← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayarta ta d'auko tana fad'in bara na tambayeshi yanayin gidan yanzu. Umma tace yauwa ko kefa.... Ringing biyu tayi ya katse kiran ya kirata. Jinjina Umma tayi mata tana fad'in harkar girma.

'Daukar wayar tayi... Bayan ta tambayeshi ya koma lafiya sai tace ya fasalta mata yanda gidan yake tunda bada wuri za'ayi jere ba dan su san abubuwan da zasu saya.

Murmushi Muftahu yayi yana fad'in dan wayar ki bata whatsapp da vedion gidan zan turo maki, to bana son kirik'e babbar waya gara sai munyi aure shiyasa.... Gidan babbane gaskiya, a GRA yake daga bayan gidan Piya-Piya, akwai babban falo mai d'auke da dining area, sai kitchen babba mai had'e da store, d'akuna ukku ne kowanne da band'aki, sai wajen motsa jiki, gaba d'aya gidan tiles ne, so ba ruwanku da siyo leda, kayan na'ura na amfanin kitchen ma duk akwaisu ba sai an siyo ba,,,, daga wajen gidan akwai lambu da wajen wanka.

Dariya Hibbah tasa tana fad'in nagode Mufty nah. Murmushi yayi yace haba bakomai, dan ma ansa bikin da wuri naso na bada oder a kawo mani komai daga Dubai, amma bakomai idan kinzo sai muje mu siyo kawai, idan yaso naki sai a bama Umma. Hibbah tace nagode. Sallama yayi mata ya kashe wayar.

Rungumeta Umma tayi tana fad'in nayi farar haihuwa, wata rana ma Dubai d'in zaku koma gaba d'aya. Hibbah tace ai da hada ke zamu tafi. Dariya suka sa gaba d'aya

***

Zaune Bilal yake a gaban mahaifinsa kansa a k'asa, kallonshi Alhaji yayi yana fad'in Bilal wai meyake damunka ne? Kwana biyu naga kamar kana cikin damuwa, ba dai kana taya Momyn ka kishi bane akan auren da zanyi? A firgice Bilal ya d'ago kai yana kallon Alhaji dan bai san da maganar auren ba.

Murmushi Alhaji yayi yana fad'in ko bata fad'a maka zanyi aure ba? Jiya mukayi maganar da ita ai. Sosai idanuwan Bilal sukayi ja jin mahaifinsa zaiyi aure da wannan shekarun nashi.

Duk'ar da kai yayi yana fad'in Abbah aure kuma? Amma naga baka tab'a maganar k'ara aure ba. Alhaji yace aishi aure hab'o ne, idan yazo ba'a iya tsaidashi.

Bilal yace to Abbah wata ka samu mijinta ya rasu ko kuma rabuwa sukayi da mijin shine zaka aureta? Dariya Alhaji yayi jin abinda Bilal yace. Kallonshi yayi yana fad'in bani da ikon auren budurwa sai bazawara kenan ko? Bilal yace ba haka bane, naga shekarun ka sunja ne.

Alhaji yace waya fad'a maka ana tsufa da aure? To k'aramar yarinya zan aura, idan kasan Hamrah d'iyar wajen Malan Bukar to itace zan aura..... A zabure Bilal ya mik'e jin abinda Alhaji ya fad'a... Hamrah? Ba dai Hamrarshi ba? Girgiza kai ya farayi yana ja da baya hawaye suna zubo mashi.

Da kallon mamaki Alhaji ya bishi ganin yanda ya firgice. Momy ce tashigo falon d'auke da ruwa, tana shigowa Bilal yana zubewa k'asa a sume. Saurin aje ruwan tayi suka nufi kanshi su duka.

****

Zaune Hamrah take a d'akin mahaifinta ta gama fad'a mashi tana son zuwa wajen dangin mamarta tayo kwana biyu. Kallonta Malan Bukar yayi sai yaga duk ta rame, tausayinta ne ya kamashi, sai dai baya iya nuna hakan.

Gyaran murya yayi yana fad'in kin fad'ama Umman ku ta amince ko? Da sauri Hamrah ta d'ago kai tana kallonshi jin abinda yace. Malan Bukar yace tambayarki fa nakeyi.

