← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[7/5, 5:34 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👧 *MATA JIGON AL,UMMA👩‍👩‍👧*

👇🏽
*4 STAR'S WRITERS*🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

*Assalamu Alaikum, ina masoya makaranta littafin hausa, ku fito shahararrun marubutan nan 4 Star's writers sun zo maku da wani sabon salo, MATA JIGON AL'UMMA, labari ne wanda zai k'ayatar daku, wannan labari mun sadaukar dashi ga dukkanin Mata, ku biyo mu domin jin abubuwan da labarin ya k'unsa, kada ku bari a baku labari.*

Bismillahir rahmanirrahim

Page - 0⃣1⃣

Zaune take akan kujera 3siter afalonta wanda yasha kayan alatu tamkar baxa.a mutuba

Tagumi ta rafka ta zurfafa tunani har na awa guda

Ahankali ta dawo da kallonta ga agogon dake bangon dakin taga sha daya da rabi na dare 11:30pm ta mike ahankali taje ta kashe kayan kallon dake falon tunda ba kalla takeba kota kalla ma ba wani fahimtar me akeyi takeba sbd damuwar da take ciki

Ta dawo ta zauna asanyaye tahau tunanin mijin nata da akullum shike sakata ackn damuwar nan Amma kuma tana ganin duk wani abun dayake mata da laifinta tunda tun afarkon Aurensu ita ta dage akan shi zata aura iyayanta da danginta sunkishi sbd wani hali dayake dashi amma ita ta nace masa wanda har saida takai karar iyayanta kotu akansa domin babu hannun iyayanta a ckn Wannan kallagaggen Auran datayi wanda tana nadamar yinsa ayanzu don tana ganima bakin iyayene yafadawa auren

Shi dama nasa iyayan yafi karfinsu don sai ana saura sati guda daurin Aurenma yafadawa mahaifinsa mahaifirsa ta rasu sai matar uba wanda baya yi mata magana inyaje gidan basa shiri kwata kwata da ita

Khamal kenan yaro dan kwalisa matashi meji da kansa me gadara nerar da yake da ita

Khamal dan fata ne yanada babban kamfani da yake aikin fata yaransa ke mai hidima da shige da fice akan cinikin fatar daga garin nan xuwa wani garin harkar ta bude masa sosai

Humaira itace matar daya aura yake kuma gasa mata gyada ahannu domin shi mutum ne me akidar turai da son yai fafa amma ita wannan sambaya ga tsarinta

Tun daya Aureta yaiyai da ita akan yakaita tayi tsarin iyali amma taki kwata kwata ta nuna masa baza tabi abinda yake so ba wannan kadai yasa musu rashin jituwa dama kuma yana bin matan waje ta taba kamashi yakawo mata mace har cikin gida tafuta unguwa to akai rashin sa.a tadawo da wuri taga abinda yatada mata hankali mace har kan gadon Aurenta suna masha,a da mijinta

Tun daga sannan taji yafice mata arai amma bata dau mataki ba

Ayanzun hakan zarginta yanaga abinda take tunanin khamal yatafi gun macene shiyasa yayi dare awaje don bai saba dawowa fin goman dare ba

Taso takirashi awaya to amman tana tunanin halinsa zai iya balbaleta da masifar daya mata inta kira yakance mata to inyazo gidanma me zaiyi mata ko tanada iko dashine?

Hakan take gudu shiyasa ta kyaleshi kawai tana dai zuba idon ganinsa ne

Sai shabiyun dare taji dirin motarsa acan farfajiyar gidan

Bacci yafara daukanta sama sama tajiyo kugin motar

Yashigo falan ko sallama babu baiyi zaton xai sameta afalonba

Ta taso ahankali ta karbi jakar hannunsa tana masa sannu da zuwa "amma yau ka dade da yawa ko kabiya wani wajen ne?

