← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ta matsa ciki ta jiyo muryar Umma tana fad'in kaga irin abinda nake fad'a maka ko, anfi awa d'aya dana aiketa kasuwa amma har yanzu bata dawo ba, dama kafin ta tafi sai da tayi mani rashin kunya wai girmanta yawuce ace taje siyen kaji kasuwa, sai da taji nace zan fad'a maka kafin ta amshi kud'in ta fita sai k'unk'unai takemun.

Kafin Malan yayi magana sukaji sallamar Hamrah. Gaba d'aya suka juyo suna kallonta. Da sauri Umma ta matsa tana fad'in ya na ganki hannu biyu ina kajin? Duk'awa Hamrah tayi tana fad'in wallahi naje har anyi ciniki nazo bashi kud'in bangan su ba.

A firgice Umma ta saki ashar tare da shak'o Hamrah tana fad'in wallahi baki isa ba, shegiya 'yar bakin ciki, ai dama daga yanda kika tafi nasan ba kiyi niya ba, to wallahi kinji na rantse maki acikin gadonki za'a biyani.

Kamar daga sama sukaji an sauke ma Hamrah icce a jiki. Ihu tasa ta shige jikin Umma. Malan ne rik'e da icce yana fad'in wallahi nagaji da iskancin ki, dan Uwarki kamar ke ace baza ki iya rik'e kud'i ba sai kin zubar? Dama yanzu take fad'a mani rashin kunyar da kikayi mata ashe kud'in ma zubarwa zakiyi.

To wallahi sisi na bazaiyi ciwo ba, waccan akuyar da Uwarki ta bar maki za'a yanka a tarbi bakin da ita. Umma tace a'a Malan ban yarda da wannan abun ba, amatsayin su na manyan baki bazamu tarbesu da naman bak'ar akuya ba, ai wallahi ko naman rago sunfi k'arfinsa, harkar girma miyar ta nama, dan haka idan bata da kud'in biya na dole asayar da akuyar yanzu a bani kud'i na.

Malan yace wannan haka yake, kallon Hamrah yayi yana fad'in kina da kud'in biyanta ko asayar a bata kud'in ta? Cikin kuka Hamrah tace wallahi Baba bani da ko sisi, kuma bada son raina kud'in suka faad'i ba.

Umma tace ke kika jiyo ni dai abiyani kud'ina kuma yanzu. Malan yace shikenan bara na kaima Bala mahauci sai ya siya. Da sauri Umma tace ai daga gida ake fara ciniki, tunda akuyar ta saba da gidan zan taima na siyeta.

Malan yace shikenan ma, gaskiya kina da zuciya me kyau, to nawa kika siya? Umma tace tunda akuyar ba wani abincin kirki ake bata ba zan daure na siyeta dubu biyar, domin muna ganin da yanda take rayuwa.

Kallonta Hamrah tayi tana kuka, wai akuyar da take da ciki ce za'a sayar dubu biyar, akuyar da duk abinda ta samu dashi take siyo mata dussa amma wai dubu biyar.

Malan yace e gaskiya yayi, sai ki kawo kud'in a cire dubu biyu a bata sauran ukkun. Umma tace amatsayin ka na dillali kaima dole a baka la'ada ai.

Murmushi Malan yayi yace haka ne, tunda agida na take rayuwa bazanki k'arb'ar dubu d'aya ba. Umma tace bara na d'auko kud'in daga yau akuya ta zama tawa.

Haka ta kawo kud'in aka bama Hamrah dubu biyu Malan ya d'auki dubu d'aya aka maida ma Umma kud'in ta. Tashi Hamrah tayi tana kuka tashige d'aki. Umma tace fitowa zakiyi kije ki siyo ubanwa zai siyo maki.

Malan yace bani naje nasiyo daga can sai nayo cefane gaba d'aya. Umma tace ka rago kud'in lemun da za'a siya masu goben, kuma kaima bashi na baka tunda hakkin kane. Malan yace angama Uwargida ran gida.

