← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lailah ya haka naga kin wuce!"kin saki layin gidanmu ina kuma zamu biyah!?."Saleema ta ce fuskarta dauke da tambaya!"

"Lailah da ke driving dinta cikin kwarewa juyowa tayi gefenta, da saleema ke zaune,Ta kalli saleema tayi Murmushi,Sannan ta ce"To sarkin korafi!"Unguwar malammai,za muje kuma tafiyar nan ma taki ce saleema,gwara muyiwa tufkar hanci,mu tunkare su da shiri,Wani zaure zamuje inda za a dauko Baba da Mama agaban mu arufe masu baki!"Ko tashin zancen aurenki bazasuyi ba, bare dalilin sakinki da Aleeyu yayi!" kuma duk wanda yazo masu da zancen zasuyi masa korar kare!"

"Ajiyar zuciya saleema tayi tace"kin fa kawo shawara ni duk na manta komai wallahi!"Ko kan Malam banbi bah!"Inji saleema."

"Nikam bazan manta da shi ba Dan da bazarsa nike taka rawata, a gidana, da gidanmu uwa uba kuma hegun mayun can dangin miji!"kinga sai yadda naga dama kuma nace akeyi a kowanne bangare, kuma mallam mudi ne ya tsaya min."

"Tafawa sukayi suna dariya saleema tace kawata kin zama kadangaren bakin tulu......"Kwarai kuwa saleema ni ciwon ido ce kuma kutuwar uwa zama da ni dole...!"

"Ni adda ke ina tsoronki lailah....Shu'ama ce ke wallahi."

"Hhhh.....fada da babbar murya saleemataaah..."

"Dai dai nan suka isa bakin gidan mallam mudi,Parking lailah tayi suka fito,Kofar zauren gidan suka shiga sai dai me...."timjin yake da mnyn almajirai,da masu kudi da 'yan kasuwa ana yiwa mallam fada."Dayan hanyar gidan sukabi inda baza a gano su ba,Daidai dakin mallam suka tsaya!"Malama Hajiya, ce ta tarbesu tare da masu iso a dakin,shinfida da ruwa takawo masu tana munna ta aika a sallamo mallam a zaure domin yayi baki,Da yake Hajiya matar mallam da lailah sun San juna sosai,Kuma alkhairin lailah na kudi da tufafi na shiga hannun mama Hajiya akai akai."

"Da sallama mallam mudi ya qaraso da tasbahar sa qatuwa irin mai dubun nan har
qasa,Kan shi yasha nadin rawani,ya sha alkaybba mai matukar kyau sai muzurai yake da ido yana lazimi,Da murna ya iso wurin,Bayan sun zauna sun gaida shi lailah ta sanar masa dalilin zuwan su sarai daga nan taqara da zancen Alhaji tasi (Abokin yallabai mai son saleema)Domin ajawo masu hankalinsa zuwa ga saleema itama kanta aqara turara mata yallabanta."

"Mallam mudi washe baki yayi."Kana ya ce"Ba Matsala kamar anyi an gama."

"Laila ta ce nasani mallam tamkar yankan wuqa ne..."

"Mallam ya dubi saleema ya ce "karki damu in shaa Allah komai yazo karshe kuma alhaji tasi zai aureki sai kin zama tauraruwa mai haskawa agidansa."Zancen iyayenki yanzu ya kike so shin mallake su kike so kiyi?Ko kuma rufe masu baki za'ayi sai yanda kice? Idan ko kina son asa masu tsoronki da shakkarki ne kici duniyarki da tsinke kiyi abinda ranki ga so sai ayi?Yanzu fada min me kike so?nikuma yanzu zan dukufa ga rokon Allah saidai ku isa gida Ku sami labari ya canja."

"Mallam nidai kawai ka rufe masu baki duk abinda zanyi kar su saka min ido ko baki fakat!"

"To.....to..toooo....Angama Hajiyah." turensa mai dauke da qasa ya janyo wasu qananan duwatsu ya dinga yawo da su aturen tare da tambayar sunayen iyayen saleema, bayan ya kammala komai."Ya ce zasu iya wucewa."

"Kudi masu yawa lailah ta bashi wai ayi sadaqa"Tare da masa godiya."Hajiya matar mallam mudi ma kudi lailah tabata sukayi sallama suka wuce."

