← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yadda reaction din safara ya canxa dajin karar wayar ,gamida irin kalamar soyayan dake cikin wakar ringing tone din yasa mufida tasha jinin jikinta,dan haka kallo daya taima lambar ta haddace ta akanta ,sannan tai picking call din kamar dai yadda Dr ta umarceta dayi,Allah ² mufida take subar wajen danta samu ta gabatar da kanta ga Dg Anas, amma sakamakon gwaje gwajen da aka sakasu ga kuma layi da suka tarar,dan ma honorable yana nan bai tafiba, sai bayan azahar sannan suka samu suka koma gida,honorable yaso ya kebe da Mufida dan su samu sundan fahimci juna, amma Sam taki bashi dama, sai cemai tayi ta gaji yanxu ya dawo gobe, hakannan dole yabi umarninta dan azauna lafiya.

Mufida ta zayyanawa Alawiyya dukkan abinda ya wakana a waya, hakan nema yasa ta jinjinawa kawartata sosai da wannan na mijin kokarin da tayi,sannan ta shawarceta da kada ta kirashi yau ta bari sai gobe adaidai lokacin da take ganin matarsa na wajen aiki, hakan kua akayi.

Mufida dai dan zumudi da jin dadi dakyar ta samu bacci ya dauketa,amma duk da haka xuciyarta ta kasa samun natsuwa dan batasan wane irin tarba zaima soyayarta ba

Misalin karfe goma na safene mufida ta lalubo lamvar Dg a wayarta,Wanda tuni ta sanya masa suna da *HEART COOLER* a wayarta,gabanta na faduwa tadai daure ta dannan alamun kira,sannan ta kara a kunnenta,kirjinta yana ta bugu fat fat kamar xai fado kasa,. ASSALAMU ALAIKUM taji an fada daga daya bangaren.

Muje xuwa😃

******** *******

*Alqalamin Nabeela Dikko* ✍🏻
👇🏻

"Mallam Siddiku Shantali (mahaifin Aleeyu)Da Malam Halliru Ya'u (Mahaifin saleema)Duk suna zaune acikin unguwa Daya( Rijiyar Barga Argungu)Kasancewar akoda yaushe suna haduwa a massalici ana zaman zumunci da mutunci ga kuma maqotaka yauma sun hado a masallaci bayan an kammala sallar subahin basa fitowa sai rana ta haska wajajen 8:30am hakan."Nan ne bayan sun gaisa Malam siddi ke jajantawa mahaifin saleema dangane da duk abinda ya faru komai bai rage ba dangane da jawabin da Inna shatu(matarsa)Ta labarta masa a Daren jiya Wanda Aleeyu ya shaida mata har sayarda gidansa da saleema tayi!."

"Malam halliru ko tun yana tsaye har yakai zaune saboda mamakin Halin yarsa!"Hawayen takaici suka zubo daga idanuwansa!"Yanzu da matuncinsa da iliminsa amma ace yau yarinyar gidansa ce ke ta asa agidan miji!"Duk tarbiyar da tsare gida da yake nuna masu!"Baisan da wace kalma zai bawa mallam siddi da dansa Aleeyu hakuri ba!" saboda kan shi ya daure sosai!"To ina saleema!? dan shi baiji motsin saleema agida ba!" kuma ko mahaifiyarta baiji tana zancen ba."Ran shi ya sosu dan shakka ba yayi saleema tayi asarar miji nagari kuma bazata samu kamar Aleeyu ba."

"Murmushin Wanda yafi kuka zafy mallam halliru yayi tare da share fuskarsa!" sannan ya ce,"Mallam siddi ko da baka fada min wannan maganar ba nasan saleema ce batada gaskiya domin ba ta da kirki!"Yaron nan Aleeyu yayi matukar hakuri da ita,Badan shi bane da tuni an fara mata kirgar aure!"Dan Allah kada kuga laifinsa kuma mun gode Aleeyu ya cika d'a nagari yanada mutunci nasan cewa yagaji da halin saleema ne kuma hakan da yayi shi yafi dacewa toma uban wa tasaye da kudin gidan!?!"Shiyasa banganta ba!"Saboda tasan cewa zan iya karyata a gidan nan!"Shi ne dalilin kin zuwanta!"Amman watakila tana gidan kanwata Bintu(Gwaggonta) yanzun nan zan bincika idan na koma gida!"

