← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 26

Sashe 16

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad yayi masa fada sosai ta inda yake shiga batanan yake futaba har yana ce masa inya gaji da zama da ita to yabashi dama ya aureta shi domin haihuwar yake nema kozai samu ajikin humairan

Wani kishin hakan yanaushi zuciyar khamal

Amma bai nunaba saima nunawa Ahmad da yayi komai yawuce zaije yasamu humairan ya maidata

wannan kalami na Ahmad ya tsaye masa arai don yanada matuqar kishi kuma bazaiso abokinsa ya maye gurbinsa ba gara wani can da ban wanda bai saniba

Abun yaita nukurkusarsa arai

Cikin humaira yashiga wata na takwas tayi nauyi sosai alokacin tafara yan sana,o,i na cikin gida tana kulle kulle kayan miya bushashshe harma tana dorawa su hassana da hussaina suna zaga unguwa don asan tana siyarwa ko za.a zo gida asiya

Mutanen unguwa sunsha mamakin wannan talla na yara tunda sunsan dai babansu me rufin Asirine gidansa da get ga motarsa mekyau kuma sunbar ganin babansu sunsan dai ba mutuwa yayi ba balle ace maraicine yasasu yin tallan

Dama humaira ba ma,abociyar shiga makwabta bace balle suji cikinta saidai kawai suyita tseguminsu su kadai

Ana hakan wataran khamal yazo da yamma unguwar domin yasauko yadawone don yadawo da matarsa tunda yasan tanada ciki har yanzun matarsa ce batayi iddaba saita haihu yanada damarsa

Kicibus sukai da hassana ta dauko talla akanta

Yatsaya da motarsa yakura mata idanu yatabbatar dai hassanar ce yarinya karama tana talla kuma "yarsa tacikinsa lallai humaira ashe tozartashi takeyi baisaniba sai yau tabbas saiya hukuntata saita gane kuranta na abinda tayi masa yakira hassana tajuyo taganshi

Amaimakon tayi murna yarinyar ko ta taho gunsa saima kallonsa da tayi kawai ta zura gida aguje donta gayawa ummanta Abbansu yadawo

Hakanma yataba masa zuciya wato ma tasakawa yaransa tsanarsa kenan tunda ga hassana na gudunsa tabbas humaira bata kyauta masa ba zata gane kuranta ayau.......

*MUNA MIK'A GODIYA GA MASOYA WANNAN LITTAFI NA MATA JIGON AL'UMMA, MUNA MAI BAKU HAK'URI SABODA ZAMU DAKATA DA RUBUTU SAI ZUWA BAYAN SALLAH IDAN ALLAH YA KAIMU DA RAI DA LAFIYA. MUNA NEMAN AFUWAR DUK WANDA MUKA B'ATAMAWA BISA KUSKURE, ALLAH YASA AYI AZUMI LAFIYA KUMA YA BAMU ALBARKAR DA TAKE CIKI. MUNGODE*.

*UR'S*.
*4 STAR'S WRITER'S* 🖋
[7/5, 5:37 AM] Nabila Lady: 👩‍👩‍👦 *MATA JIGON AL'UMMA*👩‍👩‍👦

👇🏽

*4 Stars Writers* 🖊📚

*NABILA RABI'U ZANGO*(Nabeelert Lady)
&
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MMN KHALIL*

*Page* 0⃣8⃣

*MUNA YIMA 'DAUKACIN MASOYAN MU BARKA DA SALLAH, ALLAH YA AMSHI IBADIMMU AMIN, MUN GODE DA IRIN SOYAYYAR KU AGAREMU👏🏻😘*

A hankali khamal yake tukin motar yana jin wani qululun bakin ciki aransa wai "yar cikinsa ce yau ke yin tallan kayan miya! Shi khamal dan kwalisa tabdijan!!da sake.

Yana farking da
Motar yafuto afusace Yashiga ckn gidan yana me kwalla mata kira

"Humaira!humaira!!ke humaira kina inane!?

Humaira tana jiyo muryarsa gabanta yahau dukan uku uku domin tasan kwanan zancen tunda hassanar tagaya mata komai naganin babansu da tayi

Data tuno yanda yai watsu dasu suka shiga wani hali kuma saita dake tsoron data shiga nashi yakau domin koma meye aishine sila ta shiryi kalmomin da zata fada masa inhar yai mata fad'a akan hakan

Yashigo dakin yatararta zaune tsirtsi da ciki agabanta saiyakara quluwa da ganin yanda yasameta da ciki ashe bata xubarba, lallai humaira bata qaunarsa tunda bata bin mgnrsa yasan zaman da zai da ita awannan karon.

