Sashe 34
Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nan da nan Ummi tagama abincin Hajiya tahada breakfast tasoya chips ta sossoya eggs da sausage ta hadama su Amal abinci a lunch bag tadauko tafito zata ijiye a dinning tahada ido da Hadiza dake tsaye a dinning din tana sanye da riga da wani palazzo trouser mai shegen kyau na material pink tayi folding hannunta a kirji tana kallon Ummi da jajayen idanunta dasuka kumbura sukai jazur kaman mai ciwon ido abinku da faran fata, chak Ummi ta tsaya anan gaban kitchen din takasa karasowa dinning din ayanda zuciya ke diban Hadiza jitake kaman tazo ta shake Ummi tamutu gabaki daya, daga kafanta tayi tafara tafiya ahankali akuma zuciye tace “how dare you Ummi kika aure mini miji? Ni Hadiza kika aurama miji? Kin manta lokacin dana taimaka miki kina neman aiki ido rufe wayanda kikema aiki ada sunyi japa sun koma Canada anata gantali dake a Abuja ana nema miki gidan aiki baki samuba, na taimaki rayuwanki nabaki aiki nakuma biyaki da kyau, yan aiki da ake biya duba ashirin, dubu shabiya but ni nace zani dinga biyan ki dubu hamsin sabida duka gidana zaki kula dashi da yarana sabida bani zama ina fita aiki, sakkayan dazaki mini kenan ki aure mini miji, mijina Ummi? Nura na?” Ihu Hadiza tayi tana tafiya tace “ki daga fuska ki kalli kwayar idanuna bakar munafuka, algunguma, makira bakar mayya, butulu, shedaniya watsassiya, sai bayan kin aureshi zakizo ki kasa kallona kina sunnar da kanki kasa kaman baiwar Allah, dagakai ki kalleni Ummi, nace ki kalleni!” Hadiza tai maganan tana ihu daidai tana kaiwa gaban Ummi ta finciko gaban riganta gamgam tawani kalan jijjiga Ummi ta mugun makureta tana kallon fuskanta tace “wulakantacciyan yarinyar irinki harta isa ta aure mini miji, ni Ummi kina yar aiki na, sabida ina fita na barmiki gida kikai using opportunity nan kika auri miji na eh”? Hadiza tai maganan tana buga Ummi abango saida Ummi tasaki lunchbag din kasa tai kara Hadiza ta makure mata wuya tace “wlh, wlh, yau saidai afutar da gawanki ki daga gidan nan, ke! Dakikiyar yarinyar irinki tayi kadan tace inyi kishi da ita, bazan taba iya raba Nuri dakowa ba balle ke jinjiran yar iska kinajina? I will kill duk wacce tace zata auri Nuri na, dagani sai shi har lahira” “Hadiza!” Nura daya sauko tareda yaran suna surutu ya hangosu da gudu gudu ya sauko daga bene yazo wajen da sauri ya bambare hannun Hadiza daga wuyan Ummi yace “are u mad kasheta zakiyi”? Tari Ummi tahauyi sosai tana nishi idanunta sunyi ja, cikeda fada Hadiza tasake yowa kan Ummi tace “Nuri ba ruwanka awannan fadan is between me and this this munafukar makiran yarinyar” dasauri Nura yatura Ummi bayanshi daidai su Aman suna zuwa wajen da gudu zasuyi wajen Ummi suna “Anty Ummi sorry” rikesu Hadiza tayi dasauri tana tafarfasa tace “ku zonan ina zaku?” Dasauri Aman yace “wurin Anty Ummi, u hurt her Mom” cikin ihu Hadiza kaman zata make Aman tace “waye Ummi? Me kuka hada da ita? Who is that girl to you? Dagayau baku ba ita Aman kaida sister ka, Ummi is a bad evil person, babu wanda yataba cutata arayuwan nan kaman ita, bantaba nadaman abu arayuwana kaman nai nadaman ranan dana dauketa aiki ba, kar wanda yasake kiran sunanta cikinku agidan nan, Ummi is the worst evi…….” “Hadiza!” Nura yasake kiranta ranshi abace dasauri Hadiza takalli Nura tace “what!? Nura I said what kake kirana? Don’t tell me ka yarda cewa yar aikin nan son yarana take? Okay bakaso nagayama yarana she’s evil, Lemme tell you something today Yarinyar nan bata taba son yarana ba, she just use them tayi winning heart naka da nawa damuka yarda ta zauna gidanmu, bata taba son yarana ba, she use them taja ra’ayinka kasota, tunda ta kyallara ido taga muna biyanta 50k instead of 20-15k da ake biyanta a inda tabasa aiki ta kudurci aniyan saita aureka, saita zama matarka, saisa taja yaran jikinta sabida tasan you love yarannan morethan ur life sune the way to your heart, your weakest