← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 26

Sashe 14

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saleema batasan wainar da ake toyawa ba tana shan waqa sai ganin Aleeyu tayi ya shige dakinsA ya fito da tabarma ya shinfida wani ya zauna duk da batajn maganar su tasan abokinsa ne dan baya kawo kowa gidan sa."

"Earpiece din ta cire a kunnan ta sannan tayi masu wani mugun kallon up and down ta watsar!"Tare da bata fuska kamar bata taba fara'ah ba!"Ta ce Haba malammai ya zaku shigo min gida ba sallama!?"Anakallahu bakasan darajar matarka ba ne azo har gida da katou a keta min haddi!!!!"

"Aleeyu ya ce "kiyi hakuri ranki ya dade, munyi sAllAma ai,Abu ne kunnenki bakiji ba!"Nasan nayi laifi wannan bakon da nayi ya rikeni shiyasa ban dawo da wuri...."

"Mtwssss!!!Aikin banzah!Kai kAsAni wato abokinka yafi matarka daraja!"Tun safe kabar gida nan kuma kasani sarai kabarni da yunwa!Koda yake ba abin mamaki ba ne tunda kasaba barina da yunwa!"Naso kasamu ta kasheni ka huta nima na huta DA masifa!"Saleema tafadi tana kumfar baki!"KAnta ta kauda gefe!"

"Hafeez da ke zaune kamar photo kallon su yakeyi kamar yaga video..."Murmushi yayi ya ce"Hajiya saleema ayi hakuri fa nine na rike oga ya rikani unguwa ne amma ayimana afuwa."

"Murguda baki tayi tare da qara turo dan kwallinta gaba!"Alamar ko ajikinta dinnan."

"Aleeyu ya ce"Saleema wannan shi ne abokina kuma amnina Abdul Hafeez da nake baki labari ko yaushe,Yau Allah yayi mun sake haduwa da shi."Hafees ga matata nan saleema."Kema uwargida kinga Engr.Abdul Hafeez ko!?"

"Tabe bakinta tayi race"Eh

Na ko ganshi ashe jin sa yafi ganinsa ma!"An dade ana sharara min labarinka!Hafeez to ya gida ya bayan rabuwa....?"

"Duk da zancenta yasa yaqara duba jikinsa kaf ba makosa!Amma tace jinsa yafi ganinsa abin ya Sosa masa rai!"Amma daurewa yayi yace"Duk suna lafiya qlaw sunce agaida,Ya akaji da rashin yaran mu Allah ya gafarta musu sai hakuri da jArrabawar rayuwa!"

"Amin nagode,Hakuri kuma da jarabawa ku ta shafa ni tuni na karbi sakamakona jira nike in kara gaba!"

"Kansu ya daure dukan su,DA jin magAnarta sai dai shiru sukeyi na dan lokaci daga mai gidan har baransa."

"Kai lado zo nan dauko Kofi je randa daubowa Hafeez ruwa......"

"A'ah mun koshi wallahi nagode ba sai ya kawo ruwan ba."Mun sha ruwa a mota."

"Aliyu baiji dadin kalaman saleema ga abokin ba!Gashi har darajar kawo masa ruwa bai samu ba!"Duk komai shi keyiwa kan shi amma bai kamata tayiwa abokinsa ba!"

"Tashi yayi ya zuba ruwa a botoci sukayi alwala,ledojin ya mika mata yace ki dibi mai isarki ki zuba mana sauran."Kisama su lado suma!"

"Tuni Hafeez ya fita yana jiran fitowar bawan Allah abokinsa mai hakuri dan saleema ta hasala shi,Da shi ne sai ya mareta dan ya tsani,wulaqanci da rainin hankali!"

"Ledar saleema ta karba awulakance ta bude taga friedrice da pepper chicken take away hudu, dayar ledar drinks da snacks ne, ta ce"Kaico!Maciji baka raminka sai na wani daga ni basai anyi bayani nasan ba kudin kwadagonka ba ne anan,Sai dai gumin wani qato caaan....."

"Dakata saleema wai meye haka!?Wallahi bakida imani da tausayi!Kiyi min komai zan dauka amma banda Hafeez dan Allah ki ajiye masifarki gefe har ya tafi abinshi!"Aliyu ya ce'A zuciya ko ranshi na kuna da ana canja mata nan take da wallahi yanzu ya canja Wucewa yayi yasamu Hafeez suka tafi massalaci domin yin sallar magrib."

