← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 26

Sashe 3

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aleeyu cikin shagon nasu na ajiye kayan aikin su ya shiga ya dauko soso,carwash,da towel da sauran su domin fara aikin sa."Sallau ya nuna wa Ali wata sabuwar mota(BUGATTI) ruwan kore mai duhu yace yafara wanketa mai motar yanzu yana tafe Aliyu ya ce to kana ya fara wankewa yana sharar zufan da ke bin jikinsa saboda tsananin rana!"

"SALEEMA ko Aleeyu mijinta na fita ta yafa mayafinta ta bar gidan kaca-kaca ko shara babu bare wanke-wanke."Ta saba mayafi tabar gidan cikin shiga ta alfarma domin zuwa bukin qawar su saudat ubah."Gidan Hajiya lailah ta tafi daga can suka wuce gidan Hajiya Fatyma cikin hadaddiyar motar ta da Saleema taci burin samun irin ta koda kuwa ta hannu ce."

"Dukkan su sun sha ado na nunawa a jaridu sun hadu iya haduwa Hajiya Ftyma da lailah an sha gold sai wAtsi da hannu akeyi ana shan kamshi."Saleema kuwa duk ita ma tayi wanka mai kyaun gaske wanda dai ba za a fita ba."Swiss less ne pink da takalmi da jaka da gyale da sarka fashions ajikinta."Tayi kyau matuka sai dai kaffa-kaffa takeyi kada jama'a su gane ba zinari ajikinta."Sai wani daga kai takeyi da glass manne a fuskarta."Tunda suka shiga babban falon Hajiya saudat ubah kallo ya koma kan su maroka sai kirari sukeyi was Hajiya laila da Fatyma qawayen Saleema suna koda su da mazajen su ko ta kan Saleema basu waiwaya ba!"Wanda hakan yayi matukar bata mata rai sosai!"DOMIN ita ma ashekarun baya ko Saleema ba a kiranta da shi sai dai uwar gidan Engr.Ali gadanga."Da tunanin aka cika su da abinci da abin sha da sauran kayan makwaleshe duk da Saleema naso sai dai tana dan basarwa kada aganota akarshe dai fita tayi da plask din na nama da snacks kitchen din gidan ta shige ta zube a Leda ta boye ajakarta ta fito tana hura hanci!"Ita ala dole babbar mace matar mai kudi."Sai gaisawa takeyi da jama'a tana dariya da fara'ah saboda kawai suga hauren ta na hajj da har yanzu sabo ne hul tana kyalli kamar yau tadawo daga saudiya Hajiya Saleema kenan."Sai dai azuciyarta mafita take nema ayau su samu ita da qawayenta dan babban burinta ta mallaki motar kanta kamar daa babu shakkah sai ta aiwatar da kudurinta na sayar da tsofon fankon gidan na Aleeyu."Jiran takeyi a kare cin bukin su fita domin asamu maslaha da mafita yadda za'ayi."

"Mallam sallau kwance a inuwar da suke hutawa wayar sa tayi kara,Dauka yayi da hanzari ya ce"Assalamu Alaikum."

"D'ayan bangaren amsa masa akayi."Sallau ya ce "Eh ranka shi dade an wanke har ma ta bushe to yallabai sai ka iso Allah shi kiyaye."Ameen Alhajin ya CE"Tare da kashe Kiran."

"Juyawa yayi ya CE"Mallam Aleeyu ga Alhaji Hafeez nan zuwa ya dauki mota."In ji sallau."

"Aleeyu ya ce"To mallam sallau Allah ya kawo shi lafiya,Bari nayo cefane kafin yazo ya sallame ni."Na wuce gida."

"Sallau ya ce"A gaskiya mallam Ali kana da kirki da tunani kuma duk wanda ke zaune tare da kai zai karo da halaye na gari musamman sanin hakkin iyali."A gaskiya nafara koyi da dabi'un ka wadanda ada ban mayarda su komai ba ina alfahari da kai abokina!"

"Murmushi Aleeyu yayi mai dauke da jin dadi!"ya ce ba komai sallau Allah ya barmu tare sai na dawo yanzun nan."

"Yawwa adawo lafiya."

"Bayan minti goma sai ga Alhaji Hafeez yazo yayi farin ciki sosai da ganin aikin wankin motar sa yayi kyau."Sun gaisa sosai kana ya dauko kudi ya ba Sallau naira dubu biyu duk da sunfi na wankin mortar."

