← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 26

Sashe 9

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tuni aka gama cinikin gidan akan naira million daya da rabi da yake gidan yana da dan damar shi two bedrum da toilet da kitchen da kuma public toilet ga harabar gidan,Nan take tabada takardun gidan da ta dauko a karkashin katifar mijinta, an basu notices na kwana uku kacal!"Su tashi su bar gidan kuma ba fargaba ta aminche da hakan!"Nan wurin ta cire million daya da dari biyu asaya mata mota ta hannu mai kyau sosai Matrix!"Hajiya lailah da tayi mata tsaye akan komai har ya daidaitah ta shaida mata mota zata zo hannu acikin makon nan!"Dadi da farin ciki kamar ya kashe saleema, Wacce ta aikata komai kamar yadda ranta ke so,"Sallama sukayi da lailah ta wuce tare da abokan tafiyarta dallalan gida da mota."Saleema ko faty ta kira ta sanarda da ita komai, duk da fattyn bataji dadin abinda saleemar ta aikatawa mijinta Aleeyu,A ranta ba!"Amma ba yanda zatayi azahiri munna ta tayata!"Nan take tambayarta Alhajin ko yadawo take sanar mata gobe ne zasu iso kebbi dan suna Abuja yanzu!"Cikin zumudi saleema ke sanarda ita goben zata shigo da yardar Allah."

"Fatyma ta ce"Sai kin zo Allah ya kai mu!"Sukayi sallama kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa!!!" ………

***** ******

*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
👇🏻

Iya kaduwa Humaira ta kadu dajin lafazin Khamal nacewar wai tazaba ko rabuwa dashi ko rabuwa da cikin dake jikinta su zauna.

Tabbas wannan magana bame yiyuwa bace agurinta sbd khamal shine rayuwarta haka ma rayuwar "yayanta ma tana da amfani agareta domin tana ganin acan gaba zasu jikanta zakuma suyi mata amfani tunda danginta sun gujeta sune zasu zame mata dangin uwa da uba

Khamal yasake daga mata murya "Humaira kizaba ko zama dani ko rabuwa dani wanne yafi miki?

Yatsatstsareta da manyan idanunsa masu rikita mata lissafi

Tace asanyaye "Zama da kai masoyina.

Ya gyada kai yace "to inhar kuwa zaki zauna dani to saikin yarda anzubda cikin nan najikinki dan walh ban shiryi tara yara awannan zamanin ba haka kawai da yarintata inkoma tsohon karfi da yaji.naga alamar ma inxan biye mk humaira ashekara zaki ringa haihuwa to walh ba dani ba maza kishige yanzun nan muje azubda cikin inhar da gaske kina sona.

Hawaye ne masu zafi suka zubo mata tahau yi masa magiya "dan Allah Abban twins kayimin rai walh ina son cikin...

Yakatseta "ohhh!!kina son cikin nine bakya so ko?nine bakya son farin cikina? To "! To naji kina son cikin nabarki dashi kizauna dashi ni zanyi nisa daku zangani wanne ne zaiyi mk amfani cikin koni da bakya so... "walh ina sonka kayi hkr kayimin rai kada kabarni

Takama kafar wandonsa ya angajeta ta bugu da kujera take bakinta yafashe sai jini

Nan yabarta yafice abinsa yana cika yana batsewa kamar bakin kumurci inka ganshi saika zaci ko fada yasha da dan,uwansa namiji

Har dare takai tana kuka ta tasa twins agaba ko abinci yinin ranar bataci ba

Ta tashi ckn dare tayo alwala tayi sallarta tana kuka take gayawa ubangijinta halin data shiga da addu.a akan Allah yakawo mata dauki

Da safe data tashi idanunta sun kumbura don kuka

Da jiri ta tashi ta lalubi wayarta takirashi amma 10 miss call bai dagaba

Asibiti taso xuwa amma ba damar ta futa bata sanar masaba tanada tsoro da kiyayae doka

Haka ranar ta wuni bata sashi a idoba tun daren jiya daya futa

Takira zee ta gaya mata komai

Zee ta shaka sosai taringa mata bala..i
"to ai kece humaira tun farko kin bari namiji yarainaki walh danice saina zaba inga tsiyar da za.ai shi asuwa zaki zauna yana wulakantaki da kyanki da ajikinki da iliminki to walh bari kiji kada kisake fadamin halin takaicin nan naku kedashi don baxaki ringa sakani abacin rankiba in zaki kwatowa kanki "yanci tun wuri kikwato ato.

