Sashe 6
Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malan Bukar yace mece ce shawarar taki? Zama tayi tana fad'in kaida Allah yayi ma kyautar *JIGON AL'UMMA*, taya zaka tsaya kana tunanin hanyar samun kud'i? Kawai tunda ga Hamrah ka bashi ita amaimakon kudinshi, kaga kaci riba biyu, na farko kaci kud'i abanza, na biyu ba ruwanka da sayen kayan d'aki, tunda shine zai aureta kaga dole yayi mata komai.
Murmushi Malan Bukar yayi yana fad'in Allah yayi maki albarka Kubra, hakik'a ke mace ce ta gari, tabbas na yarda da akace *MATA JIGON AL'UMMA* ne, cikin sauki gashi kin kawo mani hanyar mafita, hakik'a mata kuna taimakon mazajen ku, basu kad'ai ba, gaba d'aya duniyar ma, gaskiya duk gidan da babu mace kango ne, ai mace ko jaririya ce kada ka rainata, domin wata rana zatayi maka amfani.
Murmushin jin dad'i Kubra tayi tana jin dad'in yanda Malan Bukar yake kod'ata. Tashi yayi yana fad'in bari naje na samo tantak'washi dole yau muyi farfesu saboda kin faranta mani. Kubra tace dakata, bana so kayi wannan maganar yanzu sai zuwa nan gaba, kaga kafin bikin Hibbah idan ya amince sai ahad'a ayi tare. Malan Bukar yace angama Uwar gida ran gida.
****
Bayan kwana biyu da rabuwar Hamrah da Muftahu wata rana taje kasuwa a hanyarta ta dawowa ta had'u da *Bilal*, duk yanda taki tsayawa sai da ya tsaidata, da k'yar ya roketa ta amince tashiga ya sauketa gida.
Bayan sun gama gaisawa bai tsaya b'ata lokaci ba ya fad'a mata abinda yake ranshi, sosai Bilal ya burgeta, nan ita ma ta amince dashi, haka sukayi sallama cike da farin ciki ta shige gida tana mai godiya ga Allah daya kawo mata canji... Tana shiga zaure taci karo da Hibbah wadda ta lab'e tana masu lek'e.
Cike da borin kunya ta wuce ciki... Tana zuwa ta fad'ama Kubra, murmushi Kubra tayi tace kada ki damu kanki, Hamrah ai bazata tab'a auren jin dad'i ba, idan baki sani ba sa'an Ubanta nakeso ta aura, kuma ki zuba ido kiyi kallo, dan haka kada sabon saurayinta ya b'ata maki rai. Tsallen murna Hibbah tayi ta rungume Kubra.
Tun daga wannan rana Hamrah da Bilal suke soyayya, sosai take sonshi haka shima, su Kubra da Hibbah kuwa kallonta kawai suke suna dariya domin sun san bazata tab'a samun Bilal ba. Ta gefe guda kuma Hibbah da Muftahu suna soyewa, dan tuni ya manta wata Hamrah.
Sai gashi an wayi gari Mahaifinta ya furta mata nufinshi akanta, duk da bai fad'ama Alhaji Garba Yaro ba, yayi haka ne dan yafi so ya fara samun had'in kan Hamrah kafin ya tunkari Alhaji Yaro da maganar, domin yasan hakinshi, matuk'ar ya gano yarinyar bata amince ba yana iya kwafsa masa, hakan yasa ya fara tuntub'ar Hamrah kuma ya gwada mata umarni ne ba shawara ba.
Wannan shine asalin labarin Malan Bukar da Iyalinshi......
*Alk'alamin*🖋
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
(Nabeelert Lady)
[7/5, 5:35 AM] Nabila Lady: 👩👩👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩👩👧*
👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚
*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*
*Page* 0⃣4⃣
*Alk'alamin*🖋
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
( *Nabeelert Lady*)
*Cigaban labari*
Bayan da Hamrah ta gama kukanta tashi tayi tayo wanka ta shirya dan bata jin zaman gidan gara ta fita ko zata ji saukin zafin da zuciyarta takeyi.
