← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Garba yace amma ka tabbata dai ba auren dole zakayi mata ba ko? Malan Bukar yace Allah ya kyauta nayi ma 'Diyata auren dole, kasan halin Hamrah, irin halin mahaifiyarta gareta, tana tsoron samarin zamanin nan, gashi Yayarta ta samu mijin aure, da nayi mata magana akan ta fiddo miji a had'asu sai tace ita bata tsayawa da kowa, kawai ta bani dama na zab'a mata duk wanda naji ya kwanta mani dan tana tsoron tayi zab'on tumin dare.

Alhaji ganin yanda muka dad'e da kai, kuma nasan cewar matarka d'aya gashi ba wasu yara kake dasu da yawa ba, sannan baka wuce k'ara aure ba hakan yasa nayi tunanin na baka d'iyata, nasan ko bayan raina bazaka tab'a wulak'anta mani ita ba, wannan dalilin ne yasa nace na baka aurenta.

Alhaji Garba yace ni kuma gani nake kamar sayenta nayi tunda kamar biyan bashi ne kayi da ita, tunda ka bani ita ni kuma nace tunda ka bani auren d'iyarka shikenan kabar kud'in dana baka, haka kawai zuciyata ta kasa amincewa da abinda nayi, sai nake ganin kamar musanya mukayi.

Jikin Malan Bukar ne yayi sanyi jin Alhaji yana so ya maido magana baya, kallonshi yayi yana fad'in haba Alhaji, wallahi ko baka bina kud'i ni mai iya maka kyautar d'iya ne, ai kayi mani komai. Kuka yasa yana fad'in dan Allah Alhaji ka daina wannan maganar, d'iyata d'iyarka ce na yarda da kai wallahi.

Alhaji Garba yace shikenan na amince da hakan, Allah yayi mana jagora, amma bana so ka fad'ama kowa cewar kud'i na baka bashi da ka bani auren d'iyarka na yafe maka kud'in. Malan Bukar yace wallahi bazan fad'a ba, nagode sosai. Tashi yayi gudun kada Alhaji ya sake kawo wata maganar yayi masa sallama ya tafi yana sauke ajiyar zuciya........
[7/5, 5:36 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Page* 0⃣6⃣

*Alk'alamin🖋*
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
( *Nabeelert Lady*)
👇🏻

Zaune Malan Bukar yake a d'akinshi Kubra tana gefe ya gama fad'a mata yanda sukayi da Alhaji Garba. Kubra tace lallai wannan mutumin da basira yake, Malan sai fa kayi ahankali kada ya harbo jirgin mu, dole sai ka tsawatar ma Hamrah domin kada yazo tayi wani abu da zai nuna dole akayi mata, idan ya gano haka ina mai tabbatar maka bazai aureta ba, kuma dole ka biyashi kud'inshi daga ranar kuma girmanka ya zube awajenshi.

Malan Bukar yace aiko idan har tayi wani abu dayasa Alhaji ya gano gaskiyar lamarin zata fuskanci hukunci mai tsanani, dan haka kije ki kira mani ita dan gobe ne zai zo su gaisa.

Tashi Kubra tayi tana fad'in gara dai kaja mata kunne. Tana fita tashiga d'akin Hamrah tana fad'in to sarkin munafurci sai kifito Ubanki yana kira, makira kullum kina cikin d'aki salon wani yazo yace muna kuntata maki.

Tashi Hamrah tayi ta biyo bayan Kubra. Tana shiga ta zauna tana fad'in sannu da hutawa Baba. Malan Bukar yace me kikeyi ad'aki salan wani yace akwai abinda akayi maki, wallahi Hamrah kishiga hankalin ki dani, naga alamar kina so ki bani kunya ko? Kai Hamrah ta girgiza tana hawaye.

Malan Bukar yace emana, gashi tunda nayi maki maganar aure kike fushi dani, ashe Hamrah amatsayina na mahaifinki bazan iya neman alfarma awajenki ba? Nayi d'awainiya dake tun kina k'arama dan kawai yau kin girma na nemi alfarma awajenki shine kike fushi dani? Shikenan, tunda bazan iya alfahari da abinda na haifa ba kije, zanje na bama Alhaji hak'uri ko kuma shi mijin Hibbah ya hak'ura sai ita ta auri Alhajin kinga bazanji kunya ba.