Yatsaya akanta yanuna
Yanunata da yatsa yace "humaira meyasa kike so kitozartani,kinaso kixubarmin da kima da darajata a unguwa ke wace irin macece me tonon asiri da bankada?

Ta daga ido takalleshi tace "Kaima wane irin mijine me bankadar asirin mace da gallazawa da rashin tausayi?

Bata karawa cewa kanzil ba tayi shiru kanta akasa

Mgnrta ta kona masa rai baiduba cewar irin wacce yayi bace shin itan ya taji.

Yanuna kansa yace "ni kike gayawa haka?eh lallai aidama ba tarbiyya ce ta ishe kiba tunda baki koshi da tarbiyyarba agun iyaye kika baro gabansu kika biyo namiji duk don kicika burinki na son haihuwar "yaya rututu "ya"yanma mata wanda amfaninsu agunku shine ku dora musu talla dan a wulakanta uba.

ta shaqa amma amma saita dake tace "Eh kwarai kuwa "yaya mata ai abin sone domin *mata jigon Al,umma ne* wata ma nasan ayanzu hakan neman haihuwarsu take ido rufe

Yace " ya isheki haka kibani amsata meyasa kk dorawa hassana tallah nawa hassanar take da zata zama "yar tallah

"Domin rufin asiri agaremu shiyasa nadora mata tallah tunda bamuda abinda zamuci agidan nikuma bazan iya futa yawon bara ba shiyasa.

ya hadiyi yawun bakinsa yace "yayi kyau. Kinkyauta yanzu da iyayena agarinnan suke da shikenan kin tallatasu agari kintozarta musu jikoki..,ta katseshi da sauri

"Hakan shine daidai domin haihuwa tayimin rana kuma bazan daina sontaba don bansan ranar da zatayi min agaba ba.kuma koda iyayanka na garinnan bazanki dorawa yarana tallah inhar basu kula dasuba.

yai mata banza yashige dakinsa ya ajiye dan akwatinsa yai dibi dibi ya fito yakalleta yace "kinshiryi zaman Aure dani?

Tace "Inka shirya nima ashirye nake.

"da ban shiryaba ai da baki ganniba.

"nima da ban shiryaba da ban sanarwa kawata donta gayawa abokinka yanemo kaba.

yaja tsaki yace "daga yau duk abinda zai faru tsakanina dake kada kikara fadawa Ahmad bana bukatar yasan komai akan gidana inba hakaba zaki fuskanci bacin rai.

tayi masa banza yamike yabata guri tabi bayansa da kallo wani kaunarsa taji yana mata zillo aranta

*****

TO tunda yadawo gidan bai nemeta da jin dadin Auratayya ba sabgarsa kawai yake haka itama bata nuna ta damu da hakanba ko shige masa batayi tunda cikinta yatsufa dama sai uzuri

Burinta dai yacika khamal dinta yadawo mata hankalinta yakwanta kuma yana sakar mata fuska yaranne dai bai fiya jansu ajikiba gara gara baby Amal ma yarinyar tanada masifaffen kyau kamar balarabiya yakan jata ajikinsa yai mata wasa

Allah yasauki humaira lfy ta zankado jaririyarta mekyau ainun kamarsu daya da khamal kamar antsaga kara har dimple din

Ba laifi ya yaba da kyan babyn domin yaga yanda suke kama dashi Amma duk da hakan yafi jin Amal Aransa

humaira tafahimci khamal yafison ta haifi Namiji shiyasa baya nuna rawar jiki inta haifi mace itako tana son "ya "ya mata domin *MATA JIGON AL,UMMA* NE

bai rageta da komaiba na cikin gida saidai kuma datayi Arba,in din baby Nabeela taringa dokinsa Amma shi baya baya yaringayi da ita data tambayeshi dalili saiyace mata "Tsoro nake kada inkwanta dake kisamu ciki. Tunda kedin dai kamar kaza kike kuma planning baya karbarki.

taji zafin kalaminsa Amma bata nuna masaba Saidai taci Alwashin bazata yi wani planning ba gara tagama haihuwa tun yanzu da yarintarta agaba ta huta kuma ta tabbata wata ran yaranta ne masu jinkanta fatanta Allah yaraya mata su.....

