← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mansur yace baka da kirki Mufty, to yanzu ina zaka aje amaryar tunda naga babu d'aki agidan ka? Mufty yace haya zan kama mata mana, kafin mu gama cin amarcin mu na gyara inda zan maida ta.

Dariya suka sa gaba d'aya. Mansur yace akwai abinda yake bani mamaki da kai, da farko K'anwar Hibbah ka fara nema, kawai daga sama naga abun ya juye, yanzu kai baka jin kunyar Hamrah? Saurin dafe kai Muftahu yayi jin an kira sunan Hamrah, saurin tashi yayi yana fad'in tashi muje bana buk'atar jin wannan maganar.

Cike da mamaki Mansur yake kallon Muftahu ganin yanda ya birkice daga yin maganar Hamrah. Ko saurarenshi Muftahu beyi ba ya wuce mota yana dafe kai. Jiki a sanyaye Mansur yabi bayanshi yana tunanin dalilin da yasa abokinsa shiga wannan yanayin, amma koma menene zai bincika.....

***** *****

*Rubutawa Nabila (maman kalil)*👐🏼
👇🏻
*in d memory of my late father Alhaji Hudu mai agogo mai his soul rest in peace da'iman Amen.*

Fiska cike da annashuwa,Alawiyya ta kalli kawar tata saa'nnan tace,

"Shawarar fa dadan wuya kawata ,anya kuwa zaayi hkan,"?

Mufida tace

"Nidai fadamin dan Allah dan wlh na kagu da inji shawarar nan taki,"

Alawiyya ta nisa,saa'nnan tace

"Kiga dai baki da kowa garin Lagos nima km haka,asalima bamusan hanyar taba sai a' labari ,dan haka abinda zamu shirya kawai kidnapping dinki akayi,kinga ni kuma daga nan zan shirya duk yadda zaayi wajen kiranata ,dan wayata xansa a muryar maza muyita waya da ita ahaka, hade da jan lokaci,dan baxan ma bukaci aban kudi ba har sai na tabbatar da cewa kin kammala dukkan abinda ya kaiki Lagos, idan yaso bayan kin dawo sai ki nuna mata wanine a gidan ya taimaka miki kika su'buto daga wajensu,koya kika gani?"

Jikin mufida ne yayi sanyi,saa'nnan tai zugum tana nazarin wannan alamari,kasan cewa zata saka mahaifiyarta cikin tashin hankali ,dan tason yarda take kaunarta matuka da gaske,hakanne ma yasa bata barinta tayi koda doguwar tafine,

Amma ace daya bangaren na zuciyarta raya mata yake,kawai taje, dan abune na kankanin lokaci watakil ma baifi tai kwana uku ba ta juyo,saa'nnan km idan ta dace da samun soyayyarsa irin daular da zata Shiga,itama ta shiga cikin jerin mata masu aji ,kima da mutunci a idon jamaa'.

Tana cikin wanana dogon naxarin ne Alawiyya ta dafa kafadarta saa'nnan tace

"Tabbas nikaina nasa alamarin da girma yake ,dan hakalin kowa ne sai ya tashi,amma fa bamuda xabi dan aganina wannan ita kadai ce mafita nidai a wajena,idan km kinda wata shawarar wadda tafi wannan to sai abita"

Ajiyar zuciya Mufida tace sannan ta dubi Alawiyya tace

"Kidan bani lokaci kadan zanyi shawara akan wannan maganar,inhar bani da way out to tabbas wannan shawarar taki zanbi,alabashi idan komai ya kankama duk Wanda na batama wa zan bishi da alkairi daya bayan daya".

Tana gama fadin haka gaba dayansu suka bushe da dariya,har sai da maman Alawiyya ta lekosu tana tambayar su da lafiya? Nan dai suka wayance da cewa bakomai.

Kusan kwana 2 kenan da waccan maganar ,ama Mufida ta kasa yanke hukunci,ta rasa yadda zata billo wa alamarin gaba daya,data yanke hukunci fadama Alawiyya ta amince,gaba daya tausayin mahaifiyar tata sai ya kamata,dan tasan zata jefata cikin mawuyacin hali,

Tana cikin wannan dogon tunanin ne kwatsam sai Allah ya fado mata da wata dabara,gaba daya taji farin cikin ya kamata,dan kuwa tabbas hakan zaayi,kasan cewa zata iyayin komai dan ta mallaki DG Anas dinta,.