**** *****

Hannu Momy tasa tana share hawayen tausayin 'Danta da suke zubo mata, wannan wane irin abun kunya ne haka, ace yarinyar da 'Danka yake nema ita ce kuma zaka aura. Lallai dole Bilal yashiga tashin hankali.

Hannun Bilal taji ya rik'o nata yana fad'in Momy dan Allah kada ki fad'ama Abbah wannan maganar, da alama shima yana sonta, zan iya sadaukar da farin ciki na agareshi.

Hannunta ta cire tana fad'in wannan abun kunyar yayi yawa Bilal, amma dole naja bakina nayi shiru, domin idan ma na fad'a masa zai ce nayi haka ne dan na hanashi auren da zaiyi, da ace ma bai fad'a mani zaiyi aure ba dan na fad'a ba wani abu bane, amma yanzu da ya ji zaice shiri ne mukayi, saboda kishi yasa na fad'i haka.

Bakomai Bilal Allah yaga zuciyarka, tunda har ka sadaukar da farin cikin ka ga Mahaifin ka kai ma Allah bazai barka haka ba, insha Allahu wata rana zakayi farin ciki, kuma Allah zai kawo maka wata mafi alkhairi, ni da kai ina rok'on Allah ya saka mana juriyar abun, kuma a yanzu naji bana bakin ciki da aurensa, domin na gano cewar Mahaifinta saboda kud'i zai aurar da ita, hakan yana da alak'a da sharrin Matar Uba, dan haka zan aje komai na rungumi k'addara.

Bilal yace nagode Momy, a yanzu kam naji dad'i, domin nasan zaki kula da Hamrah, baza tayi maraici ba, amma Momy ina neman wata alfarma. Kallonshi tayi tana murmushi tace wace irin alfarma kake nema? Gyara zama yayi yana fad'in ina so kisa baki domin Abbah ya barni na tafi Dubai sati mai zuwa domin ina so na fara kasuwanci kuma acan nakeso na zauna har sai nan da wani lokaci kafin na dawo.

Jinjina kai Momy tayi tana fad'in dama ai kana da visar can k'asar, domin farin cikin ka dole na taimaka maka ka tafi hakan zai sanyaya zuciyar ka, domin baka nan za'ayi komai.

Bilal yace da alama Abbah bai tab'a zuwa yaga Hamrah ba, domin bata fad'a mani yaje ba. Momy tace tunda bashi ita akayi kasan bikin bazai dad'e ba shiyasa ma bai damu da zuwa ganin ta ba.

Bilal yace nagode Momy Allah yasa Abbah ya amince. Momy tace amin, amma ina so ka saki ranka saboda bana so ya matsa maka da tambayar abinda yake damun ka dan bana so yashiga damuwa kuma ga hidima agabanshi.

Murmushi Bilal yayi yana fad'in Momy halin ki daban ne, duk da Abbah zai maki kishiya amma baki son abinda zai sashi shiga damuwa, lallai Momy kina d'aya daga cikin matan da ake kira *JIGON AL'UMMA*, Allah ya k'ara maki juriya da hak'uri. Momy tace amin. Bara naje na had'a ma Abban ku abinci.

Da sauri Abbah ya bar jikin k'ofar jiki a sanyaye, har wasu hawayen tausayin matarshi da 'Danshi yaji sun cika masa ido. Tun lokacin da Momy tashiga d'akin Bilal shima ya taho da niyar shiga, domin wajenta zaije sai yaga ta nufi d'akin Bilal. Maganar da yaji tana mashi ne ta hanashi shiga d'akin domin yasan idan yashiga Bilal bazai fad'a mata gaskiya ba, shi kuma yana zargin abinda Bilal yaji ya fad'a ne yasa shi ya suma, hakan yasa ya tsaya har ya gama jin komai.

Haka ya k'arasa d'akinshi jiki a mace, kenan Malan Bukar k'arya yake masa? Dafe kanshi yayi yana jin tausayin Bilal da Matarshi.......

