← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan Bukar yace banga kin fitar dana dangin Hamrah ba ko acikin naki zaki aika masu? Wani kallo Umma ta bishi dashi, da sauri yace a'a ina nufin ko zaki basu ne? Kai bama sai kin aika masu ba tunda itama za'a kawo nata saboda atare nakeso ayi bikin.

Cike da masifa Umma tace babu wani biki da za'a had'a, yanda Hibbah ta riga Hamrah samun miji dole ariga yin bikinta, haka kawai azo a had'e bikin akasa gane na 'yar gata, kai tsaya Malan, naga kamar kana so ka kawo mani wani kilibibi, to wallahi bazan d'auka ba, dole a banbance bikinsu.

Matsowa yayi yana fad'in haba uwargida sarautar mata, ni na isa nayi wani abu ba tare da amincewarki ba, kawai dama shawara ce na kawo, amma ina so ki bari ayi bikin gaba d'aya da na Hamrah, kinga babu wanda zai gane bamu da kud'i, kinsan dai bamu da wasu kud'in da zamu sayi kayan abinci masu yawa da za'a dafa aranar biki, gashi kuma mijin Hibbah d'an manyan mutane ne, idan mukayi k'aranta zasu raina mu, amma idan muka had'a bikinsu kinga Hibbah ce zata ci riba, na farko ba ruwanmu da siyen gara, domin nasan Alhaji zai aiko da kayan abincin da za'a dafa, kuma nasan zai bani kud'i masu yawa kinga sai muyi amfani dasu.

Murmushi Umma tayi tace shiyasa akace maza kunfi mata kaifin tunani, shiyasa nake sonka Malan, tabbas duk abinda aka kawo na Hamrah dole gidan Hibbah zai tafi, tabbas wannan shawara ce mai kyau, shikenan a had'a bikin kawai.

Malan Bukar yace yauwa nagode da kika fahimce ni, kinga idan suka kawo kayan sa rana sai a aika ma Iyayenta na can. Umma tace haka za'ayi, amma ba duka za'a aika masu ba, zan aje sauran nayi kullin biki dasu. Malan yace an gama, anjima da yamma zanje na sameshi sai muyi maganar.

*****

Sosai Bilal yaji dad'in yanda Dadynshi ya amince da maganar tafiyarshi, nan yayi ta masa godiya. Dady yace anya Bilal ba akwai abinda kake b'oye mani ba kuwa? Bilal yace bakomai Dady kawai ina farin ciki ne nima zan fara kasuwanci a waje. Dady yace toshikenan Allah ya bada sa'a, amma zakazo wajen d'aurin aure ko? Saurin d'ago kai Bilal yayi kafin ya mayar dashi yana mai jin wani d'aci azuciyarsa.

Dady yace koda yake nima bazanso bikin ya d'auki lokaci ba akusa nakeso ayishi, tunda baka dad'e da tafiya ba kawai kayi zamanka bayan biki sai kazo kaga Auntyn ka. Runtse ido Bilal yayi hawayen bakin ciki suka ciko a idonshi.

Murmushi Dady yayi ganin yanayin daya shiga. Gyaran murya yayi yace shikenan tashi kaje kacigaba da shiri zuwa asabar insha Allahu sai ka tafi, bani wayata nakira Malan Bukar inaso muyi magana akan sa rana ne.

Jiki a sanyaye Bilal ya tashi ya d'auko masa waya, da sauri yabar falon saboda hawayen da yake b'oyewa sun fara zubowa. Yana fita Dady yayi murmushi yana girgiza kai, sosai ya jinjina halin dattako irin na Bilal. Bayan ya kira Malan Bukar anan yake fad'a masa dama anjima zaizo. Dady yace shikenan sai kazo munyi maganar.