"Da godiya ya karba."Juyowar da Alhaji Hafeez zaiyi yayi dai-dai da isowar Aleeyu sukayi sabani kayan cefanen suka zube!"Har manjan da ya auno aleda ya fadi qasa ya fashe da kayan miyan!"

"Subhannalahi!"Alhaji Hafeez ya ce dan Allah bawan Allah kayi hakuri!"Sallau da Aleeyu durkushe suna tsintar kayan miyan da Aleeyu ya samo da kyar saboda rashin kudi!"Domin kudin da yasamu Tarawa yayi domin ya kaima yan NEPA su kulla masa wutar da aka yanke agidansa kimanin mako biyu yanzu."

"Kudi Alhaji Hafeez ya dauko a aljihunsa ya mikawa Aleeyu da ke durkushe yana kwashe kayan sa."

"Tashi yayi tsaye yana kakkabe jikinsa da ya baci da ruwan tumatir yace ka barshi Alhaji nagode inji Aleeyu."Dagowar da zaiyi sukayi ido hudu da Alhaji Hafeez da yayi tsuro yana kallon Fuskar Aliyu da bazai taba mantawa da ita ba arayuwar sa duk wuya duk tsanani!"

"Shima Aleeyun,Alhaji Hafeez yake kallo tare da nuna shi da ya tsaya yace Abdul Hafeez malami!"Kai ne kodai gizo idona keyi min!"

"Rungume shi yayi tare da cewa nine Aleeyu meya sameka!"Me kakeyi anan!"

"Sallau yace yallabai ai shi ne ya wanke ma mota Malam Ali ga kudinka!"Ya miqawa Aliyu kudi!"yanauu mamakin shin ko sun san juna!?"Meye hadin yallabai da Malam Ali?Da wadannan tambayoyin ne yayi tsaye yane sauraren ko zai samu amsar su awurin!"

Toufah muje zuwa.......

*Alqalamin*
*Nabila Dikko*🖊

********

*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)

*Humaira* ta zabga uban tagumi tarasa samo mafita arayuwarta Rana zafi inuwa quna yanzu idan tace zatabi ra.ayin khamal itace zata cutu tunda ayanda yake tafiye tafiyennan ita kadai take zaune da kadaici ackn gidansa to inko ta haihu tabbas kadaicin zai rage mata zataringa ganin babynta atare da ita gashi danginta sun juya mata baya ballantana insun rabu da khamal takoma gunsa tunda akullum gargadinsa agareta shine kota yarda tayi planning kokuma yasaketa

Iyayanta basa sake mata adalilin tabujire musu a Auren khamal din tazabeshi akansu

Da kawayenta guda biyu kawai take mu,amula zainab zee da Ashanty dukansu basuda Aure Zee baxawarace tarabu da mijinta akan baxai barta tayi aikiba ita kumaa tafison aiki datake na banki fiye da komai arayuwarta Ashanty kuwa karatune yahanata Aure ita yar Akidar sai anyi dogon karatune kafin Ayi Auren

Sallamar kawayen nata taji atsakar gida

Tayi sauri ta goge hawayen daya fara ziraro mata akuncinta

Ta taresu da murnarta

Suka zazzauna takawo musu ruwa da lemo tana fadin "kuyi hkr banyi girki ba yau.

Zee tace "ke ko akanme zaki zauna bakiyi girkiba kada fa kiyiwa kanki illah abanxa awofi akan damuwar d'a namiji donshi inya futa me dadi zaici a restaurant

Ashanty ta tabe baki tace "barta dan Allah kawata gara dai takashe kanta akan hakurin gidan Aure kinga inta mutu saiya Auro me daidai ra.ayinsa

Hawayene yaziraro mata tasa hannu tahau gogewa tana fadin "ko ayau ma yajaddadamin cewar inhar banyarda naje nayi planning ba to yan gb da sake aure kuma zai rabu dani ako yaushe inya gaji.

"Ya dade baiyi Aurenba dan abu kaxa ta ubanshi...zee tafada da dagawar murya domin ita din mafadaciyace akwai saurin fushi da zuciya

"Ai walh kada kiyi planning dinma kome zaiyi sbd nangaba inmahaifarki ta lalace kece zaki cutu bashiba kuma kina gani zaiyi auren yahaihu anuna mk gadara agida wata tazo tafiki power agunsa alokacin dazaiso haihuwar.