Waya kawai ta dakko gami da lalubar sunan Alawiyya ,kankace me harta shiga,itama kuma da yake ta kagu taji irin hukuncin da kawar tata ta yanke,batare da bata lokaci ba ta dauki wayar,bayan da suka gaisa,Mufida ta fara shaida mata irin nazarin da tayi,tana mai cewa

"Yes na amince da shawarar ki kawata, amma da dan gyara cikin lamari,kinga ina matukar tausayin mama,dan haka idan kin kirata ki nuna mata bazaki cutar daniba matukar tai shiru da bakinta bata fadawa kowa ba,saa'nnan layi akebi wajen fara saurarar case din kowannen mu, kasancewar Munada yawa,kuma ni yanxu nice ta 15 akan layi,ki rika kiranta duk bayan kwana daya kina fada mata halin da nake ciki gamida kwantar mata da hankali, ki kuma nuna mata kina matukar jin tausayina, hakan nema yasa watakil ma idan har kin sami dama zaki iya sakina batare da oganninki sun saniba,saboda ina matukar kama da kanwar ki data mutu,ki tabbatar kin jaddada mata illar sanar da kowa wannan alamari, nima kuma akai a kai zan dinga hadamu conference muna gaisawa da ita,amma yakiga shawarar tawa"

Idanu kawai Alawiyya ta xuma ma Mufida tunda ta fara kwararo mata wannan dogon bayanin,dan agaskiya ta matukar burgeta da wannan shirin nata,

Lallai kawata kinada basira,hakan yasa ba banxaba kike daukar na 1 acikin ajinmu,wlh shawarar tayi sosai, dan kiga baza ta shiga damua ba sosai akan shawarar mu ta farko,abinda ya rage kawai yanxu kisa mana ranar tafiya,dan kinsan da sassafe ake kama fara,abari yq huce km shike kawo rabon wani"

Da sauri Mufida ta katseta da fadin

"Ay kuwa wannan rabon nawane nini kadai,km cikin ikon Allah zanyi nasara,dan idan na shigo ma ta ciki tayi takanta".

Ay kuwa dukkansu suka bushe da dariya gamida tafa hannu,amma wannan karon saida suka rufe bakinsu bayanda sukai shewa dan sun manta da gargadin maman Alawiyya

Muje xuwa..........
[7/5, 5:37 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL'UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Page* 0⃣9⃣

*Rubutawa Nabila (maman Kalil)*
👇🏻

_*In d memory of my late father Alhaji Hudu mai agogo mai his soul rest in peace amen*_

A yaune ranar da Mufida ta sanya musu dan aiwatar da nufinsu,dan haka tun dare ta kammala shirinta tsaf,takai kayanta zaure gamida boyesu cikin tarin wasu shirgin abincin dabbobi, ba wani kaya ta diba masu yawa ba,kala hudune cacal, sai guzurin kudi da tayi dan akalla zai kai dubu sabain da biyar, shima a irin tarin da tadade tana yine na wankar samari ta tarasu,sai gashi yau Allah yayi ta bude bankin ta

Waya mufida ta kafa wa idanu,Allah ² take taga karfe 8am tayi amma gani tayi lokacin Sam baya gudu,duk tabi ta kagu,tunaninta kawai mortar da zatahau kada duk su tashi,dan taji ance da sasafe suke lodin su,

Koda karfe takwas tayi ,Mufida cikin zumudi ta nufi dakin mahaifiyar tata,da nufin karyar zuwa siyan catin waya,alabasshi ta cika wandonta da iska,

sallama tai mata saa'nnan ta kutsakai ciki,kwance ta tarar da ita a kudundune a bargo tanata rawar dari,nan mufida taja tayi turus gaban yayi wani mumunan faduwa,dan ko bata fada mata ba tasan bata da lafiya ne,take wasu zafafan hawayen takaici ne kona tausayi ne oho?suka gangaro mata kuncinta ba tare da ta shiryawa zubar suba,da sauri ta goge hawayen dake fuskarta,saa'nnan ta karasa inda mahaifiyar tata ke kwance,