point Nura, open your eyes and see Ummi played you and me, Nuri Mezakayi da this village evil girl yar aiki fa eh Allah kadai yasan mazan mutane nawa taci, I will post her pictures on social media to makesure babu wanda yakara daukanta aiki a abujan nan tunda she’s a witch, ka barni naci bura’uban yarinyar nan Nuri tasan cewa Allah dayane” Hadiza takaima Ummi nushi Nuri yatare hannu ta hanyar rike hannunta gam cikin kakkausan murya yace “karkiyi kuskuren tabamin mata Hadiza stop all this thing!” Nura yayi ihu saikuma cikin turenci yace “I’ve given this respect leave this girl alone before I disrespect you in front of her” tafi Hadiza tayi tace “akwai disrespect daya wuce na kariga ka aurota ka kwanta da yar aikina taga kalan buranka dani uwar dakinta keci akwai Eh Nura talk!” Hadiza tai ihuu dayasa Nura ya runtse idanu yabude su ahankali yakalli Aman da Amal daduk ke kallon Maman nasu sunyi tsuru tsuru, dan juyowa kadan Nura yayi yakalli Ummi dake labe abayanshi yace “tafi dakinki” gyadamai kai tayi tawuce Hadiza zatayi kanta Nura yariketa gam, Hadiza tabita da kallo tana duramata ashar tace “munafuka, jibeta kaman bushashen kifin dayay kwantar a kasuwa oporoko, banda ma namiji kanshi kaman kan jarirai ne mezakayi da yarinyar nan mai kama da fiffiken kunkurun dayay shekara dari da uku aduniya eh, makira zuciyanta yafi fatar jikinta baki, tanaji da lebe kaman wacce ke aiki agidan giy……” “Hadiza!” Nura yayi maganan yana fizgota su Aman suka fashe da kuka Nura yakalli yaran saikuma yasaketa yace “look at yaranki ko breakfast basuyi ba zasuje school kina haukan nan bakisan zaiyi affecting mental health da cognitive development nasu ba” cikin fushi tace “eh bazasuyi breakfast dinba ka gayama yarinyar chan bata ba yarana, kada ta kara dafa musu abinci kota musu wani abu, wlh ko hannunta nagani akan jikin yarana kome namata ita taja and kada ka ta kara shigan mini kitchen” Nura yana wani kallonta yace “kitchen banaki bane, duk wani abu naki na kitchen din nabaki dama ki kwashe ki ciresu daga kitchen din zan sayo wasu nasa cus Ummi will enter this kitchen and cook for me” Nura yakallesu yace “zo kuyi breakfast” rike hannun yaran tayi tace “Nura bari kaji yesterday you took advantage of my fragile state kayi yanda kaga dama dani not anymore, billahillazi Nura zan nuna maka cewa yimini kishiya was the worst mistake daka tabayi arayuwan ka, bakana fadin bakada kwanciyan hankali ba yanzu kafara ganin asalin rashin kwanciyan hankali, muzuba nidakai I will deal with you and deal with that thing daka kawomin gidan nan as matan ka, bakasan ba’a wasa da fire ba because u will get burn, Nura I will treat you f*ck up wallahi kuwa” sosai Nura ke kallon Hadiza but sabida yaran saiyayi shiru yatako har gabanta yaduka yakama Aman da Amal dake kuka looking terrified ya karbe su daga hannunta yace “bani yarana” yajuya zaiyi dinning dasu kafin yaje Hadiza tarigashi zuwa dinning din duka abincin da Ummi takai dinning dan breakfast Hadiza ta kabar, dasauri Nura yaja Aman baya dan yadauki Amal gudun karya kone da ruwan zafi yana kallon Hadiza, ahaukace ta duka ta kwashi lunchbox na yaran da Ummi ta watsar akasa dataji shaka dazu ta bude tana ciro komi tana zZzagewa akasa tace “baza’a aci abincin yar aikin ba, yarana bazasu karacin abincinta ba, nace baza’a ciba, angama cin abinci again, Nura that peace dakace bakasamu dani ba ajikin yar aikina zaka samu wlh, wlh, wlh bazaka sameshi ba, Nura u will never know peace now dakamin kishiya I swear by Allah” sosai Nura ke kallon Hadiza kaman ba itane tagama kuka jiya kaman wacce ke shirin mutuwa ba, baice mata komiba yajuya yakoma falo yazauna yaciro wayanshi yakira school din yaran yace abasu breakfsat da lunch yau daidai motan school din zuwa, lallashin yaran yayi yadauko juice a fridge yabasu sannan yafita yasasu a school bus sannan yadawo cikin gida Hadiza na tsaye a tsakar falon tarike waist nata tan kallon Nuran.