← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 26

Sashe 26

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Amal dayake so acknsu ma yau data kama shi fuzgewa yayi ya turarta don itama yau yaji zarginsa akanta yamotsa

Haka yafuce zuciyarsa akekashe babu tausayin su
Ack

Tana kuka tana hada komatsanta dana yara a akwati da buhunhuna

Data hadasu guri guda saita zauna akusa da kayan tahau kuka ta rumgumo yaran abin tausayi

"Yan sanda su biyune dayan yace "malama ke muke jira ki futa mukulle masa gida yabamu key.

Takasa daga ido takallesuma domin idonta yayi mata nauyi dan tsabagen kukan da tasha

Dayan dan sandan yace "mukama mata kayan mukai mata waje tunda naga tayi nauyi bazata iyaba

Haka suka kama mata kayan suka ringa kai mata bakin get har suka gama sannan suka dawo suka bata umarnin fita

Ta hada kan yaranta suka fito waje tana rungume da baby Nabeelah sai Amal data kama hannunta twins nabiye da ita suna kuka

Tanaji tana gani suka kulle gidan suka tafi Abinsu to anbasu umarni ankuma cikasu da kudi dayake dai suma marasa imanin ne

Wata makwabciyarta tafito taga abinda yafaru tahau tambayarta ko meye dalili?

Bata boye mataba ta zayyane mata komai

Maman khalil ta kama baki tace "nashiga uku ni Aisha bantaba jin irin wannab tijara da masifa ba sai yau keko me kikayiwa ubangijinki har haka take faruwa dake?tabbas inkinsan akwai wani babban zunubi da kika aikatawa Allanki ko iyayanki maza kinemi yafiya domin Allah najarabtar bayinsa da abokan zama naki yayi worst maman twins innice baxan iya daukaba walh,tabdijan wannan wane irin wulakancine haka,matarka ka koreta kasa arufe mata gida,ga yara, gaskiya inxan baki shawara kidauka to bazata wuce na ki mance dashiba ki kama Allah,ki kama yaranki gaba inkinyi hkr zakiga sakamako mekyau don Allah zai jarabceshi agaba kuma dan yaga kina sonsanefa maman twins dan Allah kimance dashi.
humaira tace

"mmn khalil ko da danyaga ina son nasama dai baiwuce tsanar dayaiwa haihuwar da nake yawan yi akai akai ba,kuma baya son haihuwar "yaya mata.na dade da fuskanta yana nunamin karara ina gani tunda baya daukarsu baya nuna musu soyayya.

Mmn khalil tace "ikon Allah.kai wannan khamal dai baiji dadinsa ba meye illa a haihuwar "yaya matan? "Yaya mata ai Rahamane kuma *mata ai jigon Al,umma* ne kisha kuruminki kada kisa damuwa aranki Akwai Allah kedai kimika lamarinki ga ubangiji kawai.

Humaira tashare hawaye ta murmusa tace "nagode sosai da shawararki zanyi amfani da ita.

"to yanzu ina kika nufa ? Iyayanki agarinnan sukene?

Ta gyada kanta tace "E.

mmn khalil tace "to bari naje nayiwa kanin mijina magana baifita aikiba yanada "yar k'urkura saiyazo yakwasar miki kayan yakaiki har gidanku.

gaban humaira saida yafadi data tuno iyayanta amma saita dake tace "to nagode.

tananan tsaye ba dadewa saiga mannir kanin mijin Aishan yazo da "yar kurkurar yadebar mata kayan yaloda amotar yace tashiga

tashiga gaba itada yaranta

yatambayeta sunan unguwar tagaya masa

yaja suka tafi

*******
koda suka shiga cikin unguwar ita taringa nuna masa hanyar dazata kaisu gidan nasu har suka isa kofar gidan gabanta bai dai faduwaba

Zaisauke mata kayan tace yadakata taje tadawo tukunna.

yaranma cikin motar tabarsu baby Nabeela tayi bacci tana jikin hussaina

atsakar gida ta tarar da iyayan nata

Babanta zaifuta ummanta tabiyoshi tana masa adawo lfy.

