tazomini yasa nike ganin kaman Ummi achan tsaye dawata balarabiya” dawani kalan gudu Ummi tazo tafada jikin Gwaggo sai kuka ga kanwar Ummi ta biyun itama tashigo sai kawai dukansu sukahau kuka dagota Gwaggo tayi tace “Ummi kene binni ya karba haka kin ganki kuwa ya akayi kikazo? Banace kada kizo ba duk sati sai Mudi yazo gid…..” fuska Ummi ta share tace “Gwaggo akwai baki maza awaje dauko tabarma Aisha ki shimfida wajenki zukazo” dasauri Gwaggo tace “bakin yan uwan baturiya nan ne, yaki yarinya gaki fara kaman madara” murmushi Meeena tayi tazo ta gaida Gwaggo, Gwaggo ta aika Aisha ashigo dasu nan da nan aka shigo dasu wai bakin Gwaggo yaki rufuwa taga manyan dattijawa ansha shadda fura tashiga hada musu kowanne a kwarya mai kyau su Aisha harda Ummi dama Meena natayasu har Baffa saida yasha huran sun dade basu sami aslin ingantaccen fura irin wannan ba sukai salla.
Daukan nasu huran sukayi su Ummi duk suka tafi daki saida aka gama Baffa ya gabatar da zancen daya kawosu wai Gwaggo kasa boye farin cikinta tayi nan ta sanar dasu komi game da Ummi da aurenta ada tace zancen aurenta kuma maigari ne mai bada yaran aure Dan haka atafi wajenshi nan akanshigo da komi aka shiga mota aka tafi wajen mai gari shima yayi naaam babu wani wahala Dan Auren bazawara ba wahala and tanada right Ummi tafito da mijinta yanzu tunda nabiyu ne kuma itane takawoshi har kauyensubnan da nan su Musa suka ijiyema abokinsu sadaki dubu dari uku aka daura aure tsakanin Nura da Zainabu Ummi akan sadaki 300k mutane dayawa sun shaida aka kawo su goro cingam menene menene aka rarraba wai Nura sai murmushi yake he just can’t believe it duk suna wajen Aisha tazo da gudu tace “Gwaggo ga Mudi chan yazo amman yan sandan nan sunmai duka” tashi Nura yayi da sauransu Maugari yace “dan Allah kukai yaron nan gidan yaro ya addabi mutanen Hm kauyen nan” komawa sukayi akai arresting Mudi nan fa Gwaggo tayi throwing small party itadai Ummi taja makale adaki taki fitowa Meena ko tafito sai video take yanda matan kauye ke rawa Musa yakawo bakinshi saitin kunnen Nura yace “kai mutumina bura’uban chan haka kauye keda tsala tsalan mata bazanyi wuff dawata ba kuwa anan kai jibidai kirjin wanchan dake rawa” tureshi Nura yayi yace “dan iska” dariya Musa yayi yana kallon yammatan, Musa yataba engineer yace “kaga yara amman Allah yamusu kindirmo a kirji” Nura yayi kaman baijishi ba aranshi yace “na Matata Ummi tamafi kowa nan kindirmo” yadan lashe lips yana kallon agogo, Aisha ne tazo tace “Gwaggo tace kazo” binta yayi zuwa falon Gwaggo tana zaune ga Ummi agefe kanta akasa zama yayi ahankali Gwaggo tace “Nura na yaba da hankalinka ne saisa nabaka Auren jikata dan mutumin kwarai ne zaisa diyarka a mota da yan uwanshi azo har kauyenku a nemi aurenta dan haka nabaka ita amana kagansu nan su hudu ne dukansu marayun Allah ne ba uwa ba uba kaji tsoron Allah bamu da kowa a binni dazance je gidan Ummi dobamin ita, tana hannunka ka kulamin da ita na yarda da tarbiyan dana bama yaran nan sunada kunya natsuwa amana da girmama na gaba dasu Ummi bazata taba cutarda kai ba Ummi matace karike ta amana sai kuma inaso nadan roki alfarma ka barta tadanyi ko sati guda ne anan wajena a danyi mata gyaran amare” abu Nura yaji ya tsayamai awuya Gwaggo tace “kayarda”? Ahankali yace “ba matsala” Gwaggo tace “yauwa tunda an kama shegen yaron nan banda sauran tashin hankali na gode Nura bari nafita nabaku guri kuyi sallama” Gwaggo ta tashi tafice.

