← Book details Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 26

Sashe 19

Mata Jigon Al_umma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mufida ce ta shigo harabar inda ake duba marasa lafia hannunta rike da mahaifiyar tata,ga mamakinta taga mutane sun cika wajen dankam ko wajen xama babu ,mamaki ya kamata,hakan ne yasa ta gaza hakura ta tambayi wata mata dake jingine jinkin bango,dan itama ko wajen zama bata samu ba,sakamakon cinkoso,

"Baiwar Allah lafia naga mutane haka dankam a wajennan?

Matar ta bata amsa da Fadin

"Wata likita yar kasar Sudan ce taxo tana duba marasa lafiya kyauta da km magani shima kyauta,idan kuma aikine shima kyauta zatai maka,banda kudi da kayan abinci da take rabawa,km ta tabbatar mana da cewa ko zatai kwana 10 ne sai ta gama ganinmu dukkanmu,dan haka kije can da sauri adauki sunanki dan ankusa rufewa kiyi sauri,

Mufida cikin zuciyarta tace tab wlh baxan iya bin wannan dogon layinba,kawai dan magani kyauta ta tabe bakinta,ana hk Dr safara ta fito daga dakin duba marasa lafiya dan yi musu bayanin zatatafi yin sallah,

Dago kanda mufida zatai tai arba da kyakyawar fiskanta,aikua gabanta yayi wani mumunan faduwa kirjinta ya kama bugawa fat fat,kan kace me taji jiri na neman kayarda ita

Muje xuwa......

******* ********

*Alqalamin Nabeela Dikko* ✍🏻

👇🏻

*Alhamdulillah Ina tayaki munna kammala Degree dinki Amini Rahma m sani Allah ya sanya albarka ameen* .😍

''Bayan sallar ishaa ya nufi gidan su ya samu duk ahlin gidan na tsakar gidan suna cin abinci."

"A ladabce ya gaida iyayen nashi kana ya zauna kusa ga mahaifinsa."

Dubansa ya kai gare shi yace"Aleeyu, Abdoul Hafeez ya wuce koh?

"Eh,Baba ya wuce munyi waya ya sauka lafiya bayan magrib nan, yace agaishe Ku."Inji Aleeyu."

"Masha Allah,muna amsawa yasha hanya ai,Amma ya naganka kamar bakaji dadi Aleeyu?Ko rabuwa da abokin ne!?Baba yace cikin kulawa...."

"A'ah Baba tun dazu nake fama da ciwon kai daman nace bari nazo na ganku tun fitar mu da Hafeez ban dawo ba!"

"Hakane ka kyauta Allah yai albarka."

"Amin Inna ta ce tare da yiwa Naja umurnin takawo yayanta abinci da abin sha."

"Cikin ladabi ta amsa ta nufi kitchen din domin zubo abincin...."

"Da zolaya baba yace"A gaskiya Aishatu bakya kyautawa saleema kullum cikin kiyon Aliyu kike sai dai idan baizo gdannan ba,Yanzu kin kafa dura masa abinci kamar tuni baki yaye Dan naki ba..."

"Inna ta amshe zancen tana dariya tace"Kaji Malam da son tsokana yo matar tasa ab inci take dafawa ne!?Ai gara ya ci ya koshi nikam bana son wasa da yunwa yanzu ulcer ta cinye hanjin mutim."

"Aliyu murmushin jin dadi yayi saboda yanda inna ke kulawa da shi tamkar ita ta haife shi tabbas ta maye masa gurbin margayiya mahaifiyarsa."Fatan sa ya kyautata masu a yanzu."

"Naja ce ta katse masa tunani ta hanyar ajiye masa abinci tuwon farar shinkafa da miyar danyar kubewA sai qamshi ke tashi,Kofi dauke da fura mai sanyi da pure water,Cikin sanyi tace Yaya ga abincin..."

"Yawwa Naja'atu nagode."

"Wani irin taji yadda yau yacika sunanta complete sabanin Naja!"Mikewa tayi da durkushen ta nufi dakinsu saboda ba kasafai take zama idan yana awuri ba,Saboda kwarjininsa da kuma tsoronsa da takeji duk da yanzu ya daina takurata!Amma Sam takasa sakewa da Yaya Aleeyu."

"Abinci ya fara ci suna dan taba hira da iyayensa cikin raha da jin dadi har ya manta bakincikin da saleema tasa shi dazun....."