"Mallam siddi yace kasan yaran yanzu Idan ka haife su baka haifi halinsu ni kaina raina baiyi dadi ba saboda Aleeyu ya yanke hukunci batare da sanin mu ba!"Halin yaran zamani!"Kenan abin takaici ba gyara bare ta koma.... !"

"Haba mallam siddi....aiko da akwai gyara a auren....wallahi saleema bazata koma ba!"Sai dai na aura masa kanwarta.....ko yanzu Da ace duk qannanta basuyi aure ba da zan ba Aleeyu auren su!"Dan ni yanzu na yafe saleema kuma na debe ta acikin yaran....."Dakata mallam Halliru kar fushin zuciya ya kai ka ga barna kaimata fatan shiriya kada kai mata baki Dan Allah!"Mallam siddi yace cikin yanayin tausayi..."

"To bakomai nagode Malam siddi Dan Allah ayi hakuri kuma duk inda takai kudi gidan Aleeyu za a mayarwa masu su!"Ya koma gidansa!"Ba komai Aleeyu ya yafe gidan da kudi ku bar mata nan dai mallam siddi ya zayyanewa Mallan halliru irin abin arzikin da Abdul Hafeez abokin Aleeyu yayi musu har sabon gida da motar da yabashi."Murna mallam halliru yayi tare da masu fatan alheri!"Daga nan sallama sukayi da juna kowa ya nufi gidansa."

"A zuciyar mahaifin saleema yana Allah wadai da halayenta saboda neman tsiya ga arzikinsu ya dawo amma takasa zama taci arziki ta gwammacewa ta dawo gida da zama."Da haka ya shiga gidansa cikin bacin rai batare da bata lokaci ba ya labartawa Luba(mahaifiyar saleema)komai da ke faruwa saboda yasan cewa ko ita batada labari Dan saleema ko shawara batayi da uwarta bare qannanta!"Inna luba da kukanta da hawaye ba kalar zagin da batayiwa saleema ba!"Saida mallam ya koma bata hakuri!"Ta ce mallam barni nayi kukana mana meyasa saleema bata gane abinda muke mata dubi arayuwa!?Yarinya sai son shagalin duniya kamar bazata mutu ba!"Wallahi ta cuce mu akullum burin shi ne yaranmu su kasance sahun farko acikin jerin *MATA JIGON AL'UMMA* amma ita taki, ta taka muhimmiyar rawa arayuwar gidanta,da ta al'umma!"Yanzu da ta kashe auren uban mi zatayi agidan!"Tazo ta zauna wallahi daga yanzu bazan qara komai ba agidannan matukar saleema tadawo da zama aciki sai na azabtarda ita kamar baiwa!"Sai ta gwammacewa kidi da karatu...."Shegiyar shedaniyar yarinya da batasan arziki da mutunci ba!"Yanzu tana ina mallam....!"Shi ne nake tunani ko tana gidan gwaggon yara!"Hakane bazata wuce can ba!"Yanzu ki shirya muje har can mu ci mutuncinta!"To mallam kafin nan ka karya mana...."Bazan iya cin komai ba luba bakin ciki saleema ya kosar da ni!hakuri zamuyi mallam Allah ya shirya mana."Ameen luba ki sauri ki fito muje...."To yanzu zan shiryah!..luba tace"Tare da shiga dakinta domin ta kimtsa..."

"Bayan Aleeyu yayi wanka shiryawa yayi cikin yadi kaftan miyon goro da hula."Yayi kyau matuka,Sai rama da yayi acikin yan kwanakin nan,Ya dade yana nazarin kan hukuncinda Babansa zai yanke masa domin yana da tabbacin inna ta sanar masa komai zuwa yanzun."Gidansa ya rufe ya fada mota direct wurin sana'arsa ya nufa da aqalla yau kwanan sa uku bai tafi ba."

"Sallau na shan rake ya hango mota shakka ba yayi oga Hafeez Dan Sudan dan hakan yake kiransa,Da sauri ya qarasa jikin motar yana washe baki,bayan anyi parking tun kafin ya bude motar sallau ya bude masa sai dai me Aleeyu ya gani...."

"Baiyi mamaki ba Dan yasan cewa aminin juna ne da oga hafee."

"Murna sukayi sallama da gaisuwa kana sallau yace mallam Ali lafiya ko kwana biyu!?"Wallahi ina batun nafara neman gidanka na binka ko kana lafiya kasan halin rayuwa..."

"Lafiya qalaw Malam sallau ya kokari ya aiki."Inji Aliyu.