Juyoda kanshi yayi yakalli Ummi da kanta ke kasa tana jikin bango kaman ruwa ya hadiyeta mikewa tsaye yayi yana duba agogon dake daure da writs nashi sannan yakalleta yace “tashi ki rakani Amarya zan tafi” akunyace Ummi tadaura duka hannayenta kan fuskanta tarasa inda zatasaka kanta sabida kunya, he loves yanda takemai yarinta yarintar nan kunya kunyan nan, gently ya duka agabanta dab da ita yana kallon dogayen yatsunta masu fararen kumba dake kan fuskanta daya rufe yayi shiru, kamshin da Ummi taji na shiga hancinta yasa tadan ware two of her right fingers kaman munafuka tadan bude idanunta dan so take taga ina yake dan yanda takejin kamshin turaren nan nashi karaf suka hada ido ya leko fuskanta ta spice na yatsun ahaukace ta yunkura zata tashi karaf yariketa hannunshi daya yakai ta waist nata yarikota dasauri taboye kanta akirjinshi sosai takejin kunyanshi, yanda yaji fuskanta akirjinshi yasa ahankali yasaki hannunta yakai dayan hannunshi daman bayanta yaturata tashiga kirjinshi gabaki daya sannan yacire hannunshi daga waist nata yasa dukansu abayanta ya rungumeta da kyau tareda sauke ijiyan zuciya ataushashe yace “Assalamu Alaykum Matata Zainab” wani irin sanyin kunya Ummi taji tanaji takasa yarda jikin Alhaji take arungume haka, wlh kirjinshi bala’in taushi ga fadi kaman wani katifa, tun tanajin kunya taki sakin jiki hartai lamo tadaina motsi tanaji yanda kirjinshi ke beating ahankali, wayanshi ne yahau ringing batare daya saketa ba yazare hannunshi daya yaciro wayan yakai kunne Ummi bataji akace ba, amman da muryanshi dataji harya chanza launi yace “bari nagama sallama da iyalina nafito” yana maganan yacire wayan daga kunnenshi yamaida aljihu kafin ahankali yakai hannunshi daya yadago kanta daga kirjinshi maida kanta tayi da sauri, murmushi yayi cikin whispering yace “ina sonki Ummi, amman banji amsan soyayyata aranki ba aka daura mana aure kina sona”? Noke kanta tayi akafadanshi kaman yanama yarinya magana yace “kunyana kikeji?” Gyadamai kai tayi, ahankali yace “nazama mijinki yanzu babu ragowan kunya, yaushe zaki bani amsa?” Kanta yasake dagowa for the second time wannan karan batai musu ba ahankali ya manna mata peck agoshi batare daya cire bakinshi akan goshinta ba yace “zanbar miki Meena da some mopol anan ranan itiyau zan dawo na dauke, banda yawo, idan kinason wani abu ki kirani ki sanar dani kinji”? Gyadamai kai tayi ahankali yasa hannunshi a aljihu yakamo soft hannunta yasa bandir na 500 aciki yace “ki ijiye kudin nan tare dake kome kikeso kiyi dashi kinji”? Gyadamai kai tayi, har lokacin bakinshi nakan goshinta lips dinta ya kalla tanada a bit chubby soft bottom lips sai na saman is slightly thin a bit pinkish a bit dark he seriously wanna kiss her like right now but then yanason tazama comfortable dashi dan ijiyan zuciya yasauke kadan kafin ahankali yasaketa yace “zan tafi” dan komawa baya kadan tayi kaman kada tafita daga jikinshi tana sussunnar dakai tace “Allah maidaku gida lpy nagode da abubuwan daka kawoma su Gwaggo Allah kara budi mai albarka” Ameen yafadi yayi wajen kofa dan juyowa yayi yakalleta kaman yadauketa yakeji yadai daure yadaga labule yafita daga dakin.
Chapter 19 · 0% Book details