Zee tana datse wayar taji wani zazzafan hawaye ya taho mata yanzu ita yazatayi kenan tana son mijinta bazata iya canza masa hali ba tun asali da sanyin rai take bi dashi bazata iya juyewa mafadaciya ba khamal yafita fada da masifa tun asali zuciyarta ta mutu akansa

Sukansu twins aranar rikitata sukai da koke koke tarasa yadda zatayi dasu gashi bata iyacin abincin kirki shiyasa suka rasa ruwan nono sosai aranar

Ckn kankanin lokaci tafuta hayyacinta duk ta rame

Ai wasa farin girki domin sati guda tayi bata sakashi a idoba

Har alokacin kuma batayi nadama ko ta ayyana tsanar cikin jikin nataba saima kaunar cikin data karaji aranta

Allah yasota tana da kayan abinci akicin sai karancin kudin cefane ahannunta

Haka taringa manage na komai gas ne ma daya kare mata tahau amfani da kero

Shima ckn kwana uku yakare ta rasa yadda zatayi

Allah yajefo mata Ashanty taganta hankalinta yatashi tana fadin "humaira meya sameki duk kika rame?

Kinyi rashin lfy ne baki gaya manaba?

Take zuxiyar humaira ta karaya tahau kuka tana gayawa Ashanty komai

Ran ashanty ya baci tace "tun farko ke kk da laifi kawata saida nace kibi abinda mijinki ya shimfida mk kikaki Zee tana zugaki nikuma kinganni da ban taba Aureba nahango mk abinda zai iya kawo mk matsala arayuwa kinga dai khamal shine uwa da uba agunki to yanzu kuma ga abinda ya faru agareki kina ganin rayuwarki zata tafi ke kadai?

Humaira tahau girgiza kai tana fadin "a.a Ashanty walh bazan iya rayuwa babu khamal ba dan Allah kitaimaka min kisan yadda zakiyi kinemominshi kibashi hkr plz kawata.

Ashanty ta tausaya mata tasan yadda humairan ke matuqar kaunar mijinta wanda ada sunsha batawa da ita ma akan khamal din don dai sun sahqune yasa bata tabayin fushi da ita takuma san zafin soyayya shiyasa take mata uzuri tunda itanma ahalin yanzun zuciyarta takamu da son abokin khamal din Ahmad Amma data shawo kan lamarin ta hanyar kaishi gidan malami sai gashi ansamo matashi ahannu sai yanda tayi dashi

Ashanta tace "kiyi shiru zantaimaka miki kuma zamu shawo kansa yabar mk cikin saidai ki kiyaye agaba.

Tasa wayarta tayi dailing nambar Ahmad bugu daya yadaga suka gaisa ta zayyane masa komai

Ahmad yayi mamaki domin kokusa khamal bai gaya masaba kuma suna haduwa sosai

Take suna gama waya kuwa yakira khamal din yace masa yazo maza yanzun yana so su hadu zasui magana me muhimmanci

Koda suka hadu Ahmad baiyi masa maganarba yadaukeshi Amotarsa sai gidan Khamal din

Kamal yasha mamakin Ahmad bai ce uffan ba domin sai alokacin yayi tunanin ko humaira takai karar sane

Da sukai farking sai yaki futowa

Ahmad yakalleshi yace "meye dalilinka nayin hakan?meyasa kake gasa "yar mutane khamal?

Khamal yahau sosa keya yace "ita tagaya maka ina mata wani abun?

"Ba ita tagayaminba yanda ka boyemin to kawarta tasan komai tagayamin yanzu hakama tana ciki kuma kabani mamaki dahar akan abu kalilan zaisa kayi mata hukunci irin hakan wato hotel kaje ka kama kaida yar iskar nan ko?shiyasa kake boyemin don kar nayi maka fada yayi kyau.

