← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi tayi da sauri Bilal ya rik'o hannunta yana fad'in wallahi Umma zan fad'a maki dawo ki zauna. Zama tayi tana fad'in ina jinka.....

****** ******

Kinaji ko Hibbah, wannan shine wanda zaki rik'a sha da madara, wannan kuma wanka zakiyi dashi, sai wannan wanda zaki rik'a turara jikinki dashi. Jinjina kai Hibbah tayi tace Umma Allah yasa wannan nashan bai da d'aci. Umma tace ko yana da d'aci dole kisha, kinsan dai kud'i na kashe akan wannan magungunan, damma Lami tana ganin girmana shiyasa ta rage mani.

Hbbah tace amma Umma banji kince akwai wanda zan rik'a matsi dashi dan ya k'ara matse ni ba. Sakin baki Umma tayi tana kallon Hibbah jin abinda tace. Hannu ta kai ta mangare mata baki tana fad'in kinci Uwaki, a gidan uban wa kika san maganin matse mace? Rik'e baki Hibba tayi tana fad'in Allah Umma wata k'awatace mukaje gidansu shine take fad'a mani abubuwan da zanyi amfani dasu.

Umma tace amma 'yar iska ce ko? Idan ba 'yar iska ba tana budurwa ace tasan wani maganin matse mace, to meya had'aki dashi bayan amatse kike, kodai kina wasan banza da maza ban sani ba? Da sauri Hibbah tashiga girgiza kai. Umma tace to bana son na sake jin irin wannan maganar abakin ki, ko wacece zatayi maki maganar maganin mata ki nuna baki san komai ba, haka zakije gidan mijin kirik'a nuna mashi kinsan wani abu game da aure, ina mai tabbatar maki duk macen da take budurwa aka kaita gidan miji tarik'a nuna tasan wani abu sai mijin yaji ta rage daraja awajenshi, kome zai fad'a ki nuna baki tab'a sani ba koda kin sani a film ko a rubuce, domin masu rubutawar suna rubutawa ne saboda matan aure ba 'yan mata ba.

Hibbah tace kiyi hak'uri bazan sake ba. Umma tace shikenan tashi kije kisiyo madara daga yau nake son ki fara sha. Hibbah tace Umma na manta Mufty yace gobe Kawunsa zasu kawo kayan sa rana.

Umma tace ikon Allah, aiko bari Malan yashigo na fad'a mashi ya kawo kud'i ayi masu girki. Hibbah tace Umma dan Allah kada asa jan nama asiyo kaji kinsan fa 'yan gayu ne. Umma tace dole ma kuwa, ai dole asiyo kaji kada su raina mu. Kira mani waccan jakar na aiketa kasuwa kafin Malan d'in ya dawo gara taje tasiyo kajin da kud'in hannuna afara gyarawa.

Juyawa Hibbah tayi tana kwalama Hamrah kira. Hamrah tana zaune tana linke kayanta tajiyo muryar Hibbah, da sauri ta fito tana fad'in gani. Yamutsa fuska Hibbah tayi tana fad'in kasuwa Umma zata aike ki abinda kika tsana. Da kallo Hamrah ta bita tana jin wani bakin ciki, ta tsani zuwa kasuwa arayuwarta, sanin hakan yasa Umma koda yaushe take aikenta koda abun da za'a siyo baida yawa.

Bayan ta gaishe da Umma tace gani. 'Daure fuska tayi ta wurgo mata dubu biyu tana fad'in kije kasuwa kisiyo mani kajin hausa guda biyu na d'ari bakwai-bakwai, d'ayar abaki k'arama ta d'ari shidda idan kuma zasu siyar ahakan su baki ukku, ga d'ari nan ki hau adedeta ki maido mani canjin ashirin.

Duk'awa Hamrah tayi ta d'auki kudin tana fad'in to, fita tayi tana share idonta. Hijabinta kawai ta d'auko ta fito, kai tsaye bakin titi ta nufa ta hau adedeta, da kyar yace zai kaita a naira arba'in.

