← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cikin gidan ko a tsakar gida take ta daura kafa daya kan daya."Wakar Nura m Inuwa mai taken "manyan mata."take bi da saurare,Dan kwallinta takai shi har goshi @360 da daurin ture kaga tsiya."Chewing gum be abakinta tana ci."Gefenta Almajirai ne ke wanke-wanke da shara!" Bakowa ba ce sai saleema da tacika faam!"Tana jiran Aliyu da ta tanada wa shafukan masifa da rashin mutunci!"Ko ba komai yau tasamu sanadin yunwa!"Wanda tuni take Neman mafarin da zata samu mafakar da take nema domin ganin ta rabo da Aleeyu..."

"Har zasu kutsa kai cikin gidan sai Hafeez ya dawo da Aliyu dake gabansa baya a kunne ya rada masa magana ahankali...Wanda ni kaina bansan ko me yake fada ba..." sannan suka shiga da sallama daga ciki......"

****** *******

*Daga Alk'alamin*
*Nabila ( Maman Khalil*)
👇🏻

*In the memory of my late father Alhaji Hudu mai Agogo, may his soul rest in peace Amen*

Cikin yanayi na rashin jin dadi, Mufida ta karasa gida,dakin ta kawai ta nufa,da isarta ta fada kan katifar ta,ko mayafi bata iya cirewa ba,zafafan hawaye ne ke gangarowa daga cikin idanita,ita kanta ta rasa meye dalilin da yasanya zuciyarta ke azabtar da ita haka,akan abinda bata da tabbas akansa,lallai yau ta tabbatar wada kanta so masiface,so cuta ce,wadda indai ba Allah ne ya kiyaye ka daga sharrin taba ,zata iya halakar dakai,musamman ita da bata garantin da cewa a tata soyayar,

Kwalla Kiran maman ta taji kamar daga sama,tana fadi

"Mufida!!! Mufida!!!"

Dan haka ta tashi gamida goge hawayen fuskarta,sannan ta nufi inda ake kiran nata,zaune ta taddata bisa tabarma,da alamu kammala cin abincin daren ta kenan,dan ko kwanon abincin bata dauke ba daga gabanta,

Gefe ta samu ta zauna, gamida cewa

" mama gani"

Mahaifiyar tata ce ta dubeta,sannan tace

"Kobaki fada min kina cikin damua ba,ni nasan hakan dan kuwa fiskarki tuni ta baiyanar da abinda ke zuciyarki,dan hk fadan meke damunki,"

Itadai Mufida bata iya cemata komai ba ,tadai sudda kanta kasa kawai,

Toh tunda dai bazaki fadan komai ba tashi ki tafi,Allah yayi mana maganin komai,amma ki sani honorable yana nan akan batunsa na naiman aurenki,km kinga nidai banga kina sauraron kowa ba,km a matsayinsa na dan yayana bazan taba cewa ban amince dashi ba.

Koda kuwa taji an ambaci sunan Honourable,dan danan ta dawo cikin tunanin ta,dan kuwa tasan mama bada wasa take ba zata iya sawa a daura mata aure dashi,dan kuwa tana matukar kaunarsa,akullum cikin yabon kyawawan halayensa take

"Dan Allah mama kibar wannan maganar dan ni wlh inada Wanda yake sona kuma nake kaunar sa,ki karayin hakuri zuwa dan wani lokaci kadan dazarar ya dawo gari ina tabbatar miki zaizo har gidannan ku gaisa ,dan kitabbatar bada wasa nake ba"

Mama ce ta bata amsa da cewa

"Zuwa yaushe zai dawo din? Dan nagaji da kananan maganganun da suke zuwa min kunne a unguwar nan akanki,sanin kanki ne ina kaunar ki,kasan cewar banda wani tamkarki,kinga kuwa bazan zuba idanu ana jifanki da muggan kalamai

Cikin sanyin zuciya Mufida tace

" ba dadewa zaiba mama ayadda ya fada min, sadai kinsan ita tafi kankayita kake da kanka

Da wadannan magan ganun Mufida ta shawo kan maman nata harta samu ta sakko akan batun Honorable

Washegari misalin goma na safe,Mufida ta dira gidan su kawar ta Alawiyya,dan dorawa daga inda suka tsaya,ay kuwa ita kanta Alawiyyar bata wata wata ba ta kammala dukkanin ayyukan ta na gida ,saa'nnan suka tsunduma cikin social network,

