← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana haka ne Allah ya kudurta ikonsa domin kuwa Allah yahada abinda ake gudun hadawa don kuwa ansami kubucewar abubuwa don kuwa rabo ya rantse aranar dayayi sau daya jal Allah ya mantarsa yayi ackn kuma ciki yasamu Hhhhmmm 😃 sautari sai yayi rawul biyu arana sbd shi mutum ne mabuqaci gashi yanajin dadin humaira kamar sabuwa yake jinta domin tasan takan gyara dashan abinda zaikara mata testing

Gata da iya salo salon kwanciya da tarayrayar miji a shimfida

Baby Nabeelah tana wata biyar Khamal yatafi Dubai yin wani business dinsa shida budurwarsa Aleesha domin yaso yatafi da humaira amma saiyace mata "kinga kinyiwa kanki kin dakushewa kanki rayuwar jin dadi dake yadace intafi tinda zan dade to amma kinzama uwar "ya"ya ga jego dole kizauna kiyi gadin yara da gida inyaso gaba innayi aure sai intafi da wacce ta gyagije jikinta ta tsane kanta ke kuwa saikiyi tazama kina haihuwar abokan shawara jigon Al,umma ko? Yak'arasa fada yana kallonta yana mata dariyar k'eta

Cikn Jin haushin kalaminsa tace "eh fadi ka kara *MATA JIGON AL,UMMA* Ne aduk inda muke mune gaba kuma ina godewa Allah da yadda ya kaddaromin tawa rayuwar don natabbata tafi ta wata kuma indai Aurene kayi uku arana d'aya bakada matsala dani.

Yaso ace yabak'anta mata rai to amma yasan humaira bakomai ke bata haushiba

Koda yad'age kafa yatafi saitaji babu dadi gidan don yai mata sabo da soyayyarsa amma inta kalli yaranta saitaji farin ciki yaxiryarceta tabbas haihuwa rahama ce

Twins sune masu wayo suna zuwa sch daga boko har islamiyya

Dayake yabar mata komai na kayan abinci dana amfanin gida da kudi ahannunta hakan baisa ta damuba don saida yayi sati kana yakirata awaya

Koda suka gaisa ackn yaran Amal yafara tambaya don yana son yarinyar sbd kyanta don yasan kyanta zai iya daukaka darajarsa inya Aura mata mekudi anan gaba

Twins suka gaidashi one by one ta wayar

Amal tayita masa gwaranci yana dariya ta wayar

Aleesha datake toilet tana wanka tana jiyoshi

Koda tafito dg toilet din zuwa tayi ta amshe wayar ta kashe zaiyi magana kenan ta cilla harshenta abakinsa tuni yahau tsotsa

Ita kuwa humaira abata bangaren dadi taringaji aranta ganin yanuna kulawarsa ga yaran

Duk alokacin bata san tanada ciki ba saida yayi wata guda da tafiya

aranar data fahimci tanada cikin ba karamin damuwa ta shiga ba domin ita kanta taso ace sai baby Nabeelah tashekara kamar yanda Amal tayi

taje tayi test and scaing komai yabayyana tar domin cikin yashiga wata uku likita yatabbatar mata amma basu gano mata ko wane jinsi bane likitan yace sai inyayi 5 tadawo aduba

ta rame tayi kyau sosai tabbas da ace ogan nata nanan zai iya ganowa da kansa cikine da ita

taci alwashin kuwa baxata taba gaya masa ta wayaba har saidai inya dawo yagani

Dayake likitan yabata shawara akan kada ayaye baby Nabeelah domin tsiranasu da ciki dai wata ukune ta bashi ita baby tanada 6 mounth ciki 3

Awannan karan ta tara kawayenta taringa musu kuka tana neman mafita agunsu domin ta zayyane musu labarin abinda yake wakana again a tsakaninta da khamal

Ashanty takama baki tace "ashe dama bai hkr ba?dama bai sauka daga wannan kudirin nasa nabanza da wofiba,lallai saiki zauna kibiye masa kada kidau mataki walh nagaji Humaira wannan karon bazan mk komai akaiba ido zan zuba inga iya gudun ruwanki keda Khamal idan keme zcy ce zangani