Ashanty ta gyara zama tace "a.a zee kibarta tabi ra.ayin mijinta sbd su sami zaman lfy nasan humaira kina son khamal sosai kada gaba kiji haushinmu fa kuma kekanki inkika tsara iyalin ai zakifi kyan jiki koke Zee da kikai Auran ba planning din kikaiba sbd aikinki?

"Banyi planning ba Ashanty Allah ne baikawoba natabayin bari ma alokacin ina amarya.

Humaira datayi kasake tanajinsu ta gyara zama tace "ina son khamal baxan iya rabuwa dashiba gashi ina son haihuwa fiye da yanda nakeson kaina yanzu bansan mafitaba.

Zee tace "to abinda xance mk dai daxarar kin samu cikin zanhadaki da malamina ayi masa rubin baki kawai.

Ashanty tace "nikuma da zakiji shawarata dakin bi ra.ayin mijinki kawata kada asami matsala.

Humaira ta harari Ashanty tace "kefa kinada matsala Zee tafiki hankali da hangen nesa

Zee tayi dariya tace"barta dai kawata saitayi aure zata gane.yanzu dai yakamata kifara zuwa nakaiki ma gun mallam mudan din domin yafarajin bukatunki kafin samuwar cikin.

Humaira tace "to ai yanzu banida kudi walh yadaina bani kudi kwata kwata da kansa yake yin siyayyar komai na girki dan kar inkaru dashi

"Tabdijan maza kenan gadai gida har gida yaji kayan alatu amma matar gidan zero take.

Suka sheqe da dariyar keta zee da Ashanty harda tafawa "zee tace "kada kiji komai zansa yai mk lamunin aikin farko ko inbiya mk inyaso next saiki tanada

Humaira tayi mata godiya

Sunsha hirarsu kafin su tafi

Ashanty da zee da humaira kawayene sosai tun jss one har shigarsu jami.a tare suke basa fada kansu hade yake matsalarsu guda suna buga ronce suna shan shisha amma ita humaira batayin ko daya saima insunyi tabisu da Nasiha dan sudaina.

BAYAN WATA biyu ckn qudirar Allah humaira tasami ciki ahakan yana basar da ita yana juya mata bayan saida Allah yakawo rana guda daya nemeta ciki yashiga

Asatin dayai tafiya sarin motoci kwatano tafarga da hakan

Tun tanajin tashin zuwciya har tadawo tana kelaya amai ga bacci datake faman yi ba dare ba rana da kanta tafahimci ko me kenan

Da gaggawa takira zee awaya tashaida mata halin da take ciki.

Zee tace "Ayya yarinya ciki yasamu saiki shiryah muje gun mallam kawai ayi addu.ar rufin bakin khamal.

Humaira taringa murna aranta tana ayyana cewar zata iya komai akan wannan cikin inhar zata haifeshi kalau tana son haihuwa tanaso taga ta tara yara kamar biyar kobakwai agabanta domin "ya"ya Rahama ne …………

*daga Alqalamin Auntyn Sayyada Da Shahida* ne👌🏼🖊
[7/5, 5:35 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA* 👩‍👩‍👧‍👧

*4 Stars writers*
👇🏽
*Nabilah Rabi,u Zango*
*Marubuciyar Zamani*
*Nabeelart Lady*
&
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
&
*Nabila Dikko*
&
*Nabila Mmn khalil*

*Page* 0⃣3⃣

Ranar monday Da safe kafin humaira tagama shirinta tasa waya takira ogan nata khamal domin ta gaya masa zataje asibiti amma saitaji ba,a daga ba bata hakura ba tabada taxarar minti biyar takara kira taji andaga amma ba muryar mijinta tajiba muryar mace taji ta daga tana fadin "wacece yashiga wanka ne.

Ran humaira yai matuqar baci dataji macece tadaga mata wayar miji harma wai take gaya mata cewar ya shiga wanka it means ma kenan tare suka kwana

Takalli agogo taga takwas da rabi na safe

Taja tsaki domin tasan tunaninta bai bata wrong ba tabbas mijinta da mace yakwana wato abinda yakeyi knn inyai tafiya ?shiyasa baya damuwa da ita knn tunda yana samun abinda yake so awaje?
Chapter 3 · 0% Book details