Umma ce ta shigo tana fad'in ina fa zata fad'a mani, kasan ai bata d'aukeni da muhimmanci ba, da Uwarta tana raye zata shirya tafiya ne bata fad'a mata ba kai tsaye tazo wajenka.

Malan Bukar yace ashe bakida mutunci Hamrah? Da kikazo wajena kina fad'a mani nufinki na barki ki tafi ba tare da kin fad'a mata ba? Hamrah tace dama zan fad'a mata jira nake ka fara amincewa tunda kaine babba.

Salati Umma tasa tana fad'in kaji mani wulak'anci ko? Lallai wuyanki ya isa yanka, yau da ace ban haifa ba sai nayi kuka, tunda haka tace Malan gatanan sai kacigaba da zama da ita, kuma wallahi tana sa k'afa tabar gidan nan nima na barshi, tunda bani da matsayi.

Saurin tashi Malan Bukar yayi yana fad'in haba ita d'in banza, babu inda zataje sai da amincewarki, ai bata da wata Uwa data wuce ki, tunda kince baki amince taje ba babu inda zataje.

Murmushi Umma tayi tana fad'in yanzu naji magana, sannan ina son ka amshe wayarta domin tana waya da samarinta kaga kada ta maidamu k'ananan mutane.

Malan Bukar yace wannan gaka yake, kallon Hamrah yayi yana fad'in tashi ki d'auko mani wayarki yanzu. Tashi Hamrah tayi tana wani irin kuka tayi waje. Tana fita Hibbah ta kwashe da dariya. Haka ta d'auko wayar ta kai mashi.

Amsa yayi yana fad'in idan kinyi auren Alhaji zai saya maki da kanshi, wuce ki bani waje babu inda zakije. Da sauri ta fita tana kuka. Malan Bukar yace kiyi hak'uri kinji Kubra. Murmurshi tayi tace haba ai bakomai, tunda ka bani girmana ai ta wuce, bara na kawo maka abincin ka.........

****** ******

*ALQALAMIN*
👇🏽
*Nabilancy Luv* 💘 (Auntyn S&S)🖊

Humaira nagama karanta wannan sakon jiri yakwasheta ta fadi

Ashanty tayi saurin tarota zuwa jikinta a rude ta ringa girgizata tajita shiru ta taba kirjinta taji baya bugawa ai atsorace ta turarta ta nufi kicin don samo ruwan da zata shafa mata domin suma tayi

Arude Ashanty taringa shafa mata ruwan afuska tana kiran sunanta

"Humaira tashi mana!humaira!!humaira kada ki mutu ki tashi dan Allah "

Can ta numfasa ahankali

Ashanty tahau girgizata da karfi tanaci gaba da shafa mata ruwan afuska

Allah dai yataimaka ta dawo sosai ta kurawa Ashanty ido

Ashanty tace mata "humaira tashi mana

Humaira ta tashi zaune dakyar tana fadin "Ashanty mafarki nakeyi ko gaskene?

Ashanty ta kura mata idanu kana tace "humaira kidawo hankalinki.humaira ki dawo nutsuwarki kijini dakyau walh tallahi kada ki kashe kanki akan namiji domin asara yaranki zasuyi su kadai bandashi domin nafahimci duk wannan son da kike masa shi baya mk shi,

Humaira yakamata ace yanzu kinyi hankali kinsan ciwon kanki kina wahala akan namiji walh innice ke bazan taba damuwa irin hakaba, kinsan mutuwar aure kamar mutuwa take inhar Allah yakawo karshensa dolene ayi hkr arabu to meye naki nadamuwa harda suma haba humaira namijin banza namijin wofi danki wulakanta fa yai mk haka to meyesa bazaki nuna masa ke macece jaruma ba?

Itadai humaira jinta kawai take don ta tafi tunanin khamal ma

Ashanty takulu ganin humairan batace komai ba wato ma aikin banza takeyi

Dama ko ada dasuka taba fada sosai akan khamal dinne alokacin data shiga damuwa don yace ta amince masa yakai iyayen nata kotu kosu rabu to ita Ashanty dataji fada tayi mata akan hakan sukai baran baran dakyar Zee ta shiryasu

Ashanty ta mike da fushi tace mata "zantafi tunda har bazakiji shawarata ba inyaso inkin kashe kanki nadawo na debi yaranki na rike mikisu dan inke bakya sonsu mu muna sonsu

Humaira tace "ya zakice bana son yarana walh ina musu sonda bana yiwa kowashi.

