← Book details Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 97

Sashe 81

Matan Ko Mazan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

33
Duk tafiya akayi yarage daga ita sai Mama afalon dake kallon yanda take kuka, kaman taje ta lallasheta but itama at this point she support Babanta 100 percent, yayi maganin Hadiza, ya gyarata, kuma she trust Baba Hadiza zata ladabtu, kuma zata bada nata gudunmawan ma agayarata, tashi tayi tawuce corridor dakin dake kusada nata tabude daganan tace “taho ki shiga dakinki kiyi wanka ki chanza kayan jikinki kiyi salla” ahankali Hadiza ta tashi ta taho sai kallon fuskan Mama take data hade giran sama da kasa so kawai take Mama ta lallasheta but Mama nosend hatta shige dakin dake da yar katifa yar daidai akasa dawata yar fanka asama babu AC babu POP normal silin ne asama, sai akwatinan kayan ta kakap wanda Nura ya aiko dasu duk suna dakin nan aka ijiye, shiga ciki tayi Mama tasaki labulen ta wuce taje ya debo mata abinci da ruwa da kanta tazo ta kawo dakin, ganinta azaune yasa ta daka mata tsawa. “My friend stand up kije kiyi wanka nace!” Kallon Mama Hadiza tayi saitaga kaman ba Mama dake nan nan da itaba, jiki asake ta tashi taje bayi tai wanka Mama na tsaye akanta ta shirya tai salla tasa taci abincin dole taci kusan rabin tuwon sanan tawuce tafita da plate din tadawo daki ta kwanta tayi shiru tana kallon fankan dake kadawa asama yana kara dake damun brain dinta sai kawai taji hawaye yafito daga idanunta saita tashi ta zauna ta zubama akwatinan ta ido tana kallonsu sai kawai taji hawaye yakara fito mata a fuzar da iska komi da Zeenah tamata na dawo mata fresh yanzu da gaske Nuri is done with her tunda har yana dawo da komi nata gida wani kuka yazo mata tayishi ta gode Allah tai bacci.
3 dot taji ana kiran sunanta. “Khadija Khadijah” Adan firgice tabude idanunta jin muryan Baba yana tsaye gaban dakin batare daya shigo cikiba yace “Khadija” dasauri tace “na’am Baba” strictly yace “dauro alwala kifito falo ina jiranki” ahankali tace “tom” tashi tayi tana tangadin bacci tashiga bandaki ta dauro alwala ta dauko hijabi tafito falo Baba kadai tagani ya tsareta da idanu dasauri tasauke kanta kasa dadduma biyu ya shimfida afalon daya agaba daya abaya yace “hau dadduma muyi qiyamun laili” Gyadama Baba kai tayi yatada salla yafara karanto Al qur’ani kira’an Baba dadi sai kawai Hadiza taji abun ya tsuma mata zuciya, yaune rana na farko dataji aranta lallai fa tabar Allah for a long time cus bazata iya tuna the last time ta karanta Al Qur’ani ba wlh, sai kawai taji hawaye ya gangaro mata feeling fragile, Baba bai wani ja sallan da tsayi ba sabida ita, 5 raka’a sukayi yajuyo ya kalleta anatse ya daga hannu yace “idan bawa na cikin kunci, damuwa da fitinun jarabawa, bawa dan uwansa bazai iya magance masa matsalolinsa ba Khadija, ni ko mahaifiyar ki bazamu iya magance miki duk abinda ke damunki ba Allah kadaine zai magance miki kome kikeji, shine Ubangiji mai tsarki da daukaka, mai kuma mulki, Al Awwalu, Al Akhiru Al Zahiru Al Badin kuma, duk daren duniya Allah kan sauko dakansa ya amsa bukatun bayinsa, dan haka daga hannunki sama ki gayama Allah bukatun ki kakap, sannan ki rokeshi gafara bisa laifuffukan dakikamai, ki rokeshi haske da dacewa akan rayuwa babu abinda yafi karfin Allah, so kaima Allah kukan ki Khadija” Gyadamai Baba kai Hadiza tayi kuka na zuwanmata ta hannunta sama ahankali abin namata kaman ba itaba she can’t remember the last time datai salla haka ta roki Allah for anything, she’s feeling guilty kan tayi neglecting bautama Allah, sai kawai tafashe da kuka tace “Allah na tuba! Allah na tuba!” Sai kuka hakan yasa ahankali Baba ya juya yayi facing gabanshi, Hadiza tai kuka zuciyanta ya sosu she’s feeling kaman ma she don’t deserve rahaman Allah cus tamai laifi da dama, da kyar ta iya controlling kukan tafara addu’a azuciyanta, the first abu daya fito daga zuciyanta is Nura tanson aurenta da Nura tanason ya maidata, tanason mijinta, kawai saita shiga share hawaye, sosai tai addu’a saitaji wani imani da natsuwa na shiganta da tadade bataji ba, anan bacci yayi gaba da ita ta kwanta kan dadduman Baba tajuyo yakalleta yayi shiru idan yace bai damu da damuwa ta ba yayi karya, saisa ya kudirci anniyan zai gyarata yana kuma rokon Allah ya taimakamai yabashi iko dan idan Allah bai nufeta da shirya ba kome zaiyi abanza bazata shiryu ba, addu’oi yacigaba dayı har aka kira asuba sannan yatadata yace “taje tayo alwala tai sallan asuba” shikuma yawuce mosque.