"Da godiya,Ali ina maigida na ga yau kai kadai ne."

"Hafeez ya koma Sudan saidai wani satin zai dawo daman wucewa zanyi nace bari na biyo mu gaisa."

"Nagode mallam Ali.Ohni sallau dare daya Allah kanyi bature jibeka Ali kmr bakai ba kaga ikon Allah."Yanzu kaida wankau sai kallo."Ya Allah kace mu zamou."Kai kuma Ali Allah yaqara arziki ya kauda kaddara!"Sallau yace yana farinciki."

"Ameen sallau nagode sosai,Yanzu zan wuce sai naqara dawowa Aleeyu ya ce yana tausayin sallau!"Dari biyar ya zaro a aljihu yabashi cikin kudin da Hafeez ya barmasa yana shan
Mai a mota."

"Da murna sallau ya karba yana godiya,Ya ce Ali jeka ka zauna ga. alama baka koma wanke motar nan ba yanzu zan wanketa Dan tayi datti."Ba yadda Aleeyu baiyi ba Dan sallau yabar motar amma fafur yaqi sai da ya wanketa tatas,sannan sukayi sallama Aleeyu ya nufi gidansu sallau ya koma bakin aikinsa."

"Duk abin nan da akeyi fatty qawar saleema batada labari ko yanzun nan ta kira wayar saleema da laila duk basu daga ba hankalinta ya tashi matuka,motarta ta hau direct gidan saleema ta nufa wayam bakowa a rufe!"Akalar motar ta juya zuwa gidan laila ko zata same su a can."

"Inna Luba tana shirin sanya hijab,sai sukaji saleema da lailah...da sai yanzu suka yanke shawarar shigowa daga ciki.."Mallam siddiku ne ya amsa musu fuskarsa a daure!"Wani mugun kallo inna luba ta watsa musu mai dauke da tuhuma!"

"Nan take gaban saleema ya dinga dukan uku-uku!"Kar dai aikin Malam baiyi ba!"Wayyo na shiga uku ga inna da Baba!"Tace azuciyarta," afili ko sassauta murya tayi tace lailah na shiga uku!!!"

Lailah ta kama hannunta ta rike tace "Ki cire tsoro a ranki saleema bazasu iya yin komai ba, ke dai ki zuba ido ki kallo ai mallam baya aiki ya rasa ciii........."

*Caap wasa farin girki,abin mamaki baya qarewa ace lalacewar zamani har ya kai yara suyiwa iyayensu asiri!? Sanadin furucin da lailah tayi ne yasa alqalamina subucewa saboda tsoro!da mamakin son zuciya irin nasu. Kubiyoni domin jin yadda zata kaya*.....

****** *****

*Alk'alamin*
*Nabilancy Luv💘*
( *Auntyn S&S*) 👇🏻

Duk yanda humaira taringa ihu tana bashi hakuri akan kada yatozarta ta kada yai mata sharri Amma khamal bai kulaba yatoshe kunnuwansa yaringa ci Mata mutunci yana cewa tafito tafitar masa agida DA ita da yaranta domin bazai zauna DA fasika ba. Maza tundare bai mataba waitaje tanemowa cikin jikinta uba

Matuqar tausayi Humaira tabani

Ya nunata da yatsa "nabaki awa daya kitattara komatsanki da kika tabbatar nakine kifucen daga gida kafin nadawo kada kitaba abinda nasiya da kudina iya wanda yazama naki kadai nace,inko na dawo natarar baki futaba walh kinji na rantse ba sani ba sabo sainasa anci mk mutunci domin da "yan sanda zanzo

Yana gama fada yai waje

Ta tattara yaranta ta rungume tana kuka ranta na mata suya

Bata taba jin tsanar khamal ba sai yau bata taba nadamar zaman Aure dashiba saiyau dayai mata sharri ,tabbas da ace tanada inda xataje tazauna taji sanyi aranta da tatafin kamar yadda ya bukata

Awa biyu da futarsa sai gashi yadawo da motar yan sanda tadauka wasa ne abun tadauka fada kawai yayi ashe har ransa ne

Kawai saijin tayi sunshigo har ciki sunbata izinin futa cikin minti talatin suna jiran tafuta surufe gidan

Shi ko kallonta baiyiba yadauki abinda zai dauka yafice yabarsu da ita

Yaran sukaita kuka suma domin su twins sun dan fahimta
Chapter 25 · 0% Book details