Kuka Hamrah tasa ta rik'e k'afar Malan Bukar tana fad'in dan Allah Baba kayi hak'uri, wallahi ba fushi nake da kai ba, na amince da zab'in ka, kome kake so wallahi zanyi makashi, kuma bazan tab'a nuna damuwa ta akan haka ba dan Allah kada kayi fushi dani.

Murmushi Malan Bukar yayi yana fad'in idan har kinaso na saka maki albarka sai Alhaji yazo kin amshe shi da hannu biyu, angama hidimar biki lafiya baki nuna ma 'yan uwanki komai ba sannan zanji dad'i. Hamrah tace zanyi, wallahi zanyi kome kace, fatana kada kayi fushi dani, ka sa mani albarka kamar kowa Baba.

Kubra tace tunda tayi nadama ayi mata hak'uri Malan bazata sake ba, kasan hada yarinta ke damunta. Malan Bukar yace tunda kinsa baki shikenan, kitashi kije, gobe Alhaji zezo dan ku gaisa, zansa Hibbah ta kula dake, idan kikayi wani abu wallahi ranki saiya b'aci, ki saki jiki dashi, kome kike so ki fad'a mashi domin shine zeyi maki komai kinsan banda kud'i.

Hamrah tace nagode Baba. Tashi tayi tana goge hawaye... Dariya Kubra tayi tana fad'in wallahi Malan ka iya had'a shiri, nasan idan Alhaji yaga Hamrah ta saki jiki dashi komai shine zeyi maka na biki. Malan Bukar yace nafiki sanin waye Alhaji Garba, yana da kirki sosai, ni dai tunda naci million d'aya suje can su k'arata.

****

Zaune Hibbah take a cikin motar Muftahu sai shagwab'a take masa akan ya kaita taga gidan da zai saka ta. Murmushi Muftahu yayi yace haba Baby me kike ci na baka na zuba, saura kwana nawa akai ki gidan gaba d'aya ma, yanzu akwai wasu gyare-gyare da akeyi ki bari agama komai sannan, ko jerenki ma bada wuri za' akai ba, ana saura kwana d'aya biki zan aiko da mota sai ta kwashi kayan akai, idan yaso bayan an d'aura aure sai wasu daga cikin 'yan uwanki suje su k'ara gyara maki gidan, dan kayan gadon ki maza ne zasu had'asu bana so mata su had'a asamu matsala.

Murmushi tayi tana fad'in shiyasa nake k'ara sonka, kasan abinda zai k'ayatar dani, bakomai ai dai bikin ya kusa, idan aka kaini zanga gidan kawai. Muftahu yace yauwa koke fa. Hibbah tace amma dai alk'awarin mu yana nan ko? Muftahu yace name fa? Hibbah tace na kishiya mana, kasan kayi mani alk'awarin bazaka tab'a yi mani kishiya ba.

Murmushi Muftahu yayi yana fad'in a tsarin gidana babu wajen da mace biyu zasu zauna, komai na mace d'aya ne, dan haka ki kwantar da hankalin ki Muftahu mijin mace d'aya ne, domin a tsarina babu auren mace sama da d'aya. Hibbah tace nagode sosai.

Agogon hannunshi ya kalla yana fad'in bara nazo na tafi akwai wasu kaya da za'a kawo mani daga abuja nasan sun kusa k'arasowa. Hibbah tase amma sai yaushe za'a +awo hefe kaga lokaci yana k'urewa saboda d'inki? Luftahu yace yauwa kin ma tuna mani, babban dalilin zuwana wajenki yau kenan, nazo na amshi awonki dommn a d'knke�nake so akawo maki su b!na so kiyi mani d'ilkin da bana so
! ina da(tela cawai ki bani awonki na kah mashi< s!nnan baza'a kawo lefen ba`sai an! saura kwana ukku biKi( kuma gaskiya bq dukA jan kawoba nesan halin dangin mati suna iqa kwashe mak).