Sukai turus fara.ar fuskarsu takau kamar wanda sukaga mala,ikan daukar rai

ta dake taje garesu da sauri ta durkusa tana gaidasu babu wanda ya amsa

babanta da alamar yafi daukar zafi da ita yaharzuqo tareda nunata "uban meya kawoki garemu?muna fuka zoki fuce kafin na qonaki kamar yadda na alqawurta ko kinsake zuwane danki tadamin mikin da kikaimin kinmanta nacireki ackn yarana?dakikiya wacce ta fifita saurayi akan iyayae.

Ummanta tayi murmushin bakin ciki tace "a,aha Baban yusufa aidaka barta munji abinda ke tafe da ita.kasani ko anzo gurinne?kasani ko sako ta yayi shine takeso ta dawo...

"gidan uban Wa zata dawo? To walh ko bayan raina ban yarda tadawomin gida ba.banyarda kikarbeta ba.koda khamal dinne ya mutu bazan yarda na rikekiba sbd gaba zaki iyayimin abinda kikai min abaya. Nikuma na dade da yafeki ckn yarana.dan haka kiyi gaggawar barmin gida kifita yanzun nan ko kuma kifuskanci wulakanci.

tafashe da kuka Wayyo Rana zafi inuwa quna.

Duk da dai basu barta tayi maganaba amma ta furta kalma daya jal

*"Dan Allah ko baxaku karbeniba kuyafemin Nayi Nadama.*!

"zoki fita nace!mutuniyar banza. Babanta yace afusace kamar zai daketa

Ta mike daga gabansu da sauri tafuce tana kuka

Tana futa tashige motar da sauri ckn kuka tace da mannir "Dan Allah muje ka kaini Sharada Gidan kawata.

mannir yaja motar sukai gaba wanda aransa yahau tambayar ko iyayanta sunrasune bata saniba?toko matar uba gareta ba uwarta agidan?

baisamu amsar saba har suka akofar gidan Ashanty

saida taga gidan Ashanty Arufe kana ma tatuna ashe tace mata tayi tafiya itada Ahmad to yanzu ina ta nufa Alhalin Zee ma tace taje semener kaduna ina zataje kenan?

takira zee awaya saitace mata taje gidanta ta zauna gobe zata taho da sassafe akwai key dinta agun makwabciyarta zatayi mata waya saita karba ta bude gidan.

tagaya mannir inda zai kaita unguwar yakasai cikin gari ba bata lokaci yajuya da ita zuwa can shitausayi ma take bashi

koda suka isa yakasi ba bata lokaci tana dira akofar gidan tashiga gidan dake jikin gidan zee din takarbi mukullin gidan zee din tabude ta shigar da yaran shikuma mannir yahau shigar mata da kayan

takawo dubu daya tabashi dayake tanada kudin ajakarta amma fafur mannir yaki karba yace shikam dan Allah yayi mata komai

tayi tayi masa godiya don yayi mata komai kam

Tazauna afalon zee tayi tagumi Amal da Baby na jikinta ga dan cikinta sai juyi da motsi yaketa mata akai akai

hassana tace da ita "Mummy Abba zaizo nan?

ta girgiza kanta kawai
hussaina tace "mummy
Meyasa Abbanmu yakoromu daga gidanmu me kika masa yadawo damu karamin gidannan.

"babu komai. Kawai tace tana share hawaye

Amal sarkin wayo itama tace "mummy ni baxan kwana anan gidan ba bana so agidan Abbana zan kwana nidai.

Humaira taji wani daci ackn ranta yarannan suna son Abbansu dayawa Amma shi baya sonsu wannan wace irin rayuwa ce? Allah ka kawo min dauki.

tafada cikin ranta

4 stars sukace "Amin......
Chapter 26 · 0% Book details