Haka ta kutsa cikin kasuwar har wajen masu saida kaji, sai da ta kammala ciniki aka d'aure mata kaji tazo d'auko kud'i sukace d'aukarni inda kika aje, dama a hannu ta rik'esu dan ita bata son d'aukar jaka, babu komai a hannunta sai canjin sittin. Nan take taji gabanta ya faad'i wata irin zufa ta keto mata. Kallon mai kajin tayi tace malan kayi hak'uri na zubar da kud'in, ko kuma kila a gida na baro su. Aje kajin yayi yana fad'in shikenan kije ki duba Allah ya kyauta gaba. Haka ta fito kasuwar jikinta a sanyaye ta nufi gida cike da fargabar abinda zata iske........

Muje zuwa...
[7/5, 5:38 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Page* 1⃣0⃣

*Rubutawa Nabila( maman kalil)*
👇🏻

_In the memory of my late father Alhaji Hudu mai agogo my his gentle soul rest in peace Amen_

Cikin yanayi na karfin halil mama tace mata

"lafia?"

"Ba komai kaina ne yake dan min ciwo" ta bata amsa",toh Allah ya sauwake "cewar mama,har bayan da suka koma gida wunin ranar mufida bata daina tunanin abinda idanunta suka gane mata ba,babban abin dayafi daga mata hankali bai wuce irin zubin da Allah taga yayi wa safara,tabbas lallai ta taro wa kanta match, gaban mudubin dakinta ta nufa ,sannan ta karewa kanta kallo tsaf,takuma yi amanna cewa itama fa ba baya ba,dan tanada nata kyau din daidai gwargwado dan kuya haske da murjewar fata kawai zata nuna mata,tana daga tsaye ta fada kan lallausan katifarta hade da jan wani dogon tsaki tana fadin

" wlh duk kinibibinki ni nan na isheki,sai dai kawai ni nunamin ke mai kudice kuma wannan ma wuyarta ban shiga gidan ba nima zanyi,fatata ma ta murje nayi luwai² dani, gashin jikina ma duk su kwakwanta"nan dai taita sambatunta ita kadai,sai daga bisani ta bushe da wata siririyar dari, wayarta ta dakko cikin wata yar karamar jaka saannan ta lalatsa wasu lambobi,jim kadan daga daya bangaren aka daga,ba wata bace illah kawarta Alawiyya, nan ta kwashe dukkanin labarin abinda ya wakana ta shaida mata,sai ananne Alawiyyar ta sakko daga fushin da take da ita, jin takawo mata kakarfan uzuri,nan Alawiyya take shaida mata wannan mgnar tasu bata waya bace kamata yayi su hadu su tattauna yadda zasu fillo wa lamari,Dan haka ita zata shigo gidan anjima da yamma daga nanma saita duba mama da bata da lafiya.

Wajen misalin karfe 5 da rabi na yammane Alawiyya ta iso gidansu kawar tata amma ga mamakin ta isketa waje sunata fira da honourable,abin yada daure mata kai amma kawai ta basar ta karasa suka gaisa dashi sannan ta shige cikin gida dan duba lafiyar mama,shigarta baifi mintina goma ba saiga mufida ta biyo bayanta,dakinta ta isketa kwance kan katifa tanata yan latselatsenta a wayarta,koda ganinta ta shigo ne yasa ta tashi zaune gamida binta da kallo mai cike da tambayoyi,dariya mufida ta fashe dashi tana fadin.

"Daman nasan zaa rina, irin wannan kallon tuhuma haka?to kwantar da hankalinki ba abinda kike tunani bane,yaji labarin mama bata da lafiyane yazo dubata,kawai sai naji yana bama mama shawara akan taje taga wata babbar likita a asibintin dutse,ta kware sosai akan harkarta kuma komai nata kyutane ,kuma indai ta shirya zuwa zai mata hanyar da zaisa ta dubata cikin sauki batareda tabi wannan dogon layinba,to jin hakanne yasa nabishi waje naketa bugar cikinsa dan yadan fadamin abinda yasani dangane da ita da mijin tana,au mijin namu "

Nan Alawiyya ta fashe mata da daria jin tace "mijin namu,"

Mufida tadan daure fiska sannan tace

"To karya nayi?zakisha mamaki kwanan nan, yayinda kika wayi gari kikaga na kerewa saa'"

Nan suka tafa hannunsu gaba daya

Alawiyya ce tace mata

"To km kin sami abinda kike bukata a wajen nasa?"

