Sashe 5
Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"MAwakiya Hindu Alqali nan take ta canja kid'a da waqa,"In da take cewa."Ahayye mata!Ahayye manyan mata kuna ina ne!!?Kid'an ku dabam da na saura!Shigar ku dabam da ta saura *MATA JIGON AL'UMMA* A hayye manyan mata,Mata tubalin AL'UMMA ba'ayi sai da ku mata,Gidan da ke ku zai haskah, Hajiya saudat taka rawa... rausaya wannan Jama'ar duk nakine uwargidan Chairman na nagode..." ,Hajiya laila giwar mata!"Hajiya Faty bnsanki da wasa baah!"Buki naku maganin akwabe ku Hajiya rahma nagode!"Ga Yan biyu can kyautar Allah, Hajiya Hassana da husaina ni Hindu na gaisheku "Khadija kaka da Maryam E.s nagode Ina Hajiya Uwany Baguda da Saj Mumyn yusuf nagode kutayi min barin naira Allah saka nagode!"A hayye bukin manyan mata maganin kananan mata!"A hayye matan manya.... wacce batada naira dole ya kauce!!"Kija da baya ki kallo.."mowa na rawa waye bora..!"A hayye Ku taka manyan mata ku juya ku rausaya Hamshakan mata....."
"Tunda mawakiyar ta fara waqar su Hajiya lailah da Fatyma suka ban zama filin suna rawa suna mannawa Hajiya saudat kudi 1k suke zuba mata kamar takardar banza."Matan wurin suka dauki shewa!"Hakan ita ma Hajiya saudat ta dinga mayar masu martanin naira!"Duk sauran jama'ar wurin sai faman liki akewa uwar bukin..."Saleema ko tuni abin duniya yayi mata katutu arai!!!"dan kudin Karin ma Batada su da kyar tasamu naira dubu tayi canjin yan Dari daya.."Ta dan watsa duk da hakan ta sha habaici ga mawaqiyar dan sam batayi da matan da basu zuba mata naira!"Hakan daga cikin mata yan buki sai nunata akeyi ana gulma dan ba'a ga tayi wani abin azo agani ba duk shan qamshin ta da da hurar hancinta ashe na banza ne!"Dan qawayenta sai mulmula sukeyi suna barin kudi."
"Hakan dai aka tashi bukin Zuciyar Saleema ba dadi ganin har ledar bukin su na da bambanci da ta su Fatyma da lailah dan nasu masu yawan gaske natan bai kai nasun ba!"A zuciyarta ko cewa takeyi musiba ce ta talauci!"
"Tana cikin tunanin ne lailah ta ce "Salimcy (Da yake hakan suke kiranta idan suna son zolayarta)Lafiya na kinyi shiru menene?"
"Mtssssssw!!!Bari kawai lailah wallahi zaman nan nawa da Aliyu yana damuna hakan zamu kare rayuwar Mu a talauci!?Ni gaskiya na fara gundura kuma ban san ya zanyi ba!"Ki duba yai nafita dabam da ku sai habaici da gulmata akeyi saboda angani ba kamar da ba sai borin kunyar tsiya nikeyi!!!"
"Hahaha daman nasan za'a rina!Qawata duk hakurinki zai qare watarana ai zama cikin T class(Talauci) baiyi ba !"Sai yasa ka muzanta acikin sa'anninka!"Kedai kiyi hakuri kawai tawan Inji lailah
"Fatyma da ke Driving ta kalle su kana ta ce Hakane dan nifa na fahimci hakan ko mu da ba a tashi tare ba yanda kika koma dinnan da bzamu zauna da ke ba!"Damar abin kyaunki da kirarki suna nan daram ajikinki!"Hmnnnn..."Shekaranjiya fa da kinka je gidana Saleema abokin Yallabai har zancenki yayi min nace masa wallahi kina da aure...."
"Haba faty kin ko goga min tsiya wane aure ana fama da talauci ko kashe auren bazanyi ba nayi auren arziki!?Inji Saleema fuskarta dauke da takaicin fatyn!"
"Lailah kinji fa... Saleema ni yanzu tayaya zance batada aure alhalin da aurenta!Gaskiya na fada masa kunsan manyan mutane basa wasa musamman idan lamarin aure ne shi ta Hudu ya so yayi da ita.."Fatyma ta ce tana dariya.''