Fuskarsa ba fara.a yace "tuhumata kk ko yaya? Inma nabiya wani wajen laifine?ko aikena kikayine? Mmttsss yaja tsaki yawuce bedroom dinsa

Asanyaye ta rufa masa baya tashiga bedroom din nasa

Ta ajiye jakar tasa agefen gado tareda dosana duwawunta gefen gadon tana jiran yafito daga toilet

Saida ya watsa ruwa yafito yaxura jallabiya yakalle da bacin rai "to me xan miki kikaxo kika sani agaba.

Tayi masa shiru kanta akasa

Yaci gaba da fadansa "kinsan Allah inma jarabarki ce ta motsa yau kk kasa yin bacci toki saka aranki babu abinda zaki samu agurina tunda har kinki maganata ayita xama ahakan baxaki kara jin dumin abuna ba gara inkaiwa na waje ita....da sauri ta dago kanta ta kura masa ido

"Kalleni ki kara ba karya nake ba da gasken gasken zan sami jin dadi agurin wata macen ta waje kuma zankara aure nan bada dadewa ba tunda har zansa kiyi planning kik'i amincewa sbd jarabarki ta son "yaya to walh muxuba mugani.

Yana gama fadin hakan yaja filo yakoma falo kan 3 siter

Ta mike ahankali tamkar kaxar da kwai yafashewa aciki

Tazo ta durkusa gabansa cikin muryar kuka tace "plz my one kayi hkr kajanye wannan kudirin naka walh yayi min tsauri dayawa dan ALLAH kabari innayi "yaya biyu saimuyi tsarin iyalin amma yanzu baxan iyaba ina tsoron matsala dan Allah mudawo yanda muke ada...yai mata wani mugun kallo

Yatashi yabar mata gurin yakoma dakinsa yarufo kofar dan karta dawo masa

Humaira ta mike tana share hawaye takoma nata dakin tana tunanin mafita agareta domin baxata iya bin abinda yakeso da itaba Allah yayita da son "ya"ya gashi kuma Allah yajarrabeta da mijin da baison haihuwa yaya kenan …………??

*ALK'ALAMIN NABILANCY LUV💘(Auntyn S&S)🖋*

*******

"Zaune yake cikin maidaidaicin dakin nasa mai dauke da wata yar kod'addiyar katifa da tabarma da yake zaune."Fitilar kwai ce kunne acikin dakin wacce sanadin ta ne dakin ya haska"casbaha ce a hannunsa yana istigfari da salatin manzo (SAW)."

"Da karfi aka hankad'e labulen dakin da yaga jiya da yau ko sallama babu ta shigo hannunta rik'e da kwanon samira da ya sha lamba har ya gaji tuwo da miyar kuka ne dauke aciki,Da saurinta ta dangware masa abincin agaban sa tare da kofin roba cike da ruwa!"Juyawa tayi da nufin komawa dakinta!"

"Cikin sanyin muryarsa ya tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta."Saleema!Saleema!"

"Cikin zafin nama da jin takaici ta juyo tayi masa wani kallon wulakanci!"Ta ce Lafiya Aliyu kake kirana hakan!?"Ko bashinka na dauka!?"

"Lafiya! K'alau Saleema me gareni da zaki dauki bashi aguna!?"

"Shi nagani ai dan ko mutuwa bazata dauki babu ba!"Ka fadi maganar ka dan ina da abin yi!"Saleema ta CE, A fusace!"

"Daman tambayar ki zanyi ina kika je tun safe Har yamma ina cikin gidan nan ina jiran dawowarki amma baki dawo ba? "Sau nawa zance maki ki daina yawon nan Saleema amma sai kiyi biris!"Yanzu naje nayi cefanan miyar ganye kinyi min miyar kuka! wallahi kiji tsoron Allah Saleema ya kamata kiyi karatun ta nutsu ace bakida aiki sai yawon gidajen makota! Ko tara mata acikin gidana ana fadi banza fadi wofi kar ki manta duk halin RAYUWAR da muke ciki kece sila!"Duk bala'in nan ke kika jawo mana sanadin bak'in yawonki da tara Matan banza da kikeyi agidanki tare da kuma kaddara....!"

