← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin da tayi ita din kalar masu kudice yasa akoyaushe take yab'awa Aliyu bakar magana akan hakan duk dan ta bak'anta masa rai bata kojin nauyinsa ko kunya yanzu kaji tace dashi "kai hkr fa nakeyi da zama dakai danni ba tsarar auranka bace kadubi gidannan ka dubeka mana nayi kalar daya daga ciki?

Duk randa tafada masa hakan yakanyi murmushi kawai baya magana saboda yasan nufinta akansa shiyasa baya tankawa ko sau daya.

Tanada kawaye guda biyu wanda suke hure mata kunne

Hajiya Laila da hjy fatima hamshakan masu kudine duk da sun girme mata ba ruwanta don tana karuwa dasu tun mijinta nada arxikinsa suke tare amma ayanzu har dasu ma ake hada baki acusgunawa Aliyu

Saleema tana son taga ta buda ta bada kala tayi fafa kamar yadda sauran kawayenta sukeyi ayanzu hakan kawayen nata duk sunada motoci ta sanadiyyar miji sukayita kowacce mijintane yasai mata

Akullum mafita take nema na yanda zata ga ta mallaki mota amma abu yaci tura babu wata hanya datasan zatabi ta bille mata

Abu daya ne yafado mata arai shine tasa gidan nan akasuwa kawai batare da sanin Aliyuba tasaida inyaso sai tasayi motar ko sakwan hand ce sauran kudin saita kama musu haya

Tabbas ta gamsu da wannan shawara ta zuciyarta tahau murmushi nacin nasara don tasan babu abinda zai iyayi akai inyaji daga baya tunda ta shanye kayanta.....

*ALK'ALAMIN NABILA DIKKO🖋*

****** ****

Kuka kawai takeyi yayin da ta cigaba da sauraron maganar da mahaifinta yake mata cikin fad'a..... Kina jina ko *HAMRAH,* wallahi bazaki sa naji kunya a duniya ba, tunda Allah ya bani 'ya'ya mata ai ya gama mani komai, domin kud'in *JIGON AL'UMMA NE,* amfanin ku shine mutum ya biya buk'ata idan lokacin yin hakan ya taso, dan haka nariga dana yanke hukunci dole ki auri *ALHAJI MANSUR* matuk'ar kina amatsayin d'iyata.

Kina tunanin ina da ku agabana zan je neman wasu mak'udan kud'in da zan biya bashi ne? Sanin kanki ne wad'an nan kud'in dana ciyo bashi domin amfanin yayarki ne, dasu nayi mata komai na kayan d'aki, yanzu Alhaji yana buk'atar kud'inshi kuma ni bani da hanyar samun su, tunda har ya amince na bashi ke a maimakon kud'i kina tunanin bazan bashi ba? Dan haka idan zaki daina wannan kukan ki daina, aure babu fashi, kada na sake ganinki da kowa ak'ofar gidana kinji na fad'a maki, tashi ki bani waje.

Tashi Hamrah tayi jiki asanyaye ta nufi d'akinta wanda yake daga gefen tsakar gida, tafiya take amma juwa ce take d'aukarta, da k'yar ta isa cikin d'aki.

Dariya suka kwashe da ita daga cikin d'akin su jin abinda Baban Hamrah ya fad'a mata..... Gyara zama matar da take zaune ad'aki tayi tana fad'in ai wallahi kad'an ma kika gani Hamrah, aure ne dole ayishi, *HIBBAH* tace kad'ai zata auri sardidin saurayi zab'in ranta, amma ke kam sai dai ki auri tsoho.

Hibbah tace ai Umma naso ace sabon saurayinta kika bani ba tsohon ba dan naga shima yana da kyau kuma akwai kud'in. Murmushi Umma tayi tace haba Hibbah, nafiki sanin inda zakije ki huta, ai tunda kikace mani *MUFTAHU* saurayin Hamrah kikeso nayi maki alk'awarin samunshi, gashi kuma kinga cikin lokaci kad'an ya barta ya dawo wajenki har ana maganar aure.

Hibbah tace bansan ya akayi Hamrah ta fini yawan samari ba, kinga fa bayan rabuwarta da Muftahu ba'a dad'e ba ta had'u da *BILAL*, ai wallahi naji dad'i da Baba ya bada ta sadaka, kinga bazata auri Bilal ba. Umma tace har abada baza kiyi kuka ba tunda dai baki kasance marainiya kamar ta ba.