"Mallam mudi ko 3k ya miqawa Hajiya matarsa a aika kasuwa asawo masu zakaru biyu ayi masa miya."Da murna ta amsa tana godiya da yi masa fatan alheri."
("Ikon Allah mata jarin malamai da bokaye kudinku sune na jin dadi da cin kaji ba nasun ba duk mai wannan halin tayi karatun ta nutsu,Allah maji rokon bayinsa ne,mu roke shi da zuciya mai kyau,sai ya amsa mana,muji tsoron Allah mu gujewa shirkah.")

"Tunda kan motar ya karya layin gidan su saleema gabanta ke faduwa......Duk da tanada tabbacin batada Matsala...Amman kuma fargaba ce faal...azuciyarta hawayenda take kokarin boyewa ne...suka zubo mata ba shiri!"

"Kuka faah...Saleema menene kuma...mtwssss duk abinda nayi maki da kuka zaki saka min....!!!?"To ki shiga gida ni zan wuce ban son wulaqanci....!"Lailah tace ranta a bace!"

Toupha muje zuwa fans🥰

****** *******

*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
👇🏻

Fargaba da damuwa tasako Humaira agaba duk saita kara ramewa cikin "yan kwanaki nayanda khamal zai tarbeta inya ganta da ciki tabbas tasan wannan karon bazai mata ta dadiba ita ba komai take ji ba saita yanda zai juya mata baya zai gujeta da itada yaranta tabbas wannan ranar take ji take tsoro tana son khamal tana tausayin kanta tana kuma son haihuwa wayyo Allanta yanzu yaya xatayi rana zafi inuwa quna yanzu in khamal ya saketa yazatayi da bataliyar yaranta?don bata san inda zata nufa dasuba danginsa basa kusa danginta sunjuya mata baya gashi shi bame son yaraba balle yarikesu toko insun rabu taje ga mazajen 4 star's writers ta laluba me dama dama ta Aura wanda ke son haihuwa to aikuma duk gwaurayene 😃 auuu!🤭 ta tuno mmn khalil 😉 tanada miji wataqil ta lallaba gun baban khalil su jone inhar zai riketa da yaranta saita Aureshi ya maye mata gurbin khamal 😎🙄😱 bafa ruwan Bilancy jama.a wannan tunanin humaira ne ato 🏃🏼‍♀

*******

Mafita daya tasamo wacce ta boyeta akarkashin zuciyarta

Kawayenta ta ringa bi awaya tana kiransu domin tanaso suzo ta gaya musu halin da take ciki amma kowacce ta kawo mata nata uzirin

Ita Ashanty wai sunfita Abroad da Ahmad abokin khamal ita kuwa Zee taje kaduna semener

Tabbas tasan cewar komai zai iya faruwa tsakaninta da khamal kawai saita kaddawa Allah komai ta dukufa gaya masa da rokonsa akan yayayyafa mata ruwan sanyi kan lamarinta da khamal

Aranar dayace mata gashinan ahanya yini tayi aikace aikacen gida na gyaran gidan kaf da kuma yi masa girki na gani nafada duk da cikin yafito sosai bata bi son jikin ta ba don bata jin nauyinsa ita din me son aikice gatada tsafta da Kwalliya

Tana daga kwance akan 3 siter tajiyo dirin motarsa tuni ta mike zaune tana kwararo addu,o,i ckn ranta hr izaja,a da tahiya ta karanto har karshensu cikin ranta duk don Allah yadorata akansa

Hoo!kai jama.a ciki saikace anyi na shege 😎😃

Aguje yara suka fita taroshi

Tana jiyowa yana tarbarsu yana dagasu sama daya bayan daya

Da Amal ahannunsa yashigo tana ta masa gwarancinta don bakinta bai budeba

Ta lura sosai khamal yafison Amal cikin yaran

Dayake azaune take bata motsaba tahau masa sannu da zuwa

Ya zauna akusa da ita yana amsawa

Ya ajiye breaf case dinsa akan table yana fadin wash! Madam barka da gida

Tace tana masa wani kallo na soyayya " yww barka Abban twins ya hanya duk gajiyarce hakan.?