****

Zaune suke a k'ofar gidan su Bilal, bayan sun gama gaisawa Malan Bukar yace Alhaji kwana biyu ban l'eko ba, wallahi hidima ce ta tasoni gaba, kasan yau aka kawo kayan sa ranar yayar Hamrah, nan da sati Shidda za'ayi bikin, shine nace bara nazo naji ko kaima kana so a had'a da naka? Murmushi Dady yayi yana fad'in ai ni mai laifi ne ma, har yanzu na kasa zuwa naga amaryar tawa, kasan idan akace ka wuce abu sai karik'a jin nauyin yinsa, wannan dalilin ne yasa har yau na kasa zuwa mu gaisa.

Malan Bukar yace haba Alhaji, ba dai na baka ita ba, ai ko baka je ba za'a kawo maka ita har gida, zamanin Iyayen mu ma su basa ganin matansu sai an kawo masu, dan haka ba komai Alhaji ba sai kaje ba, duk abinda yarinya take buk'ata nasan zaka iya wakilta wani yayi maka, idan tashigo gidanka sai kuga juna sosai.

Murmushi Dady yayi yace nagode sosai, dan haka zan aiko da kayan sa rana idan yaso sai ahad'a dana Yayarta ayi gaba d'aya kaga anyi zama d'aya kenan ko? Malan Bukar yace sosai kuwa, gaskiya nagode, domin idan aka had'a nima zan samu sauki wajen dafa abinci, amma idan aka ce araba dole kowane biki sai an nema masa abinci idan wani bikin yazo, gashi ni kuma mai k'aramin k'arfi ne.

Dady yace wannan ai ba wani abu bane, ni zan aiko da duk abincin da za'aci a lokacin bikin. Malan Bukar yace nagode sosai Alhaji Allah ya k'ara girma.

Dady yace amin. Amma Malan Bukar ina so na tambaye ka, shin itama Hamrah mahaifiyar Hibbah ce ta haife ta? Da sauri Malan Bukar ya d'ago kai yana kallonshi cike da fargaba......

***** *****

*In the memory of my late father Alhaji Hudu mai Agogo ,my his soul rest in peace amen*

_*Rubutawa Nabila (maman khalil)*_
👇🏻

Misalin karfe bakwai na safe motar honorable wata zafafiyar corolla LE ta tsaya dadai kofar gidansu Mufida,kai tsaye gidan ya shiga, wannan dama shi ba bako bane agidan,koda shigarsa ba abinda idonsa yayi arba dashi face fuskar masoyiyiar Mufida,taci kwalliya ta kece raini,sai kamshi take,take gabansa ya kama bugawa kamar zai fashe,da sauri ya dafe saitin zuciyarsa da hannun sa, kana ya kauda ganinsa daga kanta,Mufida ta fiskanci yanayi da yashi amma Sam ta basar,cike da faraa' ta amsa masa sallamar da yayi kana tai masa iso har dakin mahaifiyar tata,ashirye tsaf suka taddata,dan haka batare da bata wani dogon lokaciba Mufida ta dafe kafadunta kana ta kike hannunta dan taimakawa tafiyar tata,

Shidai honorable ba abinda yake sai satar kallon kyakyawar surar da Allah yayiwa Mufida,ya rasa me yayi mata dataki amsar tayin soyayarsa,dadai rufin asiri na xamani yana dashi ga gidansa da km motarsa,ga uwa uba dangantakar dake tsakaninsu ta jini,dan da mahaifinsa da mahaifiyarta uwarsu daya ubansu daya,amma Sam ya kasa gane wane laifin yayi mata da take azabtar da zuciyar sa haka,yana cikin wannan dogon tunanin ne yaji maman Mufida tace

"Subhanallah"

Ay kua cikin sauri yakai hannunsa ya riketa gam gudun kada ta fadi,batare da ya ankaraba sai jin yayi hannunsa rike dana Mufida,gaba daya jikinsa yadau rawa, sakamakon wani irin tatausan laushi da yaji a hannun nata,turaren jikinta ya kuma bugar hancisa,cikin sauri ya xame hannunsa daga nata, ya wayence da cema mama

"sannu badai kiji ciwoba ko?kibi a hankali wajen ne da dan ramuka "

"A babu komai dana,Allah dai yayi albarka "

mama ta bashi amasa dashi,wani siririn murmushi Mufida tayi,dan ta fahimci duk abinda ya faru dashi,amma ina ka makaro danni tini xuciyata tana wajen wanin ka ,ta fadi a xuciyarta.