Ahmad nagama fadin hakan yafito yashiga ckn gidan khamal din

Jiki asanyaye khaml din shima yafito yamara masa baya

Abokai ne kud da kud tun yarinta yanda suke komai atare to haka halayyarsu take iri daya tabin mata saidai kuma aqudarsu ta bambanta donshi Ahmad yana son yahaihu ma Allah baikawo masa ba shekararsa 5 da aure amma matarsa jiddah ko bari bata tabayiba

Ya taba auran wata yar nijar ma shekararsu uku suka rabu dataga bata haihuba don itanma tanada son haihuwa dama baxarawace

Shi ahalin yanzun neman haihuwar yk ido rufe shiyasa ayau yaga laifin khaml sosai yaringa masa fada da suka shiga ckn gidan

A sitting room suke dukansu

Humaira ranta yai fari dataga mijinta duk ta rame saitaga shima yarame tayita kallonsa shikuma yanata cika yana basarwa ko kallonta baiyiba haushinta ma yaringaji nayanda tayi masa terere da sirrinsa

Ahmad yahadasu yashirya su kuma saida yaga Khamal yahakura da batun zubda cikin kana sukai musu sallama suka tafi shida sahibar tasa Ashanty

Saida aka kwana biyu sannan yasake mata yakawo kayan abinci yacika store fam da komai yayi refelling na gas

Khamal yanada rufin asiri amma Ahmad yafishi kudi dan Ahmad har gidan mai gareshi

Matar Ahmad mafadaciya ce sosai amma dayake shidin me kudine baya shakkarta ko kusa kuma bin matansa yake ahakan don yanda yake son haihuwa yace ko shege ne yasamu atiti to xai rikeshi ahannunsa baxaiji kunyar kowaba

To ahakadai ba laifi humaira tadan samu kwanciyar hankali tunda mijinta yasamu har yana kwanciyar aure da ita sukanyi hirar soyayya andawo gidan jiya don tana bashi hakkinsa yanda yasaba karba sbd ta lakanceshi shidin mabuqacine shiyasa baya hkr da ita kadai

Alokacin da cikinta ya isa haihuwa tuni ta yaye twins

Allah yasauketa lfy ta zankado jaririya me kama da ita futuk yarinya kyakykyawa sak humaira

Amal aka rada mata kuma wani ikon Allah sai yarinya tazo da farin jini

Abin mamaki khamal baya nuna kaunar yaran nasa kamar wanda aka shiga tsakaninsu abin yana ciwa humaira tuwo akwarya

Har kasa hkr kwata.yi tafurta masa suna kwance tace masa "Abban twins wai meyasa baka nuna tsagwaron kaunarka ga yaranka ne?

Ransa yabaci da jin lafazinta "me kike nufi dani wato tsanarsu nayi kenan. To bari kiji inma haka kk nufi to hakan ta kusa faruwa inhar bazaki daina haihuwa ba domin nikam ukun nan sun isa ma sbd Su mata ne rayuwarsu kalilance da ace ma maza ne shine zasu gajeni zan iya saka ran nasami wakilai agaba to matane bai zama lallai nazauna dasuba gidan wani zasuje kuma mata kuna da son kai natabbata acan gaba ke zasu ringa yiwa komai abar uba ace ciwon ya mace na "ya mace ne ace mace itake jinkan mace shi namiji sai namiji...humaira ta kyalkyale da dariya tace "haba Abban twins kadaina fadin hakan aisu *MATA JIGON AL,UMMA* Ne babu banbanci bana kuma fatan yaranmu su banbantamu zanbasu tarbiyyar da zasu taso da jinkan iyayansu kada ka damu duk zancen mutane ne wannan.

Yayi shiru kawai

Taci gaba dayi masa tausa

Yace mata "to naji Amma yanzu inaso muje dake acire miki mahaifar kanta

Da sauri tazabura tace "nashiga uku Abban twins abin har yakai hakka lallai na yarda baka son haihuwa
Chapter 9 · 0% Book details