← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi sai kin fadi da bakin ki domin kinada masaniya akai, ko yanzu ki daku!"qara mannata yayi a bangon daki!"Tuni jikinta ya raina fata sai bari take baki ya mutu ta tsorata banda hawaye ba abinda takeyi!"Da kyaar ta numfasa Ta ce,"Dan Allah kai hakuri wallahi sharrin shaidan da giyar talauci sun mantar da ni bansanar da kai ba na sayarda gidan nan tun kwanakin baya......!"

"What....!Yanzu saleema da gaske Ashe kin sayarda gidana batare da sanina ba!?"Domin kawai ki tona min asiri!?Bayan Allah ya rufa min asiri!?Me na maki da bakison ganin farin cikina saleema!?Da me na rageki!?Duk wani abu da zaki buqata wanne bana maki duk dan na kare mutuncina da naki!?Wane hakki naki ne bana saukewa!? sai wanda baki buqata! Da ra'ayi!"Amma a hakan kika sayarda gidana bada izinina ba me zaki da kudi!"Me kuma kikayi da su!"Kinsan nawa na sayi gidan nan da zaki sayarda shi akan lalataccen farashi!?"Kin kyautah kuma nagode da irin sakayyar da zAkiyi min!....Kin nuna baki sona saboda kin tsani jin dadina,bakisan mutuncina da darajata ba bare hakkokin auren mu duk kin shure,Zaman cutarwa bayada amfani!"Koma me kikayi da kudin ko zakiyi kije Allah ya baki nasara!"Amman Dole na rabu da ke, ba Dan naso hakan ba,sai dai shi ne salama, atsakanin mu!Saleema gudun watarana karki sayarda ni batare da sanina ba!"Son kudi komai yana sawa!"Hakan rashin so yana sa komai!"Dan haka kije na yanke dukkan igiyoyin aurena da ke kisamu wani mai arziki da kike so ki aura ni kuma Allah yabani mace tagari mai sona da zuciya daya domin Allah wacce zata bani kulawa da yarana tare da tarbiyya mai kyau!... Aleeyu yace yana zubda hawayen bakin ciki..!"

"Raaaas gabanta ya fadi duk da abinda take nema kenan amma kuma jikinta yai sanyi wata nadama ta lullubeta nan take ta rushe da kuka...!"Aleeyu ko saketa yayi tafadi qasa tana kuka!"

''Ya ce Kukan me zakiyi kuma abinda kike buqata ne kinka samu Dan da ganinki yau din nan da gyaran da kika sha nasan cewa ba domin ni kikaayi ba!"Kina da wani dalili da manufa azuciyarki Dan rabon da na ganki hakan har na manta!"Saboda haka kije ki cigaba da abinda rayuwarki ke so kuma tazaba maki!"Amma Dan Allah saleema ki ji tsoron Allah ki kare mutuncin yaranki ko basu raye, ke uwa ce agaresu kuma har abada za aci gaba da alaqanta ni da ke da kuma yaranmu,Iya sani na Ban cutarda ke ba saleema azaman mu,Idan ko na cuceki Allah ya saka maki!"A karshe ina maki fatan alheri kuma kiyi kokarin kwashe kayanki Dan wadanda kinka sayarwa da gidan nan zasu zo duba gidan su,kuma dawowa zasuyi dazun nan suka shaida min hakan!"Nagode Allah ya sadamu da Alheri!!!!"

"Yana karashe zancen sa ya fice daga dakinta,Dakinsa ya nufa ya kwashe duk wani abin bukatarsa anan yake ganin katuwar paper da saleema tayi ta koyon sign... Dinsa har tayi sa'a,da irin nasa ta zana atakardun gidan!"Ta sayar!"Murmushi yayi Wanda yafi kuka zafi!"Ya hade kayansa ya saka a motar sa yabar gidan!"Direct sabon gidansa ya nufa ruwa ya watsa a.c ya kunna ko zaiji sarari a ransa amma ya kasa nutsuwa a karshe al'wala yayi yafara jera nafila tare da karatun alqurni da hakan yasamu sauki aransa!"