Hibb`h tace kamar0ka sani, $nama ina �in haushin"kayan lefen da ake!kwashe ma amarya, kawai kakawo mani wad'an da zanyy amafani dasu s!i"'yan k!`'an kada ace ba'a kawo lefe ba. Muftahu yace kada ki damu kiyi ma Umma bayani(nasan zatace ayi haka. Hibbe uace zan turo maka awOn ta messagd* Muftaht y`ce nagode {k gaishe da Tm}a.


Fita Hibbah taYi cike da farin ciki tayh gida. Murmushi Muftaiu!ya saki yana sHafa kanshi ia$tada mouc ya tafi....

*** ***

👇🏹
*AlQalamin Labi|ancy Lur* 💘 (�untyn S&S) 🖎

Sosai humkira taringa fargaba tana addua akan samun cikin nan nata domin tasan shikenan karshen zaman lfyrsu da khamal yazo dole ne tashiga tashin hankali domin tana matuqar son khamal bata qaunar duk abinda zai rabasu yakawo musu rashin jituwa

Taci alwashin wannan karon bazata taba gayawa kawayenta wannan damuwar tata ba ballantana zee da zata zugata akansa garama Ashanty bata goyon bayan tayiwa Khamal tijara tasan kuma inhar taji tanada ciki awannan karon laifinta zata gani sosai bazata yarda da ba planning tayiba tunda ba taba auren tai ba kuma bazata gane cewar ana iya samun ciki inkana planning dinba sbd ba.a yiwa Allah wayo ga qudirarsa ya zartas

Ranar wata lahadi yana gida Bai futa ba yana hutawa afalo yana kan 3 siter akwance yakunna TV amma ba kallon yakeba sai chart da babynsa kawai yakeyi Amal tana kwance a 2siter tana bacci ummanta na kicin taje kawo abinci

Humaira tadawo falon da kayan abinci a ahannunta ta dire akan table taje takawo ruwa ajug ta dire duk tana kallon yadda khamal din keta murmushi yana ckn nishadi ya luntsuma a chart tamkar ma baisan tazo gun ba

Tayi karfin halin warce wayar domin kishi kecinta arai

Ya tashi zaune yakalleta fuska ba fara.a yace "miko min wayata kafin ranki yabaci.

Ckn kishi ido rufe tace masa "saika gayamin da wace kake waya haka kashiga nishadi ka mance da matarka.

Yace mata "wacce ke sona ce maza bani waya kada inbata mk rai abaza.

Ta mika masa asanyaye tace "gashi amma gaskiya abani lokacina inko ba hakaba walh ince ban yafe ba.

Ya karbi wayar yakashe datar ya ajiye agefe yazuba mata idanu yana fadin "to,sarkin yan kishin tsiya zubomin abinci ni inci .

Bata kara ce ms uffan ba ta duka kawai tabude plask din ta hau xuba masa abincin

Saida yaci ya koshi sannan yazuba mata idanu yace "madam naga fa akwana kinnan kinyi wani freash na lafiyane kuwa?

Taji wani faduwar gaba haka kawai tace masa "Lfy qalau idon ka ne amma ba wani freash

Ya turar da abubuwan gabansa kana yace "banyarda dakeba humaira anyi biyu nakwana ackn wannan karan bazan kyale kiba inhar kk muna furceni don haka ki gayamin tsakaninki da Allah ciki ne dake ko?

Tayi wani -wiki kana tace "haba Abban twins ya kake jamin wannan Batu haka nikam banda komai.

ya mike tsaye yana fadin "koma dai meye ina zuwa .

Tabishi da kallo Tana tunani aranta to wannan ina zashi me yake nufi?

Tananan Zaune har mintina kusan 15 saican taji dawowar sa itada metron Zulaihat wata likita dasuke makwabtaka akan layinsu

Suka gaisa a mutunce
Da metron

Khamal yadubi metron zulaihat yace "metron fito da abin awo ki aunata mugani
Chapter 11 · 0% Book details