"Bayan sun dawo sun sami saleema ta sallami su lado,Ta ajiye plate cike da abinci tana ci tana daga bottle din fanta ga naman kajin shima sai yaga takeyi."

"Da sallama suka kara so inda suke zaune"Aleeyu ya ce Ina abincin saleema!?"

"Uhuuuum nifa na manta kace ajiye maku da na diba wanda zanci su lado na zubewa sai wanda zan ci anjuma dan yanzu na ranan ne da banci ba nike ci,Kasan na yuni da yunwa!"Ga abincin mun dade bamu hadu ba,Sai agidan abokan arziki."

"Allah mai iko,Su malam hafeez an dawo!?To barkah ka ganni ina kwasar gara ai sai kace ba ruwan ne kadai aka sha a waje da mota ba har wannan!"Yanzu ku anbar mata da yunwa kamar takashe su gida!"dan zalunci amma ana waje ana cin dadi hakan ina fatan kai ba irin sahoron nan kake ba!"Ta nuna Aleeyu da kwalbar ta fanta."

"Aleeyu yaji haushinta sosai ba abinci yana jin yunwa!"Ba kunyar Amininsa!" Ba magana mai dadi!"Ai baisan lokacin da ya isa gareta da zafin nama ya sharara mata mari ba!"Sai da taga wuta giragizai nai mata yawo!"

"Aleeyu ni ka mara!?"tace a razane idonta na fidda ruwa!!!"

"Eh,ko zaki rama ne!?

"Hmnnnnn ka dauki bashi kajira lokacin biya banza matsiyaci wallahi kaci darajar Hafeez da sai an rabamu agidan nan azzalumi mugu kawai marar amfani!!!!"

"Haba!saleema ki daina yiwa mijinki mugun alkaba'i hakan!"Meye duniya da zaki dauketa da zafi!"Kuyi hakuri,mana Aleeyu muje!"Saleema ga wannan kisa kati(5k)Dan Allah kiyi hakuri!"Hafeez ya CE"Tare da ajiye mata kudin a kasa....A zuciyarsa yaji dadin marin sosai da Aleeyu yayi mata...!"

"Fita sukayi Hafeez na qara ba Aleeyu hakuri akan abinda ya faru...sannan suka nufi mufida restaurant sukaci abinci suka koshi."Aleeyu duk da ya hakura amma yace bazai kwana gidan ba Sabon gidansa zaije su kwana har Hafeez din."Ba yadda Hafeez bai masa mita dan ya hakura ya koma gida, amma sai yaqi."Hakan suka hakura dole."

"Saleema ko jiran dawowar Aleeyu tayi amma bata Ganshi ba!"Dole ta hakura tare da anada masa masifar aduk sanda yadawo dan shakka babu wallahi wannan karon sai yabata takardar saki!"

"Lailah ta kira tare da shaidah mata komai!"Har da Karin dan gishiri."

"Hakuri tabata akan lafiyarta da ya taba sannan ta ce kadama ki soma saurara masa ga sanadi nan kin samu na kai gida"Yabarki da yunwa kinyi maganar hakkin ki!ya dakeki...!"Kinga dole aduba maki! Bugu da kari kice baya kwana gida masu kudi yake bi maza suna biyansa"Dan ni sam ban yarda da abokin nan nasa ba!"

"Wallahi lailah hakan za ayi yabani takardata na huta!"Nima nafara zargin Hafeez din tun aurena da Aleeyu bai taba kwana awaje ba!"Matukar yana gari ba tafiya yayi amma yanzu 12 na dare bai dawo ba tun 8:30 na rufe gida dan neman magana naso yadawo na wulaqanta shi a wajen!"

"Yanzu kiyi hakuri saleema har zuwa goben mugani ko!"Inji lailAh."

"Numfashi ta sauke mai nauyi tace to lailah nagode,"Dazu fatty ta fadamun gobe yaillabanta,da Alhajina zasu dawo."

"To masha Allah lailah tace a dayan bangaran,Yanxu sai kifara shirin haduwarku."

"Hakan za'ayi gobe zanje kitso da lalley,kuma dazu na hada kumkum da dilka goben zan shafa."

"Kina wuta saleema tawa,Allah yabamu Nasara."

"Ameen nagode."

"Yawwa ni kinga ko kwana banaji chat zanyi yanzu na rage dare banzan may be yau awaje zai kwana,kadangarun bariki sun rike shi."Inji Lailah kenan zancenta tak kai tsaye ba wata farbaga ko jin zafi!."