"Dakata Aliyu kada ka nemi fada min magana!"Ai da Kar ma kace da kaddarar!"Ashe duk karatu naka na banza ne tunda har ka jahilci lamarin Allah, kayi Sabin banza wallahi!"Gobara Allah ya kawota sai dai kace nice sanadi!"Kuma na fika bakin ciki ni da yarana har uku suka bar duniya!"Nagane me kakeyiwa nacin gobarar fito fili kace min Saleema kece sanadin takarduna kudadena da kadarorina!"saboda su suka dameka ba yaranka da suka mutu ba!"To bari kaji..... wallahi yawo yanzu na fara dole naje gidan kawayena na sha jar miya,Na ci naman kaza da kayan dadi!"Me zan zauna yi acikin wannan bakin gidan naka mai hammar tsiya da babu!"Ai gwara na fita makota da abokai na fada masu damuwata na rage zafi!" Aliyu na dade da yin dana sanin aurenka!"Saboda Sam babu alheri aciki! kuma na tsaneka badan gudun tsinuwar iyayenah ba da tuni na bar gidanka na samu mai arziki na aura dan bazan jure zaman wahala da talauci ba!"Kuma miyar kuka ita nake ra'ayi banda lokacin dafa miyar ganye idan zakaci kaci idan baza ka ci ba, kabar shi na zubar ko na baiwa Almajirai!"Dan ni kasan nafi karfin cin abincin gidan matsiyaci marar zuciya irin ka!"Dogon tsaki taja tabar dakin nasa zuwa dakinta tana huci kamar zakanya."Saleema kenan."

Aleeyu kuwa hawaye ne ke bin fuskarsa yasa hannu ya share saboda ya tuna da yaransa da Sadik,siddika,da sultan da yarasa sanadin gobarar da ta tashi agidansa shekara daya da rabi da suka wuce!"

"Zuciyarsa cike take da bacin rai da bakin cikin rayuwar matarsa Saleema!"Wanda akullum banda wulakanci da tozarci ba abinda yake samu agurinta duk da yana bakin iya kokarin sa domin ganin ya kare mata dukkan hakkokinta da ke kansa!"Amma tuni tayi nisa bata jin kira bata ganin kokarinsa sai dai ma kasawarsa da zaginsa da takeyi ita da kawayenta!"Da tunanin ya bude kwanon abincin yaci duk da bawani dadi ne da shi ba."Ruwa ya kora kana ya tashi yana jero nafilfili tare da rokon mafita da Alkhairai agurin Allah tare da rokon samun shiriya ga matarsa abin sonsa, kamar yadda ya saba ba dare ba rana.

"Aleeyu kenan bawan Allah kuma zakin fama mutum ne me hakurin gaske haka Allah yayishi akwai tawakkali yanayinsa yana da sanyi baida fada shiyasa ma Saleema tayi matukar rainashi haka danginsa bata ganinsu da kima tun yana da arzikinsa take musu iko da gadara sannan bai isa yayi musu alheri ba sai aboye tabi ta kanainaye komai nashi ta asirceshi yana shakkarta sosai dan wani abun ma baya zartarwa sai da izininta

Dama tanada idon cin nera duk da alokacin da sukai aure tana sonsa amma son dayake mata yafi nashi sbd taganshi a mota mekyau ne ma yasa taringa saurararsa har Allah yanufa akai Auren.

Kuma koda akai Aurensu ma ba kullum take girki ba sai week end sbd bata so taringa gajiyar da jikinta saboda kada tsufa yazo mata da wuri acewarta kenan.

Sai da tayi yara biyu Saddiqa sa Sadik ne ma kana ta dawo yin girki kullum amma ada kafin ta haihu saidai kullum suna hanyar restaurant

Allah kenan me yanda yaso ga bawansa tun afkuwar gobarar data cinye musu kudade agidan da kadarori suka rasa abubuwa da dama shikenan tafara juya masa baya.

Danginsa babu wanda ke taimaka masa balle sukawo kafarsu gidan sbd Matarsa

Saleema kyakykyawa ce dirinta kadai ke furgita wanda duk yatsira idonsa agurin tana da matuqar kyan jiki bakace ta taba haihuwa ba inka ganta ba laifi tana gyara jikinta
Chapter 1 · 0% Book details