"Toko inhar hakane to inaso ki nuna hakan azakiri kiture tunanin khamal balle ki illata kanki kimaishesu marayu tunda shi ba sonsu yakeba.

Humaira ta goge wani hawaye daya kwanranyo mata me zafin gaske kan kuncinta

Tace da Ashanty "yanzu Ashanty ya zanyi knn da rayuwata?

Ashanty tace "hakuri da juriya.

"Bazan iya hakuri kwata kwata da khamal ba ina sonsa sosai walh.

Ashanty taja wani mugun tsaki tace "walh kuwa dakin rako mata duniya tunda shi baya sonki.ya gama gajiya dake da yaranki.

Humaira tace "kigane wani abu guda Ashanty khamal ba wai sona ne baya yiba.kawai haihuwarce baya so inringayi akufe akufe nikuma haka Allah yayini me kwanika yaki ganewa ne

Ashanty tace "to wannan kuma keya kamata kisamowa kanki mafita akansa tunda kinki karbar tawa

Humaira takama hannunta tace "dan Allah kada kiji haushina kada kema kigujeni banda kowa ayanzu aduniya..."saurara humaira kina da kowa tuntuni kinki ganewa ne iyayanki na raye amma kinyi saken da namiji yarabaku walh da zakiji shawarata dakin koma garesu kin nemi yafiyarsu kin zauna atare dasu domin samawa yaranki gata.

Humaira tace asanyaye "walh nasan bazasu taba karbata ba sungama fushi dani sun yafeni ga khamal kinmanta da harda yarjejeniya atsakaninmu kuma innakoma gunsu kinga kenan mungama rabuwa da khamal kenan nikuma bazan...

Ashanty takufula tace "ke kuma bazaki iya rabuwa dashi kwata kwata kamar yadda yarabu dakeba ko?to yayi kyau saiki nemi inda yake ki bishi maza mara zuciya.

Ashanty nagama fadin hakan tafuce tabarta tana kukan takaici

Kokusa hakan da khamal yayi mata baisa tayi nadamar son da take masa ba saima kaunarsa ce datakara ruruwa aranta taringa ayyana hakan atata kaddarar knn.

*****

Wasa wasa humaira na gidan tana zaune da yaranta Cikin zaman jiran dawowar khamal wanda wata guda kenan

Takira zee tace mata bata gari sunje semener Abuja

Haka Ashanty tayi fushi da ita

Zaman hakuri da maleji taringayi gashi hassana da husaina sunfara zuwa sch ga term yakusa karewa bata san ma yazatayi da kudi ba insun bukata na sch fees

Gashi bata taba gwada yin sana.a agidan ba gata dai da keken dinki amma babu wanda yasan ta iya dinki a unguwar balle akawo mata

Dayake tanada kayan abinci masu dan yawa

Sai abun baizo mata da zafiba saidai kawai yaji da take dakawa me yawa ko tayi yar stew dinta

Saida tayi wata biyu ahakan sannan taje gidansu ashanty taringa mata kuka wai ta taimaketa takira mata Ahmad tagaya masa yanemo mata khamal adawo musu da Auransu

Ashanty ta tausaya mata yanda taganta duk ta rame saikuma taji ta sauko daga fushin datayi da ita

Tace "humaira kinsaka kanki atasku indai da namiji ne akansa sai akiraki mahaukaciya indai bazakiyi so saffa saffaba

Humaira tace "kitayani da addu.a Ashanty haka tawa kaddarar take.

Ashanty tayi ruwa tayi tsaki awannan lamarin tasamu Ahmad da zancen wanda ran Ahmad din yai matuqar baci dajin hakan har yaringajin tausayin humairan

Da dabara yasan yanda yayi da Khamal suka hadu domin ayasanma zancen kenan da bazai yarda su haduba domin zamansu da Aleesha baby dinsa yadauko dadi agidanta yatare wanda sai yanda tayi dashi don asiri kawai yakeci a abinci baya darawa ko nan da can inya dawo dg aiki yana kashe mata kudi sosai
Chapter 15 · 0% Book details