Sashe 9
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ana kokarin yin sallar isha'i muka isa gidanmu muna zuwa ya kalleni cikeda so yace "zanyi traveling amma dai za muyi waya, ki boyeta kinji?"
"To shikenan sai ka dawo" nafada tareda dibar kayan nayi cikin gida ina tafiya ahankali.
Lokacin da nashiga Ummi tana salla dan haka na ajiye kayan a falo nashige daki naje nayi alwala sannan na boye wayar da yabani acikin akwatina nadawo falo nayi salla.
Bayan na idar ne na fara nunawa mama kayan, murna mama tafara 'ta karbeki hannu bibbiyu kuwa?".
"Eh mama, ta karbeni sosai ma"
Dariya mama tayi "to ai gashi nan ta hadoki da kayan kwalliya yadda zaki tayiwa danta kwalliya" dariya nayi bance da mama komai ba muna nan zaune abba ya dawo, nan mama ta nuna masa kayan amma abba baiyi murna ba sai fada ma da yayi wai danme zan bi salim gidansu shi baya son wannan sakarcin kar nasake zuwa nan gaba koda wasa saboda wasu samarin suna amfani da wannan damar suna bata yara, ajiyar zuciya nayi jikina yayi sanyi sai a lokacin hankalina ya tashi.
Ina komawa daki nafara kuka nadade ina kuka sannan nayi shiru na dauko wayar da salim ya bani na kunnata, massages dinsa ne suka yita shigowa rututu na kalaman soyayya daga karshe ya kirani mu kayi hira ya kwantar min da hankali cewar maganar aurenmu fa ta na nan kar na daga hankalina.
Tun daga wannan lokaci muke waya da shi a boye tuni har na warke daga abinda yayi min, kuma ko Hawwa kawata ban bari ta saniba.
Bayan wasu lokuta masu tsawo kamar watanni biyu har lokacin salim bai sake zuwa gidanmu ba a cewarsa tafiyar da yayi har yanzu bai dawo ba mama ma tasha tambayarsa sai nace mata yayi tafiya ne.
Kiba na danyi sannan sai nake jin kasala ga kwadayi da nake fama dashi, shinkafa kuwa a duniya ji nayi na tsaneta daga na ganta sai naji hankalina ya tashi.
Yau da safe bayan nayi shirin sch mama tace min ga tea nan da wainar kwai, "mama bana son wainar kwan nan, idan naje sch zan siyi awara naci"
"Yau bakya son wainar kwan?
To Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo"
Fita nayi nabiyawa hawy muka tafi makaranta muna tafiya ina fada mata yau awara nake sha'awa gashi yanzu bana son ganin shinkafa, daga ni har ita bamu zargi komai ba da haka muka karasa sch.
After first period second period na shiga malamin mathematics dinmu ya shigo, ina jin kamshin turarensa take naji cikina ya fara juyawa numfashina ya fara yin sama, da gudu na fita gaban class na fara sheka amai kamar wacce zata amayar da hanjin cikinta, hawy ce ta biyoni ta rikeni, sai kwara amai nake kafin nagama har na fita hayyacina hakan yasa hawy ta kira yan bencinmu suka taimaka mata suka kaini clinic din makarantar, nan aka kwantar dani aka fara kara min ruwa.
Nadade ina bacci kafin nafarka duk bakina babu dadi, hawy tana zaune kusa dani lokacin an kusa tashi daga makaranta, antyn clinic dince ta shigo ta kalleni "sannu kin tashi?
Kinada aure ne?" Ta bambayeni
"A'a" nabata amsa
"Yaushe rabonki da al'ada?" Ta sake tambayata
Tunani nafara yi rabona da period tun kafin salim yayi min wannan abun dan lokacin ma kwanana biyu da gamawa hakan ta faru
"Za akai 2 months" nafada ina kallonta
Kallona tayi sosai "akwai matsala kenan" tafada tareda juyawa har takai bakin kofa tasake juyowa tace "zaku iya tafiya tunda kinji sauki"
Tashi muka yi nida hawy muka fita lokacin an fito second break nan na hango mai wainar fulawa da sauri na kalli Hawy "Hawwa dauko min kudin break dina a aljihun jakata, ga mai wainar fulawa can, yunwa nakeji"
Tafiya tayi ta dauko nikuma nakara wurin mai wainar fulawar ina zuwa nafara ci ban jira hawy ba,sai da naci ta naira dari.