Ita kuwa Zee dariya tayi kawai tana fadin "Humaira kenan yanzu ke amatsayinki na mace harsaikin zauna munbaki shawarar yanda zakiyi to walh kigyara tun wuri
n
inba hakaba kuwa kixama kazar figa agun khamal

Aranar dai agaba suka sakata suna zazzaga mata masifa na yanda tabari namiji yarainata tana kuma wahala agdn miji

Zee tabata shawarar cewa "kada kisake kifada masa ma kinada cikin tunda kinsan halinsa kibarshi koda kafin yadawo zaki haihun tunda akwai danginsa bakida matsala awannan fagen

Humaira ta dauki shawararsu kuma tace zatayi amfani da ita

****

Saida Cikinta yashiga wata bakwai Sannan khamal yayi mata waya kancewar zaidawo asatin yagama abinda yajeyi

Ta wani bangaren tayi farin ciki amma ta wani bangaren saitaringajin inama kada yadawo har saita haihun Baby Nabeelah wani kuzari take kara samu itakam babu mecewa tasha ciki don watanta goma amma saika dauka ko tayi shekara da rabi itadin akwai garin jiki tafara takawa abinta ga hakora sunfito abakinta baby kyakykyawace duk kyan Amal bata kama kafar taba domin Sunan Nabeelah ma na musamman ne balle Nabeelan kanta tabbas Kyau yanagun baby Nabeelah Tabbas Dole ne baby kiyi kyau domin Daga Sunan ne...🤪🤪

******** **********

*Alk'alamin*🖋
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
( *Nabeelert Lady*)
👇🏻

Dan Allah Mufty ka fad'a mani abinda ya faru, naga daga yin maganar Ham.... Hannu Mufty ya d'aga mashi yana fad'in idan kana son mu b'ata kacigaba dayi mani maganar wannan yarinyar, ni ban santa ba, haka kawai da ka fad'i sunanta kasa kaina ya sara, dan Allah kadena mani maganar ta.

Jinjina kai Mansur yayi jin abinda Mufty ya fad'a, azuciyarsa yana fad'in tabbas akwai wani babban al'amari da yake faruwa a wajen abokinsa, dama tun ranar daya fad'a masa ya samu matar aure daya tambayeshi ina maganar Hamrah yaji yace wacece Hamrah ya dasa ayar tambaya akansa, bai gama tsinkewa da lamarin ba sai da Mufty ya kaishi wajen Hibbah domin su gaisa.

Tunda yaga Hibbah da yanayinta kawai yaji bai yarda da ita ba, zuwa yanzu ya gama tabbatar da abinda yake zargi, amma sanin halin Mufty yasa bazai d'auki wani mataki ba, tunda dai mugunta sukayi ma Hamrah gara ya kyalesu tazo gidan Muftyn taji abinda akeji da kanta zatayi nadamar abinda ta aikata kuma ta tona asirin kanta.

Murmushi Mansur ya saki ya kalli Mufty yace haka ne abokina, nima haka kawai sunan yazo mani abaki, kada ka damu daga yau na gama maganar ta, muje wajen Kawu da kace zan raka ka.

Murmushi Mufty yayi yace yauwa ko kai fa, muje dama akan maganar kai kayan sa rana ne kasan ba wani rana mai tsawo za'a sa ba. Mansur yace yayi angon Hibbatullah, muje.

Zaune suke a wajen Kawunsa bayan sun gama maganar kai kayen sa rana Kawu yace yanzu kai Muftahu ka kammala gyaran d'akin da zaka ajeta ko? Duk'ar da kai Mufty yayi yana fad'in Kawu ai abokaina sun kama mani haya na shekara d'aya kafin mu cinye shekarar ma na kammala gyaran gidan sai kawai na maidota can, bana son raba kan iyalina nafison su zauna waje d'aya dan bana son wata tace ana cutar ta.

Jinjina kai Kawu yayi yace wannan haka yake, shiyasa nake sonka saboda kasan abinda kakeyi, hakan yasa nake kok'arin shige maka gaba a duk wasu al'amuran ka, a wannan zamanin kafin ka samu namiji irinka mai son kwatanta adalci a wajen iyalinsa da wuya. Bakomai, tunda ka samu wajen da zaka ajeta kafin ka kammala gyara ai bakomai, dan haka zuwa gobe sai ka kawo kayan sa ranar sai akai masu.