Sun kusa kimanin awanni biyu ,amma ba labari,dan hk dukka ninsu jikinsu yayi sanyi dan sun gama tabbatar wada kansu rashin nasara

Ana haka hoton DG Anas cikin kayan sarki na hukumar hana fasa kwauri ya bayyana baro baro akan wayar Mufida,fiskar shi cike da annuri ,kasan cewar ya fadada ta da murmushi ,kyansa ya baiyyana afili,sajen fiskarshi Wanda yayi iyaka da kunnen sa luf luf kamar wani balarabe,saannan gashin bakinsa madai daici ya dace da yanayin kyan halittarsa.

Gaban Mufida ne yayi wani mugun faduwa koda tai arba dashi,abinka da masoyi,a sandare take nunawa Alawiyya shi amma bakinta ya kasa furta komai,mamaki ne ya ishi kawar tata,ganin irin mutumin da kawar tata ta dauko musu,tabbas tasan duk karam baninta ba zata taba lakato irin DG Anas ba dan kwata kwata yadin ba kalar zaren bace

Duban Mufida tayi tace"

Kawata yanzu kina nufin akan mutumin nan kike zubda hayayenki?shin ko baki kalli mukamin dake kafadar shi bane ? DG nefa, daga shugaba kwata kwata sai irinsa a mukami,pls idan mafarki kike ki farka ,ay Sam ban zaci burin naki yakai har hakaba,irin wadannan ina ma kasan inda zaka samusu,suda tsadar gani suke,idan gidane ga security nan,like wise office, dan Allah ki sake shawara"

Cikin karfin hali Mufida ta dubi kawar tata,kana tace

"Yes duk abinda kika fada ban miki musuba Alawiyya, amma karki manta abu guda,shi so ba ruwansa da girma ko matsayi,km wannan alamari da kike gani bayin kaina bane zuciya tace,dan hk karfafa min giwa zaki sabanin karyarmin da ita

.......... Muje zuwa
[7/5, 5:36 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Page* 0⃣7⃣

*Alk'alamin Maman Khaleel*🖋

👇🏻

*In the memory of my late father (Alhaji Hudu mai agogo)may his gentle soul rest in peace Amen👏🏼.*

Misalin karfe goma sha daya na safe Mufida ta sauka daga keke nape daidai office din custom dake kan titin hanyar zuwa zaria,hijab ne mai ruawan shudi har kusan kasa yake ja mata ta sanya, hannunta rike da wayarta,shigar ta dai tayi sosai dan kana ganinta kaga kamammiyar mace,kai tsaye gate din ta nufa ,xuciyarta kodar babu balle km kunya,

Sallama tayiwa wadansu officers guda biyu data gani zaune bakin gate din,cikin mutunci suka km bata amsa,ganin yadda sukaga kamun kanta

"Dan Allah tambaya nake"

Cewar mufida,daya daga cikinsu yace

"Allah yasa mun sani yan mata".

Murmushi kawai tai ,jin yace mata yan mata,

Dan Allah office din Oga Anas nake nema ,dan an cemin anan yake aiki,"

"Oga Anas km ?"

Dukkannin su suka ambata,daya daga cikin su yace

"gaskiya baiwar Allah duk office din nan bamai wannan sunan,daga manyan mu har xuwa ga kananan mu, amma ke waya fada miki anan yake aiki?"

Tambayar da yayi mata sam bata razanar da itaba,kasan cewar dama tun kanta fito ta shiryawa dukkanin wata tambayar da zaa iya jefo mata.

Mufida ta bashi amsa da cewa

"Mijina kamin Allah yayi mai rasuwa shima maikacin custom ne kamarku,amma shi ba wani babba bane,oga Anas shine a matsayin ubangidan sa ,kasan cewar ya mana komai na hallaci a rayuwa,baa' Kaduna nake da zamaba ziyara ce ta kawoni,shine na biyo in masa godia akan dawayyinar da yayi damu bayan rasuwar maigidana,kun oga Anas din ma a hoto ".

Mufida tai gagawar Nuna musu hoton nasane badan komai ba sai dan ,kada suyi sauri katseta da tambayar yasunan mijin nata km a ina yake aiki?.