"Nikam bacci nikeji sai gobe idan mun hade gidan fatty."Alhajinki ko Allah ya taro miki shi."

"Amin idan yana da rabo!"Nagode asuba tagari,Lailah tace"tare da kashe wayarta,Saleema ko bacci tayi duk ta dade tana tunanin Aliyu ko ina zai kwana oho!"

"Tunda safe ta tashi misalin 8: 30am ta shirya ta kulle gidan,ta nufi gidan lalle kamar yadda ta tsara scan zatayi dilkan"

"Basaura airport suka wuce shi da abokinsa domin jirgin 9:00am zai bi zuwa Abuja, daga can na 1:00pm zai bi zuwa Sudan."Sunyi bankwana sosai Aleeyu yaqara godewa Hafeez, kamar kada su rabo har da hawayen Hafeez!"domin yana tausayin Aleeyu da duk ya rame! yayi baki! ya lalace kamar ba shi ba."A karshe Sallama sukayi da juna! Hafeez jirginsu ya daga izuwa sararin samaniya."Aleeyu yana tsaye yana masa hannu har ya daina ganinsa!"Komawa yayi mota yana tunanin shawarwarin Hafeez akan saleema da hakan ya wuce Argungu."Yana zuwa shiga gari, gidansa ya nufa sai dai ya cimma gidan a rufe....."Tsaye yayi wurin kamar ruwa sun cinye shi....Tabbas zancen Hafeez dutsi ya godewa Allah da bai sanar mata alheran da Abokinsa yayi masa ba!To yanzu da safen nan ina ta tafi!?Shakka babu karshen wuya yazo dan yau zata hadu da fushin sa ya gaji da rashin mutunci Auren nan shi ne mafita kamar yadda Hafeez ya shirya masa komai!"Yanzu ma yaji yana kaunar Karin auren nan da mako biyu ba fashi amarya zata tare a sabon gidan sa...."Yana cikin tunanin wani dattijo yai masa sallama...tare da shaidah masa sune wadanda suka sayi gida sun zo duba gidan ne jibi zasu tare.....Gabansa yayi mummunan faduwa!!"Amma ya daure yace Baba anyi maka bayani sosai kamar ba gidan nan bane!Dan ni ba wanda na sayarwa da gidana!!!"Takardar shaidar gidan dattijo ya mikawa Aleeyu sign dinsa daram ajikin takarda akasa ga kudin da aka sayarda gidan kuma saleema tayi sign irin nashi tsaf!"Baba nagani kayi hakuri ga takardar gobe ka dawo Ku duba gidan!"Yawwa nagode dan nan!"Har na tsorata kar yan damfara muka hadu da su!"Sallama sukayi ya wuce!"Aleeyu ko mamakin ikon Allah yakeyi tabbas saleema ba matar zama bace!"Da ta tona masa asiri!To ina kudin!?Me tayi da miliiyan harda rabi!? In shaa Allah zai jirata a motarsa har sai tadawo daga duk inda ta tafi!!!!!!!!!!!"

Muje zuwa.......Sannu bata hana zuwa.... Ku dakace mu domin zuwan Ramadan...... Amma zai cigaba da zuwan maku bayan Azumin Ramadan....

***** *****

*Alk'alamin*🖋
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
( *Nabeelert Lady*)
👇🏻

*Allah ya bamu ikon d'aukar azumi lafiya, Allah ya sadamu da alkhairin da yake cikin watan Ramadan, Allah yasa muna cikin 'yantattun bayi amin. Ina ma kowa fatan Alkhairi*

Hibbah tana shiga gida ta fad'a ma Ummanta yanda sukayi da Muftahu. Murmushi Umma tayi tana fad'in ai ba damuwa, lallai yaron nan d'an baiwa ne, nima bana son a kawo lefe da wuri kowa ya gani, gara sai biki ya kusa da kadan sannan akawo, kinga lokacin an shiga hidima, maganar rage kaya kuma wannan ba komai, idan yaso sai in zab'i wad'an da zasu kalli lefen kawai.

Hibbah tace Umma jeran fa taya za'a san yanayin gidan? Umma tace sai ki tambayeshi ya fasalta maki yanda gidan yake kawai, nifa bana so kina masa musu akan abinda yace, kinsan dai boka be bamu maganin mallaka ba, bana son ki k'ureshi gara ki bishi a sannu, kina shiga gidan zamu mallakeshi, har gida sai kin saya da kudinshi. Rungume Umma Hibbah tayi tana murmushi.
Chapter 14 · 0% Book details