"Mai gadin gidan Alh.Idris Dan canji,ne ya tarbe Saleema cikin munna yana gaida ita kmr yadda suka saba Inda har 200/500 tana bashi dan kawai karya da nuna ita watace,sai dai yau Sam baiga fuska ba murtik Hajiyar ta shigo gidan ba fara ah duk da yana washe mata bakin kamar gonar auduga,komawa yayi mazauninsa aransa yace yau kam ba rabona ajakarta!"Cikin gidan ta isa knocking tayi akofar falon wata kyakkyawar yarinya da bazata wuce 7yrs bs, ta bude kofar,da fara arta tace Oyo yo Anty saleema."Miemah ya kike!?Normal Anty."Yawwa mummynku faah!?Tana sama a bedrum,Yawwa bara nasameta saleema tace tare da qarasawa saman."Wacce aka kira da miemah kuwa cigaba tayi da kallon series dinta a go t.v(Hattara iyaye bai kamata mu dinga barin yaranmu na kallon kowane station da suke ra'ayi ba!A matsayinki na uwa kamata yayi ki kula da abinda yara zasu kalla suyi koyi da addini ko al ada da kuma tarbiyya."Stations na addini irin su sunna t.v yadace kibari yaranki su dinga kallo bawai waqe2n banza,films da series ba Kar mu manta *MATA* MUNE *JIGON AL'UMMAH* idan al'ummah tayi kyau ko ta baci mata ne,Ita mace makaranta ce,Gurinta ake daukar darasi shakka babu *MATA JIGON AL'UMMA* NE Allah yasa mudace Amin.)

"Ko sallama batayi ta fada dakin,Zaune tasameta a dressing mirror tana makeup."Zaunawa tayi gefen bed din!"Haba malama ni har kinban tsoro Allah! kingama yar halak zancenki nike azuci yanzu nan nake shirin na kiraki."Yadai tafiya yanzun nan lafiya saleema!?"

"Mtwssss wallahi lailah kin cika zancen haushi ya zaki ganni hakan ynzu da dare har kike wani tambayata ko lafiya...saleema ta qarasa zancen tana zubda hawaye!"

"Kutumelesi!Saleema meke faruwa kuka fa!?Kinga sanarda ni Dan Allah!"Mutuwa akayi ne!?lailah ta tambaya!?"

"Ya sakeni!Ya sakeni...!!!wai nie! Aleeyu zai saka!Laila bayan nasan yana mugun sona!nima wallahi ina son shi kuma ina kaunarsa aji ne,Nike jamasa irin namu na mata masu ajidomin naga yana sona kwarai da gaske!Amma duk abinda Nike masa ina sane kuma inajin tausayinsa watarana, raina ni ne banaso yayi,shiyasa nike wulaqanta shi...."

'Haba!saleema kiyi shiru kada kanki yayi zafi ga alama kin zauce naga kin shiga rudu kamar bake ba kodai Aleeyu da abokinsa Hafeez din sun asirce ki yanzu akan namiji kike wannan sambatu ko mijin ma faqiri irin Aleeyu matsiyaci ai wannan abin murna ne wallahi kin rabu da cuta!"Kinga ki kwantarda hankalinki wallahi tafi nono fari yo sai me Dan ya sakeki shine autan maza!?Ko yana hana wasu suce suna sonki!?"Mtwsss ni wallahi har kin bani mamaki!Ni na dauka wani abu ne yafaru da ke!Ki kwantar da hankalinki Allah zai baki Wanda yafishi komai,Karki manta *MATA JIGON AL'UMMA* ne ba ayi sai damu muke fada aji ako ina,Ga Alhaji gobe ko jibi ma zaku hadu Allah ya daidaitah ki debe haushin wancan banzan! "

"Hmnnnnn......Lailah bazaki gañe ba!Bantaba jin ina sonsa ba sai yau!"Inji saleema da ido yayi luhu luhu tana shafe majina!"

"Ke saleema ki nutsu tsumagiyar saki ce ta dakeki!"Amma komai zai wuce!"

"Ta Yaya lailah!?bayan kinsan halin iyayenah sunfi so da kauna da ganin mutuncin Aleeyu fiye da ni !"Yanzu me zance masu yafa sakeni kuma har duka ukun......wayyo nashiga uku laila....ko daya bai rage ba!"Saleema tasake fashewa da kuka."