Yakalleta da murmushi kan fuskarsa yace mata "walh kam keko ankwashi awanni ajirgi asama gashi dama ansha ayyuka kafin ataho.

"Sannu my husband.

tace tana murmushi harda d'an danna masa kafada alamar tausa

Yana Lumshe idanu yace "yww dear maza kaimin ruwa inwatsa.

tace "airuwan toilet yana xuwa yanzun basaina kaiba fanfon yana kawo ruwa har showa din

ya mike yana fadin "ok ok bari inje indawo inci abinci inajin yunwa

yana shiga toilet ta mike taje kicin ta dauko masa komai dazai bukata takawo kan center table ta ajiye sannan ta zauna tadauki remote tahau canza tasha

koda yafito yasameta inda yabarta yace "kokizo kidan cuda mijinki alhalin nadawo agajiye anya kuwa kina d'okina?

tahau dariya "eh mana Abban twins five mounth fa kayi innace banyi d'oki da missing nakaba ai nayi karya domin ko baby Nabeelah aitasan mamanta na matuqar son Abbanta tasab kuma mamanta tayi kewar Abbanta tana kuma dokin dawowarsa.

yahau fara.a yana gyada kai yace "to abani abinci dai tukunna.

tayi masa nuni da table gashinan komai yahadu ai

yazauna gaban table yafara zubawa kana yaja yatsaya yahararota "au abincinma bazaki tayani da dayaba ko zubawa ko bani abaki ?

ta narke fuska "sorry kafatace ta rike bana son motsata fara ci ina zuwa

yacigaba da xibawa yana gyada kai don baifahimci inda tasa gaba ba

ita duk tsoronta daya kada ta mike yaga ciki su b'ab'e yacanza mata

hhhhmmm to aidai duk wayon amarya sai ansha romonta 🙄☺

Saida Yagama yai hani an kana yadawo kusa da ita yajanyota jikinsa yana fadin "nayi kewar kyakykyawan jikinki yaukam zanyi abinda na dade rabona dashi....shafata yahauyi saikawai yatsaya cak ! Jin tudu agabanta

ya kura mata idanu yakalleta yakalli gaban rigarta take fuskarasa ta canza shine harda daga rigarta yatabbatar dai cikinne da ita take ya turarta daga jikinsa yakalleta ido ckn ido yace "humaira me nake gani kamar ciki ajikinki? Me kenan kikai min ? Meye wannan wai?

da daga murya yakarashe mata tambayar yana nuna cikin nata

duk saita kidime tace "ci...ciki ne.

yahade rai idonsa har jajir yayi don masifa na ciyoshi zai sauke

yanunata da yatsa "humaira abin yawuce gida yaje waje,wato cikinma harda na gayyar sod'i? Bazaki tsaya da ciki naba saikin dangana da kawon dan wani cikin gida kenan ? Nashiga uku khamal, humaira cikin waye ajikinki ?waye yayi miki ciki?wayake tayani kwanciya da mata..... da sauri ta mike tsaye da daga murya ta dakatarshi "ya isheka haka khamal,kada kasake kayimin kazafi cikin jikina nakane,bantaba kwanciya da kowanne namiji ba saikai don haka cikin jikina bana kowa bane sai naka.

"karya kikeyi makira walh yau saikin gayamin me cikin domin kotu zankaiki don asirinki yagama tonuwa kowa yaga cikinki dai yasan yakai watannin danai tafiya nabarki babu cikin donni tunkafin intafi nasan bantaba zuba miki komai amahaifarkiba kinga kuwa ciki ba nawa bane tun wuri kije ma kinemo meshi kafin yaran ma nasa a auna jininsu da nawa agani......

yanda humaira ta kurma ihu tana fadin innalillahi nima Innalillahin nake kira tareda ajiye abin rubutuna ahankali.

****** *******

*Alk'alamin🖋*
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi'u Zango*
*(Nabeelert Lady)*
👇🏻

Ta dad'e tsaye a k'ofar gida tana sharar hawaye kafin tayi k'arfin halin shiga ciki. Tun kafin ta k'arasa tajiyo muryar Umma tana fad'a da alama da Mahaifinsu take.
Chapter 22 · 0% Book details