Kuka kawai Hamrah take tana tuna kalaman Babanta, wai sune *jigon al'umma?* to koda *MATA* suka kasance *JIGON AL'UMMA* ai ba a yanda ya fad'a ake nufi ba, domin duk gidan da babu mace tamkar dajin da babu haske ne, domin *mata sune fitilar rayuwa*, amma dan ta kasance marainiya agidan shikenan sai ajuyata yanda akeso.

Ta samu mijin aure an rabata dashi anba Hibbah, ta sake samun wani yanzu kuma anyi biyan bashi da ita, bashin ma na Hibbah wanda akaci domin aurenta, to ita dame za'a aurar da ita kenan? Kuma ace wai mahaifinta shine yayi mata haka.

Ya Allah kana gani, yanda zanyi biyayya a wannan auren ya Allah ka canza mani koma menene da alkhairi, ya Allah kasa na zama cikakkar *JIGON AL'UMMAR* amin.

Asalin labarin......

Daga

*ALK'ALAMIN* 🖋

*MARUBUCIYAR ZAMANI*
*NABILA RABI'U ZANGO*
*Nabeelert Lady*
[7/5, 5:34 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Page* 0⃣2⃣

*Malan Abubakar* wanda akafi sani da *BUKAR* d'an asalin garin Funtua ne jihar Katsina, sana'arshi itace *Noma*, yana da Mata biyu, ta farko itace *KUBRA*, d'iyar ta d'aya mai suna *HIBBAH*, matarshi ta biyu itace *ZUWAIRA*, itama d'iyarta d'aya mai suna *HAMRAH*. Suna zaune a unguwar *'DAN AMMANI ROAD*.

Sam Kubra bata da halin kirki, mace ce mai son kanta, 'yar asalin k'aramar hukumar *Giwa* ce wanda take k'ark'ashin Kaduna. Tunda Malan Bukar ya auro Zuwaira ta d'ora mata karan tsana, haka tashiga ta fita sai da ta asirce Malan Bukar, duk abinda zatayi baya ganin laifinta, ta d'auke mashi kai daga kan Zuwaira da Hamrah, shiyasa take abinda ta ga dama.

Alokacin da Hibba da Hamrah suka kammala karatun secondary alokacin Allah ya amshi ran mahaifiyar Hamrah, sakamakon ciwon zuciya wanda bakomai bane ya haddasa mata shi sai rashin adalcin da ake mata ita da d'iyar ta.

Sosai Hamrah tayi kuka domin tayi rashi ba k'arami ba, haka akayi zaman makoki aka gama. Kasancewar dangin Zuwaira ba'a Funtua suke ba 'yar asalin garin *'Dandume* ce yasa suka rok'i Malan Bukar akan ya basu Hamrah su tafi da ita.

Alokacin har ya yarda, yana zuwa ya fad'ama Kubra sai tace ita bata yarda ba, fitowa tayi tana kuka tana fad'in shikenan saboda sun rasa Zuwaira sai su d'auke Hamrah, koba komai itama Uwa take agareta ai, yanda suka shak'u da Hibbah idan aka d'auketa wane hali ake so ta shiga.

Haka dai Kubra tayi ta kuka har sai da tasa wasu kuka. Babban Yayan Zuwaira yace gaskiya idan suka amshi Hamrah basu kyauta ba, da nan da can duk d'aya ne, Allah ya baki ladar rik'onta. Anan sukayi masu sallama suka tafi. Hamrah kuwa wani irin kuka takeyi amma babu wanda ya fahimci dalilin kukanta, ad'aukarsu rashin mahaifiyarta ne.

Bayan mutuwar Zuwaira da wata d'aya Kubra tasa Hamrah ta kwashe kayanta daga d'akin Zuwaira tace ta koma wani d'aki da yake anan tsakar gida Hibbah zata koma d'akin Zuwairar.

Aranar Hamrah tasha kuka, haka takwashe kayanta, katifa kad'ai Kubra ta bata tace ta aje sauran kayan tunda wancan d'akin bazai d'auke su ba.

Koda Malan Bukar yaga anyi haka baice komai ba, domin an riga an gama dashi.... Duk wani aiki na gidan Hamrah ce take yinshi, tsakaninta da Hibbah ko kallon arziki batayi mata.