"Da kyar lailah ta rarrasheta tare da bata tabbacin gobe zata rakata har gidansu gurin iyayenta domin sanarda su halinda ake ciki,sun shirya karyar harda karerayin da zasu Kare kansu"Abinci marar nauyi da drinks lailah ta umurci Kande mai aiki takawowa saleema wacce hankalinta baya jikinta,Bata wani ci sosai ba ta ture Dan va abinda ke mata dadi a yanzun!" shirin kwanciya tayi da yake dare yasoma sun yanke shawarar takwana anan gidan har da safe!"Sallama sukeyi da lailah ta wuce sashen alhajinta tana jiran dawowar sa da sai wajajan dayan dare ko biyu idan antashi club nasu na alhazai yake dawowa."
"Ko ta kan yartah miemah bata sake yiba domin ta riga da tasaba duk lokacin da ta gaji da kallon kashewa takeyi ta wuce dakinta..."

"Bayan ya ci abinci ya koshi yayi hamdala,"Haramar wucewa gidansa yakeyi sai Baba yace to ka gaida saleemar."Sai da safe."Gabansa ne ya fadi saboda sam ya tsani ko jin sunanta!"A hankali yadawo ya zauna Dan sam ya manta bai sanarda iyayensa meke faruwa ba!"Boye masu ba alkhairi ba ne!"Cikin sanyi ya dukarda kai yace"Baba...! kuyi hakuri na yanke hukunci, batare da umurninku ba,dazu munsamu sabani da saleema har na saketa.....!"Saboda nagaji da halayentaaaaaa......"

"Innalillahi wa inna ilaihir raju un!Aleeyu saki fa! Kana hauka ne!?Yazaka saketa a wannan lokaci ko Dan kaga arzikinka yana neman dawowa Aleeyu, bayan kunsha wahala,da jarabawar rayuwa tare!?Wallahi maza da sauri Kayi gaggawar mayarda matarka ko ka hadu da fushina....!Fuuuuuu baba ya wuce daki yabar inna da Aleeyu wurin batare da ya qara saurarensu ba!."

"Tace Aleeyu kayi kuskure babba!"meyasa ka saketa!? sai kayi hakuri mana kowa yasan ai halinka ne!"Yanzu ina son kaje ka nemota gidansu kabata hakuri ka maidata ai lokaci vai wuce ba kuma aure rai gare shi!"

"Inna babu gyara aurena da saleema!" kuyi hakuri...!"nan ya zayyane mata zare da abawa,Tun farko har karshe, har zuwa gidansa da saleema ta sayar!!!!"Inna Saida tayi kwallah Dan tausayinsa, tace tashi tafi abinka zan shawo kan mallam, Allah yai ma albarka lalle kai abin tausayi ne Aleeyu shakka babu." da ciwon hawa jini ya kamaka yayi ajalinka to da bamu San cewa matarka ce sanadi!."Allah ya tsare gaba."

"Ameen Inna nagode da fahimta ta da kikayi sai da safe,."Tashi yayi ya wuce."Inna tace to Allah ya kaimu ka fito da wuri kai Karin kumollo, tabarmar wurin ta nade hade da jimamin hali irin na saleema,da kuma tausayin Aleeyu tare da yi masa fatan samun wata macen tagari, dakin mallam, Inna ta nufa kai tsaye domin ta bashi hakuri kuma su tattauna!".Naja da ke kwance adakinta sai sharar kuka takeyi harda ajiyar zuciya domin tausayin rayuwar yayanta Aleeyu domin duk bayanin da yayi ma Inna taji su sarai a kunnenta don kuwa akofar dakinta ne suke zaune."A fili ta furta tabbas Anty saleema tayiwa kanta ba taci akira acikin sahun nan na "MATA JIGON AL'UMMA" ba!"Tunda har tayi saken rabuwa da namijin kwarai mai kyau da addini kamar Yaya Aleeyu......!"

Toufah muje zuwa fans😍

******* ********

*Alk'alamin🖋*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
👇🏻

Saida Baby Nabeelah tayi wata uku ana hudu kana Khamal yatunkari Humaira da sha.awarsa

Taso ta zille masa don ta nuna masa itama macece amma saita kasa domin gani tayi zataga samu taga rashi

_AMMA DAI HUMAIRA KINBADA MATA_🙄

Tundaga wannan rana kuma sai suka jone tazage gurin kyautata masa haka shima yamance da komai amma kuma baya kuskurewa wajen ajiye ajiyarsa amararta, awaje yake zubarwa don yagama Haihuwa acewarsa

Itako yin hakan dayakeyi ko ajikinta domin ko ahakan Allah yabarta ta gode
Amma tasan duk wayon kaza sai ansha man ta.

******
Chapter 19 · 0% Book details