"Kuka takeyi sosai Wanda batasan dalilin sa ba!"Tashin mota tajiyo daga waje!"Raaas gabanta ya fadi,ba ko mayafi ta fito harabar gidan ba kowa!"Dakinsa ta nufa duk wani abin amfaninsa ya dauke!"Kofar gidan ta nufa tana zubda hawaye!Tabbas abinda take zargi!Ya tabbata motar da tagani gefen gidansu anyi parking mai kyau,Kenan Aleeyu yazo da ita!?To motar waye?Koh ta Abdoul Hafeez ce!?Kai ko koma wankau aka kawo masa yake danawa!?Kar dai hafeez ya wuce sudan Aleeyu ya barma motar!?Kai bazata sabou ruwa ba sa'an kwandou ba ne,Wannan motar tafi karfin Aleeyu wane shi!.....Duk batada amsoshin tambayoyinta....!"Komawa tayi daga ciki hijab ta saka fitowa tayi direct unguwar lowcost ta nufa tana kuka mai Napep sai hakuri yake bata domin ya dauka ko mutuwa akayi mata!"Kofar wani katafaren agida aka ajiye taah."Sauka tayi tana share hawayenta duk ta wani jujuce kamar wacce sabuwar hauka ta kama."Gidan ta shiga kai tsaye!."

Toupha ko gidan waye oho🤔Shin saleema kukan me takeyi?Sai naga abin nema ne yasamu!?Hmnnnn yan magana kance dahuwar mutim mai kosar da shi......muje zuwa mata jigon Al'umma...✍🏻

******* ******

*Alk'almin*🖋
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
*Nabeelert Lady*
👇🏻

Kuka kawai Hamrah takeyi bayan tashiga d'aki, ayau taji kewar mahaifiyarta sosai, tabbas rashin Uwa babban ciwo ne, Uwa itace jigon rayuwa, duk wanda ya rasa Uwa dole yayi kuka domin yayi babban rashi, da ace mahaifiyarta tana nan bazata shiga irin wannan damuwar ba, duk da alokacin da take raye ma Mahaifinsu yana nuna banbanci agidan amma ganinta da takeyi yana d'auke mata duk wata damuwa, ko ba komai zasu shiga d'aki suyi fira, amma gashi yau tana cikin damuwa babu wanda zai lallasheta, wanda take sa ran zata aura ya zamar mata jigo arayuwa gashi bazata aureshi ba, zata auri tsoho ak'ara jefa rayuwarta cikin matsala.

Hannu ta d'aga sama tana fad'in ya Allah kaine ka k'addaro mani wannan al'amari, ya Allah ka kawo mani mafita mafi alkhairi agareni, ya Allah ka saka mani juriya araina, kuma ka bani ikon yima mahaifina biyayya aduk wani abu da zai gindaya mani, ya Allah ka saka mani akan zalincin da Umma take mani acikin gidan nan, ya Allah ka tabbatar mani da alkhairin da yake cikin wannan auren kuma ka bani ikon zama lafiya a duk inda za'a kai ni. Kifa kai tayi tana kuka mai tsuma rai.

Umma ce ta fito daga kitchen d'auke da farantin abinci tana fad'in dani kike magana, banda kilibibi zakice wai zakije wajen dangin Uwarki, haka kawai kije a kullo wani munafurcin wanda zai hana a d'aura aurenki, ai wallahi matuk'ar ina numfashi babu ke babu samun abinda kike so, duk da Alhaji yana da kud'i nasan bazaki tab'a jin dad'in zaman aure agidanshi ba, domin babu wadda zata so ace ta auri tsoho.

Matsowa Hibbah tayi tana murmushi tace kai Umma keda wa kike ta masifa haka? Umma tace nida waccan munafukar, wai taje wajen Malan take fad'a masa zataje kauyen Uwarta. Hibbah tace amma dai Umma baki barshi ya amince ba ko? Umma tace kema kinsani ai.

Dariya Hibbah tayi tana fad'in shiyasa naga ta fito tana kuka ashe? Umma tace tayi kukan jini ma, bara na kai masa abinci na dawo akwai in da zan aike ki zaki amso kayan gyaran jikinki wajen Lami munyi waya tace ta kammala komai. Hibbah tace to Umma sai kin fito.