Fitowa tayi ta shiga d'akin Umman su... Da sallama tashiga, ciki-ciki suka amsa mata, duk'awa tayi tana fad'in Umma zanje gidan su Halima ne. Tab'e baki Kubra tayi tana fad'in idan ma ba can zakije ba ni badamuwa ta bace, kinsan dai an bada ke, idan kikaje wajen wani mutuncin Ubanki zaki zubar domin shi za'a kira mai baki biyu, dan haka ni ba ruwana sai kin dawo.
Tashi Hamrah tayi jiki asanyaye tayi waje. Dariya Hibbah tasa tana fad'in waya sani ko mahad'a sukayi da Bilal. Kubra tace koma makwanta sukayi ni ba ruwana, idan taje ya d'irka mata ciki ita tajiyo.
***
Zaune Hamrah take a d'akin k'awarta Halima banda kuka babu abinda takeyi. Kallonta Halima tayi cike da tausayi tace dan Allah Hamrah kiyi hak'uri, komai yayi tsanani maganinsa Allah.
'Dago kai Hamrah tayi tana fad'in haba Halima, ya kike so nayi, wai ace mahaifina ne zai badani sadaka, ni wallahi da ace ba saboda biyan bashi zai badani ba zan iya hak'uri na anshi K'addarata da hannu biyu, amma saboda cin mutunci wai biyan bashi zaiyi dani, kuma ba kowa ya bada shawarar hakan ba sai Umma, babban abun haushin kud'in da sukaci bashin na bikin Hibbah ne haba Halima.
Hannun Hamrah Halima ta kamo tana fad'in kiyi hak'uri Hamrah, insha Allah zakiga sakayya akan wannan abun, ba dai sunyi haka bane dan su bak'anta maki ba? Ina nan dake sai Allah yayi maganin su, domin Allah baya barin Hak'k'in wani akan wani.
Hamrah tace kina gani fa yanda suka rabani da Muftahu, yanzu ko ganina yayi ko kallo ban ishe shi ba, na hak'ura na samu wani amma saboda son zuciya gashi za'a bayar dani amatsayin biyan bashi.
Halima tace ki k'addara Muftahu ba rabonki bane, haka zalika Bilal ma, ina tabbatar maki duk abinda Allah ya rubuta ma bawa wallahi baya tsallakeshi, mune 'yan adam da bamu gane ba, idan Allah yasa abu zai faru da kai dole ya faru da kai, idan kikayi hak'uri sai kiga ya kawo maki mafita.
Jinjina kai Hamrah tayi tana fad'in shikenan nagode da shawararki Halima, kuma bayaninki yasa zuciyata tayi sanyi, har ina tunanin guduwa sai gashi kin bani shawara mai kyau, hakik'a kayi tarayya da mutumin kirki yafi komai dad'i, Allah yabar zumunci.
Halima tace amin, kuma naji dad'i da bakiyi saurin yanke hukunci ba har kikazo kika fad'a mani, ai babu amfani ace ki gudu kibar gidan ku, duk inda zakije bazakiyi mutunci ba, insha Allahu sai kin zama *JIGON AL'UMMA*. Hamrah tace Allah yasa.
***
Zaune Kubra take agidan makociyarsu wadda ta kasance babbar aminiyarta, sunanta Lami... Labarin yanda komai ya kasance Kubra ta fad'ama Lami. Dariya Lami tayi tana cigaba da yima wata mata da tazo kitso, kallon Kubra tayi tana fad'in kinyi dai-dai k'awata, ai wallahi duk macen da tace zatayi kishi damu tana cikin matsala.
Kubra tace ai Zuwaira tayi kuskuren auren mijina, bayan aurenshi ma har sai da ta haifa masa d'iya, duk da bata duniya d'iyarta zata fansar mata hukuncina.
'Dago kai wadda akema kitso tayi tana fad'in baiwar Allah kiyi hak'uri zanyi shishshigi akan abinda ba'a sako ni ba, tunda kikazo naji duk abinda kika fad'a, amma kisani *MATA JIGON AL'UMMA* ne, bai kamata ace kin kasance cikin mugayen mata ba, mai zakiyi a duniya? Kada ki manta inda abokiyar zamanki taje kema wata rana dole kije.