Ana cikin haka wata rana Hamrah taje unguwar *magajin makera* gidan wata k'awarta a hanyarta ta dawowa ta had'u da wani mutum, kafin yazo wajenta harta hau mashin, da sauri yashiga mota yabi bayanta. Har k'ofar gidansu yaje alokacin tana sallamar mai mashin.

Fitowa yayi ya k'araso wajenta yana mai yi mata sallama. Amsawa tayi nan ta gaishe shi. Anan ya bata hak'uri akan ya tsaidata kuma ya biyota ba tare da izini ba. Murmushi Hibbah tayi sai taji dad'in kalamanshi, hakan ya nuna mata mutumin kirki ne.

Anan ya fad'a mata sunanshi *MUFTAHU*, shima nan garin yake yana aikin asibiti Pharmacy ne anan general hospital, yana zaune a GRA yanzu ma yazo wajen wani abokinsa ne.

Nan dai ya gama gabatar da kanshi a wajenta, babu b'ata lokaci Hamrah ta amince dashi.... Ashe duk abinda suke Hibbah tana lab'e tana jinsu, cike da b'acin rai tashige gida. Haka sukayi sallama ya tafi.

Tun daga wannan rana soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Hamrah da Muftahu, yayin da Hibbah da Kubrah suka fara neman yanda zasu rabasu ya dawo kan Hibbah.

Cikin sa'a kuwa sukayi asiri suka raba tsakaninsu inda suka saka soyayyar Hibbah a zuciyar Muftahu.... Haka kawai Hamrah taga Muftahu ya canza mata, idan yazo bata sani, sai data lek'a kawai taganshi shida Hibbah amota, sosai hakan ya bata mamaki, da tayi masa Magana sai yace tayi hak'uri yanzu Hibbah yake so..... Tun daga wannan rana Hamrah ta hak'ura dashi, duk da tasha fama kafin ta yakiceshi aranta.

Babu b'ata lokaci ya turo Iyayenshi, babu bincike haka Malan Bukar yace ya basu Hibbah, nan fa aka kawo kayan sa rana........ Sosai Malan Bukar yashiga damuwar rashin kud'in auren Hibbah.

Kubrah ce ta bashi shawara akan yaje wajen uban gidanshi *ALHAJI GARBA YARO* ya amso bashin kud'i idan yaso ahankali ya biyashi. Babu b'ata lokacin Malan Bukar ya amince da shawarar Kubra, cike da neman nasara ya nufi gidan Alhaji Garba Yaro.......

*Alk'alamin🖋*
*Marubuciyar Zamani*
*Nbila Rabi'u Zango*
( *Nabeelert Lady*)

***** *****

"Kamar kullum yauma Aleeyu fita yayi DOMIN neman na kansa kamar yadda ya saba akowace rana."

"Duk aikin da ya samu matukar na samun kudi ne tunkan dako,faskare,turin baro,Sharar shaguna a kasuwa da sauran su Aleeyu yi yakeyi domin ya samu abinda zai korewa gimbiyar mata Saleema kudaji a baki."

"Bayan Aleeyu ya kammala 'Yan aikace-aikacen da samu ko da yaushe a kasuwa."Wurin wankin motoci ya wuce domin mai nema baya fidda ran zaya samu!"

"Da sallama ya isa wurin da layin motocin suke."

"Wa'alaika salam."

"Mallam sallau barka da yau an tashi lafiya ya iyali.?"Inji Aliyu yayin da suke kokarin yin musabaha da abokin sa sallau mai wankin."

"Alhamdulillah Malam Ali ya naka iyali an fitou ko?"

"Eh
Gamu mun fito kowa da godiya."

"To Masha Allah,Inji sallau cikin fara'ah,Domin shi yana son Ali da rayuwar sa."

"Malam Ali ga motoci uku nan na sama maka daga cikin wanda na samu ni sai na wanke Biyar kafin nagama kaga mun samu wasu sallau ya CE"Tare da nunawa Aliyu motocin masu kyau gaske."

"Da murna Aleeyu ya ce ''Gaskiya nagode sallau Allah yabar Mu tare Amin yace alokacin da yake kokarin goge motar da ya kammala wankewa."
Chapter 2 · 0% Book details