*** ***

Ruwa Momyn Bilal ta zuba mashi gaba d'aya jikinta rawa yakeyi, Alhaji yana duk'e agabanshi yana jijjigashi. Ajiyar zuciya Bilal ya saki mai k'arfi. Hamdala Alhaji yayi ya rik'oshi yana masa sannu. Bayan sun zauna Momy ta kalli Bilal tana fad'in wai Alhaji lafiya meya sameshi ne? Alhaji yace yanda kika ganshi nima haka kawai naga ya zube, da alamu akwai wani abu da yake damunsa.

Kallon Bilal yayi yana fad'in lafiya me yake damun ka? Duk'ar da kai Bilal yayi yana kok'arin b'oye hawayen da suke kok'arin zubo mashi. Momy tace kayi magana mana Bilal, baka da wad'an da suka fimu da zaka iya b'oye masu wani abu, idan akwai wani abu da yake damunka gara ka fad'a ko muna da abinda zamu taimaka maka dashi, idan babu sai muje asibiti a duba lafiyarka.

Da kyar ya maida hawayen idonshi ya bud'e baki yace bakomai kaina ne kawai yake ciwo. Gyara zama Alhaji yayi yace wannan sumar taka bata da nasaba da ciwon kai, dole akwai wani abu da kake b'oye mana, dan haka ka bud'e baki kayi mana bayani bana son ka b'oye mani komai domin kan ka zaka cuta.

Shiru Bilal yayi yana tunanin taya zai fad'a ma Mahaifinsa wacce zai aura itace yake so, gashi da alama shima yana sonta, domin da bakinsa yake fad'in zai k'ara aure, a fuskarshi kawai ta nuna yana na'am da wannan auren.

Murmushi Alhaji yayi yace shikenan tashi kaje, amma ka sani ni nasan dalilin shigarka wannan halin, domin a maganar da mukayi da kai ta k'arshe naga alamun hakan a fuskar ka, kuma na sani hakan yana da nasaba da maganar auren da zanyi, abinda nakeso ka sani shine, ko mahaifiyarka bata nuna mani komai ba akan wannan auren ba, dan haka banga dalilin ka na shiga damuwa akan aurena ba, idan kana jin kunyar ace mahaifinka zai auri k'aramar yarinya to ka fito da mata kaima kayi aure, kaga tsakanina da kai sai idan kazo gaisheni, tunda kaima zaka tafi gidan ka.

Girgiza kai Bilal yayi hawayen da yake b'oyewa suka samu nasarar zubowa, hannu yasa yana goge idonshi yace Abbah ba abinda kake tunani bane, Allah ya baka ikon yin wannan auren matuk'ar akwai alkhairi aciki, damuwata ba akan Momy bane, kawai bana jin dad'i ne.

Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in to Allah ya yaye maka damuwar da take damunka, kuma naji dad'i da wannan addu'ar taka, amma ka rage saka damuwa aranka, duka nawa kake da damuwa zata rik'a jefaka cikin irin wannan yanayin.

Tashi Bilal yayi yana fad'in zan kiyaye Abbah. Fita yayi yana goge idonshi. Cike da tausayi Momy ta bishi da kallo, tabbas tasan akwai abinda yake damunshi, amma zata bincikeshi domin ta gano koma menene, duk da itama tana cikin damuwar maganar auren Alhaji amma ganin Bilal cikin damuwa yasa taji tata da sauki.

Kallonta Alhaji yayi yana fad'in zuba mani ruwa nasha naga kin tafi dogon tunani, kada ki damu a hankali zai sanar damu abinda yake damunsa, kuma nima zan bincika na gano abinda yake damunsa domin ba yau na fara ganinshi cikin damuwa ba. Momy tace Allah dai yasa ba wata babbar matsala bace. Alhaji yace amin.

*** ***

Zaune Muftahu yake shida wani abokinsa Mansur suna tsara yanda bikinshi zai kasance. Kallon Muftahu Mansur yayi yana fad'in wai abokina ka fad'a ma Hibbah kana da mata har biyu kuwa? Murmushi Muftahu yayi yana fad'in so kake ta fasa aurena kenan, duk d'aukarsu nid'in babban mai kud'i ne ai, shiyasa nima na bisu ayanda suka d'auka.
Chapter 17 · 0% Book details