Hadiza tadauka Baba wasa yake yana dawowa daga sallan asuba wanda bai dadeba dan normally sai gari yawaye yake dawowa gida but yau ana idar da salla yayi azkar yafito yadawo gida yakirata fitowa tayi ga mamaki ta ganin Baba tayi da bagadadi da gaske saikace yarinya shima Baba yasan duk tsiya ai ta iya alifun, ba’un, Al Qur’ani suka farayi from fathiha yana karantawa tana repeating after him, suna gamawa sukai alifun har karshe zuwa alifun bil fatha yana koya mata baki dalla dalla, daganan sukai tauhidi Man Rabbuka, Hadiza jitayi zatai kuka abu ya tsayamata awuya ganin yanda Baba ke koyarda ita abubuwan da yasan ta iya, ko su Aman dinta a islamiyyan su sun wuce abubuwan nan amman ya maidata yarinya, lekowa Mama tayi tagansu tadauke kai abinta takoma daki tana samin natsuwa ganin Baba yarike wuta.
7:30 suka gama Baba yace “tashi kije ki daura abincin kari kiyi gyaran gida, tambayo Mamanki me za’a dafa” gyadama Baba kai tayi tawuce ciki ahankali tace “Mama ina kwana” batare da Mama ta kalleta ba tace “lafiya lau” murya chan kasa tace “me za’a dafa Mama?” Dan kallonta Mama tayi tace “ki surfa wake rabin tiya, saiki debi kadan ayi kosai, ki dama kamu asha dashi, ragowan kiyi alalen rana na gwangwani, injin nikanmu na backyard banason alalen nikan blender, buhun gawayi na kitchen ki hura wuta” ahankali Hadiza na kallon Mama kirjinta na bugawa tace “ba gas Mama”? Wani kallo Mama tamata tace “akwai amman jiya Baban ki yasayo gawayi buhu daya yace dashi za’a dinga girki yanzu” hawaye Hadiza taji sunciko idanunta tarikesu dasauri tace “Mama ban iya hura gawayi ba, shima wake ban iya surfaw……” dakuwan da Mama tamata yasa takasa karasa maganan, Mama da haushinta ke cikinta fall sabida yanda takaso auren gidan arziki yaro mai kudi tadawo mata gida tawani zabura tace “wlh kikkipa miki mari zanyi Hadiza kinci kaniyanki, are you stupid dazaki cemin baki iya surfen wake ko iya hura gwayi ba kin dauka nan Abuja ne? Dan mai garinku kafin kiyi aure ba da itace kuke girki agidan nan ba lokacin akwai gas ne? Sau nawa kika dafa alale agidan nan ki surfa waken kiyi komi? Hadiza kalleni nan wake up! Ki gaggauta tashi daga baccin dakike ubanki ba kowa bane haka ma ni uwarki, Babanki Malamin makaranta ne nikuma housewife ahaka muka raineku kuka taso, auren Nura shine ya jiyardake dadin rayuwa kikadan menene rayuwa adukiya, yanzu kuma kin kaso auren gidan ubanki kike look at everywhere” Mama ta nuna dakin da yatsu tace “bude idanunki da kyau ki kalla nan ba gidan Nura bane gidan mahaifinki ne Hadiza, ki gane banbancin so my dear bace min daga nan kije ki daura abincin safe” tashi Hadiza tayi ahankali tawuce tafito idanunta har zafi zafi suke mata tsabagen rashin jin dadin rayuwanta, tsakar gidan tafito zuwa kitchen dinsu ta tasaya tana kallon komi ga buhun gawayi ga murhun gawayin, ga tukwane, yanzu itane zatai aiki a kitchen din nan? Tasan tayi aiki aciki da but ta manta? She’s not use to old life nata again, ijiyan zuciya tasauke tasa hannunta tadauki kaskon wutan ta ijiye waje daya, tabude buhun gawayin, tadaga fararen soft hannunta dakeshan manicure ta kalla, kuka tafashe da shi ahankali tace “na shiga uku na lalace” goge fuskanta tayi da sauri kafin ahankali tasa hannun cikin buhun ta debo gawayin ta zuba a murhun, ledojin datagani da kyallen dinki na hada kasko tadeba ta zuba tana mamakin yanda take tuna yanda ake hura wutan yanzu, bataga kalanzir ba saitadau ashana ta kunna akai makamashin suka kama hakan yasa tafito tawuce flat nasu ta auno wake 8 cup tafito tadeba ruwa ta jika tadauki turmi ta bude tadauki tabarya ta kwashe wajen ta zuba tafara daka ahankali kirjinta namata badadi ko kadan.
Chapter 81 · 0% Book details