Muje zuwa.......
[7/5, 5:38 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Alk'alamin🖋*
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
*(Nabeelert Lady)*
👇🏻

*Page* 1⃣1⃣

Dady ya dad'e ad'aki yana nazari akan maganganun Bilal, tashi yayi yashige band'aki yayo wanka, sai da ya kammala shiryawa kafin ya fito zuwa falonshi. Yana zama sai ga Momy tashigo d'auke da kular abinci.

Bayan ta zauna ta kalleshi tana fad'in yau na barka kai d'aya. Murmushi Dady yayi yace nima nad'an kwanta ne sai yanzu nayi wanka na fito. Bud'e kular abincin tayi ta zuba mashi tana fad'in yau dai mutuminka aka dafa dambun shinkafa.

Dady yace amma kin kyauta, gashi ya sha zogale. Bayan ta mik'a masa ya faraci tayi shiru tana tunanin ta inda zata fara mashi maganar tafiyar Bilal waje. Duk abinda takeyi yana kallonta ta gefen ido kawai yayi shiru yana cin abincinsa.

Gyara zama tayi tana fad'in Bilal yashigo wajen ka kuwa? Dady yace tun da muka gaisa dashi ban sake ganinshi ba, da alama har yanzu jikin beyi sauk'i ba ko? Momy tace yaji sauk'i akwai dai maganar da yakeso kuyi kuma yana ganin kamar bazaka amince ba.

Dady yace kila yasan maganar ba mai amfani bace shiyasa ya kasa zuwa yayi ta. Momy tace a'a, kawai yana so ne ka barshi yaje Dubai ya fara kasuwanci saboda anan kasuwancin baya tafiya.

Murmushi Dady yayi yana fad'in amma wannan shawarar tashi atsakanin kwana d'aya yayi ta ko? Domin nasan Bilal yafison zamanshi anan amma gashi yanzu ya sake magana.

Momy tace kasan halinshi ai, kila Funtuwar ce ya gaji da ita. Dady yace shikenan kuma bazaiyi aure ba? Momy tace zaiyi mana, wai kafin ya samu matar yakeso ya tafi da ya samu mata sai ya dawo ayi biki.

Dady yace wannan yana da kyau, ina so naga mutum mai son neman na kanshi, idan ya fara kasuwancin kinga idan Allah yasa mashi albarka kinga ya samu hanyar k'aruwa, bakomai tunda yana da Visa kawai yazo ya fara shirin tafiya ko cikin satinnan sai ya tafi Allah ya bada sa'a. Murmushi Momy tayi tace amin Alhaji mungode.

Dady yace idan kin fita ki turo mani shi nafiso nan da asabar ya tafi. Tashi Momy tayi tace yanzu kuwa, ai dole Bilal yayi farin ciki idan yaji ka amince. Fita tayi tana mai nuna farin cikinta.

*****

Sosai aka tarbi bakin da suka kawo kayan sa rana, babu b'ata lokaci aka saka biki nan da sati shidda kasancewar kowa ashirye yake. Haka sukayi masu sallama suka tafi cike da farin cikin irin tarbar da akayi masu.

Umma baki yaki rufuwa ganin irin kayan sa ranar da aka kawo masu yawa, domin Mufty yayi kok'ari. Haka tayi ta yada ma Hamrah habaici ita da Hibbah. Hamrah kuwa tana tsakar gida tana ta wanke kayan da akayi amfani dasu, ga rana gashi suna da yawa, haka tayi ta aikinta tana jinsu domin bata da bakin magana.

Zaune suke ad'aki ita da Malan Bukar bayan ta gama raba kayan sa ranar, anan ta mik'a ma Malan Bukar nashi dana danginsa, nata ta ware tana fad'in anan zan rabama 'yan unguwa da sauran mutanan arziki, sauran kuma abama Hibba domin itama zatayi rabo.
Chapter 23 · 0% Book details