Goduya sukayi mashi kafin suka mashi sallama suka tafi. Suna fita Mansur ya fara dariya yana kallon Mufty. 'Daure fuska Mufty yayi yana fad'in kai fa d'an iska ne, ya zaka tasani gaba kana mani dariya kamar kaga sabon kamu.

Mansur yace ai dole nayi dariya, wallahi Mufty kana bani dariya sosai akan yanda kake tafiyar da al'amuran ka, yanzu Kawun ma bazaka barshi ba sai ka shirga masa k'arya.

Mufty yace haka duniyar ta gada yanzu ai, kana tunanin idan Kawu yasan cewar ko gidan da zan zauna ban kama ba kai kasan bazai shige mani gaba wajen kai kayan sa rana ba, kana ganin da yanda sukaje tambayar mani aurenta ma.

Mansur yace haka ne, kaga sai kayi kok'arin samun gidan da zaka ajeta. Mufty yace kada ka damu, a Tudun wada zan samu k'aramun gida mai sauk'i na kama, zuwa rabin shekara ma ya isheni na gyara mata d'akin da nake ciki sai ta koma, tunda an riga an d'aura auren ai dole ta zauna.

Dariya Mansur yayi yace Allah ya shiryeka, wallahi kayi dai a hankali, naga kana yima mata abinda kaga dama, to kada ka manta *MATA JIGON AL'UMMA NE*, idan ka wulak'antasu wata rana dole ka nemesu, domin ba'a wulak'anta mata. Mufty yace naji ya Ustaz, muje kada ka tsareni da wa'azin ka. Dariya Mansur yayi yace muje.

**** ****

Tun daga ranar da Bilal ya san cewar Hamrah ce Mahaifinsa zai aura ya nemi farin ciki ya rasa, sosai yake cikin damuwa wanda hakan ya haddasa masa matsanancin ciwon kai, sosai mahaifiyarsa take cikin damuwa, Bilal shine babban d'anta, sam bata son ta ganshi cikin damuwa.

Kwance yake a d'aki idanuwanshi suna kallon sama hawaye suna zubowa daga cikin su, sosai yake jin bakin ciki, taya zai iya zama agidan nan yana kallon Hamrarshi amatsayin matar Mahaifinsa kuma kishirya Umman sa? Tabbas idan har haka ta kasance dole yabar gidan, gara ya lalab'a mahaifinsa ya barshi ya tafi k'aro karatu waje daga can ya samu arik'eshi kawai yayi zamanshi, idan yazo ganin Iyayenshi ma bazai wuce sati d'aya ba, shima dole ya kammala gininshi idan yazo yarik'a sauka aciki.

Motsin bud'e k'ofar da yaji ne yasashi saurin goge hawayen da suke kwance a fuskarshi. Ummanshi ce tashigo fuskarta cike da damuwa. Bayan ta zauna ta kira sunanshi, tashi yayi ya jinginar da kanshi jikin gado yana amsawa.

Bilal ina so ka fad'a mani abinda yake damunka idan har kana son ganin farin ciki na. Duk'ar da kai Bilal yayi yana fad'in Umma bakomai kawai ciwo ne daga Allah.Wallahi kaji na rantse maka matuk'ar baka fad'a mani abinda yake damun ka ba zan fita harkar ka, haba Bilal, dame kake son naji? Da bakin cikin da Mahaifinka yake son k'unsa mani ko kuma da halin da ka shiga, har yanzu babu wanda yasan da maganar auren mahaifinka a cikin unguwa da yanzu an fara mani tsegumi, ya kake tunani duk lokacin da maganar ta fito zan kasance acikin mutane? Kasan halin mutanan garin nan, jira suke suji wani abun magana ya fito daga jikin mutum shikenan su baza farantin gulma, dan haka idan har bazaka fad'a mani abinda yake damun ka ba kada na sake ganin fuskar ka a idona.
Chapter 20 · 0% Book details