"Lafia dai mama? "

Cewar mufida,cikin karfin hali ta bata amsa da cewa

"zazabine da ciwon kai mai tsanani ke damuna,amma da sauki kada ki tada hankalinki kinji mufida nah,dan nasan ki da saka damua aranki musamman ma idan bani da lafiya ,"

Cikin karfin hali maman tata ta bude mayafin data rufe fiskarta dashi gamida kallon diyar tata,hade da dan murmushinta tace

Insha Allah bazan tafi in barkiba kinji,da yardar Allah sai naga aurenki,share hawayenki bar kuka ,sanin kanki ne bana son ganinki cikin damua ,ballema harta kaiki gayin kuka

Sai sannan ne mufida ta Ankara ashe kukan da take afili ya fito fili har xubar hawaye take,ta rasa meke damunta gaba daya jikinta yayi sanyi,kukan rashin tafiyar ta zatai kokuwa na rashin lafiyar mamanta,dan bazata iya tafiya ta barta cikin wannan halinba,amma ta wani bangaren tayi takaicin faruwar hakan ,musamman shirin data dade tanawa wannan ranar,

cikin karfin hali ta tambayeta da tasha magani?nan ta bata amsa da tasha,amma duk da hk mufida sai data tursasa mata akan lallai sai sunje asibiti,hakan kua akayi badan tasoba

Kira yafi talatin Alawiyya taima Mufida amma bata daga wayar ba,hakan nema yasa taji haushi ta jefar da wayar a daki itama ta shiga sabgar gabanta.batasan cewa mufida ma bata tare da wayar ta ba adaidai wannan lkcn ba.

Dr Safara haifafiyar garin Sudan ce,itace diya daya tilo ga mahaifanta gaba da baya, tayi karatun tane gaba daya a bangaren likitanci,mahifinta shine shugaban kasar garinsu mai ci yanxu haka,km yana matukar ji da ita hk ma mahaifiyarta,ta taso cikin so da kaunar iyayenta,dan suna gatantata kwarai da gske,

haduwar su da Dg Anas ta samo asaline sakamakon wani aikin sakai daya kawota Nigeria,km da yake ance shi aure ba inda baya kai mace ,ta hakane suka hadu da juna har ta kaisu ga yin aure.

Cikin salo da iya taku safara ke tafiya kamar bazata taka kasaba,masu take mata baya na biye da ita,sakamakon yanayi irin na tsaro,dukkan wanda ya kalleta to tabbas sai ya kara na biyu dan azabar kyau da daukar hankali,lifaya ce baka wadda akaiwa kwalliyar golden hade da wasu duwatsu duk jikinta ta sanya,dan koninan tatafi da imanina,adai yadda tai kyau dinnan ko makiyi bazai ce bata haduba,kamshi kua da yake tashi daga jikinta baa maga dan irin turarurukan nan ne na hayaki masu tsadar tsiyar nan ta turara jikinta dasu,baa'ma maganar Wanda ta sanya jikin kayanta.

Kasan cewar yau ranace ta musamman da taware a rayuwarta da takan duba marasa lafiya kyauta batare da kayi booking din ganinta ba,kuma ganin marasa lafiyan nata ya taallaka ne akan talakawa marasa karfi,km dama tafi xiyartar asibitoci na gwamnati,dan nanne marasa karfi suka fiya yawan ziyarta,dukkan Wanda ta duba to magani kyutane,idan kuma ciwon naka ya kama ayi maka aikine to shima kyuta ne ita zata dau nauyin komai har a sallameka banda kudi da kayan abinci da take ta rabawa.

Yau gidauniyar tata ta saukane a saibitin barau dikko,Wanda akafi sani da asibitin dutse dake jihar Kaduna,koda samun wannan labarin marasa lafia suka taru dankam alayi sunata jira ta dubasu,wasu ma lafiayarsu kalau maganin kawai suke bukata,wasu km kawai dan suyi ido hudu da itane dan su ganewa Kansu ba labari ba,
Chapter 18 · 0% Book details