Idan kika tafi kinsan wacce zaki barma d'iyarki? Ko kinsan can inda zatayi auren kinsan da wa zata zauna? Haba baiwar Allah, meye ribarki idan kika aurama d'iyar kishiyarki sa'an ubanta? Baki tunanin akwai Hak'k'i? Ko kin manta Allah yana bima bayinsa Hak'k'in su? Dan Allah kiyi hak'uri kada ki cutar da marainiyar Allah.
Saurin tashi Kubra tayi tana kunfar baki.......
**** *****
👇🏽
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
Gaban humairane yafadi jin tambayar dayai mata
To amma Data tuno
Da binnin layukan datayi na rufin baki da mallam yabata saita maze ta kakaro murmushi tayi luf ajikinsa ckn rage murya tace dashi "walh Dear nima bansan cikin yashigaba sai kwanan nan kafin kadawo dana fara laulayi shine nagane ma akwai cikin.
Yace mata "to meyesa ba.a gayamin ba saida natambaya?
Tace "tsoro nakeji kada kace azubar nikuma inajin tsoron zubda ciki kaga babu kyau kuma kada Allah yajarrabceni inmutu awajen zubarwar.
"Akan me zance azubar? Shegene cikin?kokuma ni jahili ne?
Ta girgiza kanta cikin jin dadi da karsashi data samu tace "ba daya kayi hkr nayi laifi.
Ya girgiza kai yace "bakiyi laifi ba nadai gane cewar matsa mikin danayi shine yasa har kika fara boyemin sirrinki toki saka aranki najanye ra.ayina na k'inyin cikinki fatana dai Gaba akiyaye yazamo munyi dogon planning yanzu dai na hkr amma dazarar kin haihu sai munyi five years za.a sake wata haihuwar are you ok?
Ta daga kai sama tana murmushi
Aranar ta nuna masa tsagwaron so ta shayar dashi zumar soyayya tabbas me ciki tana dauke da Ni,imarta ta musamman dg indallah wanda sai alokacin khamal ya fahimci hakan.
Awashe gari Humaira takira su Zee awaya take sheda musu yanda sukai da khamal
Zee wani ihun dadi tasaka ckn murna tace "ke mutuniyata zuwa gurin mallam yayi kyau kinga munyi maganin sa da tuni yanzu yayi mk wulaqanci dan haka yanzun aiki ya rage naki tunda yana son cikin saikiyi taki kissar ki tatsi abinda zaki tatsa kafin ki haihu tun daga zuwa awo scaining da sauran matsaltsalu kiringa yawaita fada masa domin yashaqa miki kudade tunda inbai bakiba ma qadangarun batiki zaikaiwa dan haka kada ki sake kiraga masa kawata.
Humaira tace "haka za.ai aminiyat nagode da kyakykyawar shawara.
********
Cikin watannin daya ragewa humaira ta haihu ta tatsi khamal kudade sunyi dubu dari da hamsin domin duk abinda tace tana bukata indai akan cikinne da rawar jiki yake badawa
Sosai suka shiryi yin partyn suna inta haihu don har anko suka fito dashi na swice lase na dubu 20k
Kawaye sun yiyyi su zee amarori sune suke rabon ankon wanda amotar zee din suke full tank na mai afita rabon anko amma sai weekEnd sbd zee ma.aikaciya ce
Allah yasauki Humaira lfy ta haifo twins duk mata kyawawa dasu farare yara sunyi farin jini domin akullum gidan cike yake da "yan barka
Dangin khamal sun zozzo daga garinsu sun sauka a sashin baki wanda babu kowa
Koda ganin dangin khamal saida zuciyar humaira ta motsa domin ji tayi inama nata dangin suma suzo
Ko da wasa ma bata fadawa kowa adangin nataba sbd tasan babu wanda zaizo mata ma don kafataninsu babu me zuwa inda take itama da take zuwa gurin iyayanta ba kasafai ba danma ta nace da zuwane batayin fushi duk zuwa da bakin ciki take dawowa sbd korar kare suke mata haba ai dole ita datakaisu kotu sbd namiji.
Anyi taron suna a hotel din criss cross dake Nass.lodge road
Anci ansha ankashe kudi anyi watsi da nera police band ne ya baje hajarsa agun.