"Tsaki Saleema tayi akaro na biyu!"Ta kalle su ta watsar!"
"Allah ya raka taki gona ko salima me zakayi agidan matan aure uku ai munfi karfin kishiya!"Da ace ita kadai ce da zamu bata karfin gwuiwa ta kashe auren Aliyu tunda yanzu ya riga da ya zama goro ko abin saye"Sai ta aure abokin yallabai!"In ji lailah."
"Saleema ta ce wallahi baku ganewa ni yanzu na shirya rabuwa da Aliyu sai dai na bar iyayena wallahi tunda sun ce basu bani matsawar na bar Aliyu ni kuma nasan kudi na saye zuciyar kowa a yanzu!"Idan hegun sun zaunu duk zan saye bakin Nasu mu shirya!"Ni yanzu kawai ki hadani da Alhajin dan Allah fatyna!"Saleema ta fada kalar tausayi da rarrashi."
"Dariya sukayi daga lailah har fatyn sukace yau ina kishin ki Saleema munga ya bace gudan mace uku fa!?"
"Ko gidan mace sha daya ne zan cike mu zama dozen!"Ba kun san yadda nake rayuwa ba!"Amma kun san wani abi ai!"
"Hakane Saleema nasan akwai wahala kasaba da zaqi ka kuma ga madaci amma karki manta Aliyu na sonki!"Yayi maki komai a rayuwa ke da iyayenki!"Bai kamata ki kashe auranki saboda wani dalili naki ba!"Ban son nazamo sila kuma yar jagoranki domin cikar burinki na barin gidan Aliyu!Ya nada ilimi kirki da mutunci mukan mu munsan yafi mazan mu zama nagari!"Aliyu baya bin matan banza Saleema!"Mufa kasashen waje suke zuwa suna shar holiyarsu saboda sunada kudi!"Tun bamu sani ba har muka gane!Kuma babu yadda zamuyi duk kokarin mu!"Duk macen da kika gani gidan miji tanada irin nata matsala duk jin dadinda takeyi nidai shawarata ki zauna yallabai mijina ne duk abokan shi halin su daya na Neman matan banza ki tsaya gidanki yafi maki sauki!"Inji Fatyma daidai lokacin da tayi parking kofar gidan na Saleema."
"Fita tayi daga cikin motar kanta ta raqafa gefen wurin da fatyma take a glass din motar sannan tace naji duk zancenki nagode Fatyma!"Dan Alhajin yana abokin mijinki zaki hana na aure shi!?"Sai naga ni naji na nace inaso me zai hana kibarni ko matan duniya zai bi banda damuwa matukar zanci nasha na saka sutura mai kyau inje duk qasarda nake son zuwa kamar ko to banda matsala!"
"Lailah tace''Gaskiya Fatyma kina da saka abu arayuwarki nima wallahi Saleema ba ruwa nidai kudi sune damuwa tag!"Kuma kada kiji komai zamu daidaita ki da Alhajin."Kafin nan an sayar gidan nan naku an nemo miki motar kamar yadda muka tsara!"Yanzu gobe zan turo dillalena na filaye ya duba gidan!"Karki damu salimcynah!"Lailah tace tana dariya suka tafa ita da lailah!"
"Fatyma ma dariya suka bata dan tasu tafi zama daya da laila ta ce"To salimcy sai mun hadu zamu qarashe maganar amma fa kiyi hakuri farinciki da arzikinki duk namu ne abota ba wasa ba zAnyi ma Alhaji magana idan yadawo jibi dan sunyi tafiya da yallabai China."
"Yawwa fatty koke fa nagode sai munyi waya."Saleema ta wuce daga ciki su kuma motar su sukaja suka wuce domin kowacce ta nufi gidanta suna cigaba da firar su."
"ALIYU hannun Alhaji Hafeez ya rike izuwa cikin inuwa sannan ya dauko tebur ya azama su suka zauna ya ce"Abdul Hafeez kaga yanda nadawo kamar ba ni ba ko!?Hafeez ya ce "Eh Aliyu wai meke faruwa!?Hawayen da yake kokarin kada su zubo masa su bata masa fuska ne suka fara biyo lafiyayyar fuskar sa!?Dan bakin sa mai kyaun gaske ne yafara motsawa yayinda lafiyayyun labban sa suka bude har fararen haurunsa suka bayyana yace cikin muryar sa mai dadin sauraro Abdul Hafeez naga jarrabawar rayuwa tun bayan RABUWAR MU. ......."