A ta bata amsa dashi sannan ta cigaba da cewa

"Ayadda yake fadamin ma yanxu haka gogan nawa yana gari ma,dan ko jiya daya shiga dubiyar marasa lafiya ya gansu tare dashi,dan har dakin duba marasa lafiyan ya rakata ,ya kuma dade a wajen,ya bani labarin irin karamcin sa saukin kansa ga taimako da tausayawa, to jin hakane ma yasa nace masa yasa ayi mana hanyar ganin nata gobe,gudun kar ya subuce wa haduwarmu, walahi kawata wannan dan takaitacen bayanin da yayi min na dada gamsar da kaina da nasami mijin aure, kuma hakan ya karfafa min gwiwata wajen in gagauta tunkarar sa da kudirina,inajin a jikina bazai ki amsa gayyata taba"

"Wannan dabarar taki tayi kawata,ta wajen gagauta haduwar taku,to kuma idan kun hadun keda ita ta meye next plan dinki?

To koma menene kubiyo maman kalil dan jin cigaban labarin......

******* *****

*Alk'alamin Nabeela Dikko* ✍🏻

👇🏻

_*Congrats on ur passing exams Sis Yaseerah Dikko Allah ya albarkachi rayuwarki da karatun ki Ameen*_ 🥰

"Hello!Hafez kana jina network din yana rawa!"

"Eh ina jinka!"Inji Hafeez."

"Yawwa kadai jii yadda duk al'amurran suka kasance, tsakanina da saleema da kuma Baba!"Yanzu na yanke shawarar zanbi maganar da ka fada min a kwanakin baya!"Kuma zanyi aiki da ita!"

"Ok!Yanzu nagane, shi ne dalilin sakinta har uku!Sam bai kamata ba, nasan cewa saleema ta cancanci ahukunta ta,amma bata wannan fuskar ba! Ko aure kayi Aleeyu ita kuma ka umurci takoma gidan su na wani lokaci,Idan ta zauna zaman gida,ai tayi laushi daga baya ka maidota gidanka!Ni horata naso kayi horo mai tsanani!Saboda rashin mutuncinta!Amma ka riga da ka tafka kuskure Dan Allah kada ka kara dabi'ar saki!batada kyau!"

"Haabaa!Hafeez bai kamata ace ka kasa yimin uzuri bah!"

"Kasan Halayen saleema sarai!ta nuna ma kuma tayi min rashin kunya agaban idonka!"Sann........!"

"Dakatah Aliyu....Duk nasan hakan amma bai kamata ka tsinke igoyoyin aurenku dukaa ba!"Hafeez yace adayan bangaren ran shi ba dadi tamkar yayi fira daga Sudan yadawo Nigeria ya hukunta abokin nasa Aliyu yakeji!"

"To naji Abdoul Hafeez nagode kuma in shaa Allah bazan qara makamancin hakan ba!"

"Yawwa Abokina nasan kaddara ce da bacin zuciya! fatana Allah ya musanya maka da mafi alheri,Kaji Aleeyu!"

Ameen Hafeez nagode ka gaida min da madam Nazeera da yarona da kuma Ammi."

"Duk zasuji na fito office da na baka su, dazu nakira Academic Sectary na University dinmu yace nan zuwa jibi zai kammala process din result dinka anyi clearing din komai."Kaga wani sati zan shigo Nigeria a hada duk document din muyi submit a company din."

"Alhamdulillah!Nagode Hafeez Allah yabar zumunci ya saka maka da alher....."

"Kai yi mun shiru...!banson iskanci ai yiwa kaine, ba godiya atsakanin mu Aleeyuna sai an juma!Hafeez ya ce tare da datse kiran."Laptop dinsa ya cigaba da dannawa acikin katafaren office din sa."

"Aleeyu ko screen din wayarsa ya cigaba da kallo yana murmushi, Abokinsa bayason yaji yana yawan gode masa,Ko meyasa!?Hmnnnn, bakomai zai cigaba da masa addu'ah."Toilet ya fada domin yin wanka yaje gidansu yaji inda batu ya tsaya!"
Chapter 21 · 0% Book details