Kodata nuna musu hotansa,tuni daya daga cikin su ya ganeshi,cewa yake

" ahh dan aljanna kenan ,ay wannan mutumin abinda yafi haka ma zai iya yi miki shi,yana da mutunci sosai ga saukin kai,na taba zama waje daya dashi ,ammafa shekarun akwai yawa,but yanxu dai bansan inda yake aiki ba,da dai nasan a abuja yake amma bari in shiga in tambayan miki wani abokin aikinmu inji, "

Bayan mintina kadan ne sai gashi ya dawo,nan yake tabbatar mata da cewa an tabbatar masa da cewa yanxu haka a Lagos yake aiki a kuma ellan container,dan haka idan taga zata iya zuwa canne toh?

Cikin karfin hali mufida tai masa godia sosai gamida taimakon ta da yayi,amma Sam zuciyarta ta kadu matuka dajin ance a Lagos yake aiki,kasan cewar basu da wani dan uwa ko aminai da zata jingina karyarta akansa wajen mahaifiyarta dan zame mata sanadin zuwa Lagos,tana tsaka da wannan tunanin ne,dayan officern ya taba abokin nasa hade da cewa

"Amma da gani mutumin nan ya tara dukiya ko? Dan naji ka ambaci ellan container gidan kudi kenan,nan ya bashi amsa da cewa

" hummm kai dai bari abokina,ko a sanin da danai wa mutumin nan millionaire ne na ajin farko ,ya tara kazaman kudi abokina,dan najima fa ana fadin wai yar kasar Sudan ma ya aura,wadanda suka samu zuwa dinner din bikin ma sunce tsabar kyau agum matar sa yadda kasan ita tai kanta, an kuwa yi watsi da dollars kamar banza"

shi kuwa Wanda ake va labarin jinjina kai kawai yake tsabar mamaki,koda mufida taji wadannan hirar da suke,tuni taji zuciyarta kamar ta fito ta fashe tsabar kishi,jitai gaba daya ta tsani matar tashi,dan ita gani take ba wani kyan da zata nuna mata sai dai hasken fata,dan hk ta kuduri a niyar kota halin kaka sai taje garin Lagos dan mallake zuciyar masoyinta.

Mufida ta sanar wada Alawiyya duk yadda sukai da officers dinnan, dan haka ma ta bukaceta data bata shawara kan yadda zata billowa wa tafiya zuwa Lagos,

Tunani mai zurfi Alawiyya ta shiga yi nadan wasu lokuta,kasan cewar yadda zaa billowa alamarin yanada girama sosai,cikin murmushi Alawiyya ta dafa kawar tata sannan ta dubeta tace

"na samo mana mafita kawata,km na tabbatar da zarar kika fadawa mama da sauri zata amimce da bukatar ki,"

Cike da zumudin jin mafitar da aka samu mufida tace

"Dan haka nake son shawara dake kawata,fadamin pls da sauri ina sauraranki

Don jin ko wace mafita Alawiyya ta samo musu?Ku kasance dani awani shafin don cigaban labarin......

****** *******

*ALqalamin 'Yar mutan Dikkawa*
*Nabeela Dikko*🖋

*RAMADAN🌙* Begins 5th or 6th,May 2019,In shaa Allah,The prophet Muhammad (S.A.W)Said:"Who ever Informed the others the day of RAMADAN the hell fire, Is HARAM for his/her,I have Done mine,So my brothers and Sisters please! and please! Pass the information to Muslims Ummah."

And its part of the Sunnah to ask forgivess from everyone before the Holy month of Ramadan so please forgive me If i have wronged you knowingly or unknowingly Ramadan kareen in advance.

Don't forget 8 things
SAHOOR,SOLAH,QUR'AN,DU'AH,SODAQAH,HELP OUT,IFTAR,TARAWEEH, AND REPEAT!!!!

_______________________

"Salamu Alaiku....Assalamu Alaikum... Aleeyu ya CE "A karou na biyu!....Amun wala'alaiku salamu...Lado Almajiri ya ce tare da fadin Malam sannu da dawowa.''

"Yawwa Lado,sannunku...Aliyu yace lokacin yana gaba Hafeez na biye bayan sa."
Chapter 13 · 0% Book details