*Alk'alamin🖋*
*Nabila Dikko*
***** *****
Jinjina kai Alhaji Garba Yaro yayi daya gama jin bayanin Malan Bukar, shiru yayi na wani lokaci, domin kud'in da Malan Bukar yake so suna da yawa, duk da shi Alhaji Garba Yaro bai da mugunta, yakan bada bashi ga duk wanda yake tare dasu, abu d'aya ne baya so shine mutum yaki cika alk'awari.
Gyara zama yayi yana kallon Malan Bukar yace naji abinda kace, badamuwa zan baka rancen million d'aya kamar yanda ka buk'ata, kuma kayi alk'awarin zaka maido ana gama bikin d'iyarka, kasan halina bana son magana biyu, badan mun dad'e da kai ba kuma kace bikin d'iyar zakayi hakan zai sa na baka, domin nima Uba ne, bazan so ace an saka bikin d'iyarka ba azo za'ayi kuma babu kud'in yi, dan haka zan baka.
Washe baki Malan Bukar yayi yana fad'in Allah ya biya Alhaji, hakik'a ka taimakeni alokacin da nake buk'atar taimako, ubangiji Allah yayi maka abinda kake so.
Murmushi Alhaji yayi domjn yaji dad'in addu'ar da yayi mashi. Tashi yayi yana fad'in zuwa gobe zan had'a maka kud'in, kuma zan d'ora maka dubu d'ari asama amatsayin gudummuwa ta. Duk'ar da kai Malan Bukar yayi yana godiya. Haka ya tashi ya nufi gida cike da farin ciki.
Lokacin daya fad'ama Kubra yanda sukayi da Alhaji Kubra sosai taji dad'i, koba komai za'ayi bikin d'iyarta hankali kwance komai yaji.
Kallon Malan Bukar tayi daya buga tagumi alamun tunani, tab'oshi tayi tana fad'in Malan lafiya kuwa? Naga kazo da abun farin ciki amma lokaci d'aya fuskar ka ta koma damuwa. Ajiyar zuciya Malan Bukar ya saki yana fad'in kedai bari kawai Kubra.
Gyara zama tayi tana fad'in akwai wata matsala ne? Malan Bukar yace nasan halin Alhaji fiye da tunanin ki, mun dad'e tare dashi, Alhaji baya d'aukar makudan kud'i ya bama irina bashi, duk wanda yake harka dasu masu akwai ne, kuma baya d'aukar raini, matuk'ar ya baka bashi idan lokacin biya yayi baka biya ba baza kaga da kyau ba.
Gyara zama tayi tare da rage murya tace kai yanzu Malan a tunaninka biyan kud'in nan zakayi? To idan ma biyan zakayi ina kaga hanyar biyan? Kasan dai ko rabin kud'in bazaka iya had'a mashi ba a bikin Hibbah, idan ma kana tunanin idan na samu gudummuwar biki zan baka ahad'a to ka makaro, domin duk bikin da zanyi ma wasu bana bikin kud'in, gara naje wajen dillaliya na ciyo bashi na kai, kaga kuwa nima babu wanda zaiyi mani bikin kud'i, kozan samu wallahi bada yawa bane.
Kallonta Malan Bukar yayi yana fad'in wallahi har kinsa jikina yayi sanyi, dama fa akanki na ta'allak'a, nasan ku mata kune masu yin biki, nasan bayan bikin nan dole za'a samu wasu kud'i awajenki masu kauri, kinga idan na had'a dana wajena kila cikon kad'an ne, amma yanzu da kikayi wannan maganar sai naji kin sare mani guiwa, jinake kamar na maida masa kud'insa muyi abinda Allah ya hore mana tunda gashi yace zai bani dubu d'ari kyauta.
A zabure Kubra ta tashi tana fad'in haba Malan, da hankalin ka kake fad'ar wannan maganar? To wallahi bari kaji, babu wanda zai hana mu amsar wannan kud'in, dole ayima Hibbah kayan d'aki na gani na fad'a, dan haka ina da shawara idan kai baka da abunyi.