**** ******

*Alqalamin Nabeela Dikko*🖊
👇🏻

"Misalin Karfe 6:00pm mai adaidaita ya sauketa kofar gidan,Tayi kyau matuka fuskarta da jikinta ya shaa gyara sai sheki sukeyi,An shaa kunshi da kitso mai kyaun gaske,"A hankali ta fito ta sallame ya wuce wata lafiyayyar mota idonta ya hango mata gefen kofar gidan,Hadiye miyau tayi acikin zuciyar ta tace "Allah ka kai A'i ga rogo."Koh taa wane hamshaqe ce oho,da yake bayan motar take hangowa ba gabanta ba."Direct kofar gidanta ta nufa."Budewa tayi ta shiga ba kowa bace face hajia saleema Engr."

"Aliyu da ke gefe zaune cikin rantsattsar motarsa yana shan a.c ya fito zuwa gidan dakinsa ya shiga ma adanar documents dinsa ya duba tsaf ba takardun gidan, dakinta ya nufa."

"Zaune ya sameta tana waya,Da sallama ya shiga dakin,Wani kallon banza da tuhuma ta bishi da shi!"Cigaba tayi da wayarta da bai fahimci komai acikin zantukanta har ta kare!"

"Tsaye yake ya jingina jikinsa ga ginin dakin tare da hade hannayensa yana fuskantar matar tasa saleema tare da nazari akanta idan mutim ya ganta yaga cikakkiya kuma kamilar mace amma fah a fuska,"Domin ba daga nan take ba!"saboda saleema halayenta sam ba na kirki aciki!"

"Cigaba da danna wayarta tayi tana cin chewing gum."

"Saleema daga ina kike batare da izininah ba!?"Aliyu ya ce cikin taushin murya."

"Daga inda ka aikeni!?Ni ban tambaye ka a ina ka kwana ba sai ni kake da bakin tambaya daga ina Nike! to bansani ba!"Saleema tace cikin fushi!"

"Aleeyu koh mamakin karfin hali irin na ta yakeyi tana magana kai tsaye ba tare da Jin wata fargaba aranta ba!"

"Ya ce naji kin kyautah saleema!Kin nuna min ba ni da wata qima da zaki bani hakuri bayan kinyi min laifi!Sannan ban cancanci ki nemi ixini na ba!"Idan zaki fita ko!?"Wai me kika mayarda ni ne!?Bawanki ko kuma wani sakarai!?Talauchi ai ba hauka bane, da zaki kyamace ni hakan akanshi kuma ba gareni farau ba!"Ina son kisani wallahi hakuri na ya qare!"Iskancinki da rainin hankalinki ya isheni!"Kodai ki dauki matakin gyara ko kuma ni nayi maganin abin daman darajar iyayenki da yaran mu ne nake dubi ina raga maki ina hakuri da ke nagane sam bakisan da hakan ba!"Tausayinki nikeyi da iyayenki saleema nayi maku komai arayuwa amma ke bakida buri irin kika kin juya min baya kin wulaqanta in!"To baki isa ba!Abinda kinkayi min jiya da yau yazama na karshe agareki vazan sake lamunce hakan ba!Bai kamata ki manta halacci na gareki ba!Ki tuna ko ke wacece!........."

"Dakata!Dakata!!Aleeyu! saleema tace tare da dakatar da shi da tafin hannunta , mikewa tsaye tazo daidai inda yake ta tsaya,Ta ce "Nagode Aleeyu basai ka tuna min koni wacece ba nasani sarai!"Wato an turo ka kaxo ka wulaqanta ni!Ka ci mutuncina!Kai min fade koh domin kawai ka taimake mu!?To Alhamdulillahi cikin tufin asiri kagane ni ba wanwar nike yawo ba suturata ba kai ka ganni ka ce kanaso ba dole akai ma ba!"

"Kuma ko yanzu zan fita alokacin da nake ra ayi nadawo sanda duk naga dama sai me!?"

"Taaa taas taas taji saukar mari kamar daga sama!"Idonsa yayi jajur zuciyar maza ta motsa!"Jawota yayi ya hade da bango sai fidda ido take cikin tsoro ta ce"macuci sai Allah ya saka min ka sakeni mani wuya mana ka gani!"

"Bazan sake ki ba saleema sai kin sanarda ni ina kika ajiye min takardun gida!"Naduba bangan su ba!"

"Cikin firgici ta ce nasani ne!? ko kabani ajiya ne!?"
Chapter 16 · 0% Book details