Koda isarsu wajen ganin likitan sun samu Dr safara bata karaso ba tukunnan,dan haka suka sami waje gaba dayansu suka zauna, mufida ta dakko wayarta tana dan danne danne amma shi gogan naka Sam ya kasa dauke idonshi daga kallonta,Allah² yake ma tadan kallo inda yake koya samu yayi mata wata yar alama dazasu dan keba amma Sam taki kallon gunda yake hakannan dole ya hadiye miyansa haka,

Cikin xuciyar mufida tunanine kala kala take na yadda zata billowa wannan alamarin,ta kulla wancan ta kwance wancan,sai jitai honorable yace

"Yauwa mama gatanan ma ta karaso,kinga harda mijinta ma yau"

Wani mugun bugu kirjin mufida yayi take ta runtse idanunta gam, tana ammaton sunan Allah a xuciyarta,ahankali ta rika bude idanunta dan gudun ganin abinda zai bata mata rai,Dg Anas idanunta suka fara arba dashi ,yasa wani danyen Boyle milk color ,hularsa fara Sol haka ma takalminsa,fiskarsa sai faraa' take,take mufida taji kamar taje ta rungume shi a haka dan gaba daya ya gama tafiya da imaninta,murmushi kawai take ita kadai hade da saukar da numfashi a hankali,amma ayayin da idanunta suka fara hango mata Dr safara a daya gefen nasa, take ta tsinci kanta cikin matsanan cin kishi,musamman ma data ga kayan jikinsu iri daya babu wani babanci face na dinki,dan itanma farin cover shoe ne gamida farar wata rantsatsiyar purse sai dan siririn mayafi data nade kanta dashi,tayi matukar kyau,kana gani kasan suna cike da kaunar junan su,dan sai murmushi kowannen su kema junan su,ana tafiya ana wani magana kuskus

File din maman mufida shine na biyu akan layi ,dan hk batare da bata lokaci ba ana gama ganin na farko aka kira sunanata,honorable yaso ya biyosu shima,amma mufida ta dakatar dashi ,gudun karya karya mata budget dinta,ba yadda ya iya dole ya hkra,cike da fara Dr safara ta tarbesu hannun biyu biyu,harda dan tasowarta ma ta taryi mama gamida zaunar da ita kan kujera a hankali,amma fa duk wannan halaccin mufida kallonsa take a matsayi kisisina irin na mata,dan haka ma ko gode mata batai ba illah ma kara tsanarta da tayi,Dr safara tayi nisa wajen tambayar mama abinda ke damunta,harma ta bukaci data kwanta kan wani gado dan duba ta sosai,mufida kuwa idanunta ba abin da yake hangen illah wajen da wayar Dr take ,allah ² take hakalinta ya dauke daga wajen tai wuf ta dauki wayar,ana haka cikin saa' kuwa tayi kamar ta yarda wani Abu a kasa,tasa hannu ta janyo wayar,amma cikin rashin saa' ansa mata security, ranta kuwa yayi mugun baci, ba dan tasoba ta maida wayar kan table ta ajiye, ajiye warta keda wuya sai ga kira ya shigo wayar,koda Dr taji irin personal ringing tone din data saka wa mijinta ne,tai gagawar cewa mufida

"Dan Allah yan mata yi picking call din kidan karamin a kunne na hannuna nasa safar hannu pls,"
Chapter 24 · 0% Book details