Bayan an tashi daga sch ne nafara yiwa Hawy korafin rashin zuwan salim, kallona tayi "idan bai dawoba Allah ya kawo miki wanda yafishi"
Cikin razani na kalleta "hawy anya zan iya rayuwa da wani namiji idan ba salim ba?
Ya rigada ya dandana min zumarsa a bakina hawy"
Hawaye nafara na dafa hawy
"Hawy ina son salim kuma bana fatan rabuwa dashi domin muddin idan na rabu dashi to kamar na rabuda MARTABA TA ne"
"Ban ganeba" ta fada cikin razani
Hannunta naja muka nufi karkashin wata bishiya nafara bata labarin abinda salim yayi min saboda bazan iya boye mata ba nakare labarin da cewa "da yana yimin waya akai akai amma yanzu sai dai ni na kirashi kuma kwata kwata yanzu ma wayar tasa ta daina shiga"
Kuka hawy ta yi sosai sannan tafara magana cikin hawaye "pherty meyasa kika yarda da zancen salim, meyasa baki fada min ba, meyasa kika bari ya cimma mummunan kudirinsa akanki, meyasa kika yarda yayi nasarar rabaki da MARTABAR KI?"
Ta jero min wadannan tambayoyin tana kuka,
"Hawy kidaina kuka aikin gama ya gama"
"Tashi muje gida da yamma sai muje wannan plaza din tasu ta kasuwa ko zamu sameshi acan" tafada tareda jan hannuna muka tafi amma har lokacin bata daina kuka ba.
Da yamma hawy tazo tacewa mama mamansu ta aiketa kasuwa shine tazo na rakata, mama bata hanaba tabari muka tafi, muna tafiya take yimin magana "samarin nan fa basuda tabbas pherty"
"Hakane hawy amma lokacin da abun ya faru baki ga yadda ya rinka makalkale mun ba yana min wasu surutai ni banma san ko wanne irin yare yake yiba daga karshe yace zancen aurenmu yana nan bai fasaba"
"Ai mayaudari ne yasan yana son naki meyasa bazai bari har sai kunyi aure sannan zai karbi wannan abun ba, Allah yasa ma ba guduwa yayi ba" gabana ne naji yanata faduwa.
Lokacin da muka je plaza din babu kowa sai wannan mai gadin da muka taba bashi ajiyar kaya, bayan mun gaisa ne sai hawy ta tambaye ina salim
"Wanne salim fa?" Ya tambayeta itama
"Wanda ya yi mana watsi da kaya"
"Auho jawad zakice ai, jawad ya dade bai zo nan ba dan akalla zai kai watanni biyu rabonsa da nan kuma yana kasar dan ko jiya da naje gidan nasu na ganshi"
Kallona hawy tayi muka hada ido tace "um baba inane gidan nasu?"
"Gidansu yana nan a new g.r.a acikin gombe"
"Amma baba ai ance yakusa aure ko?" Tasake tambayarsa
"Anya kuwa?
Shi jawad bana zaton zaiyi aure nan da shekaru 4 ma saboda naga shi bature ne"
"Baba ko zamu iya sanin waye jawad?"
"Me zai hana yayan nan" zama ya gyara ya fara da cewa.
"Alhaji Habibu mai goro shine mahaifinsu, sana'ar mahaifinsu itace sayar da goro tun yana sayarwa acikin kasar nan har takai yana fita kasashen larabawa yana sayarwa acikin yawonsa ne ya auro mahaifiyarsu a kasar saudiyya, babarsu balarabiya ce, su biyune awurin mahaifan nasa daga shi sai yayansa Aadil mahaifinsu dan asalin cikin garin gombe ne, Allah ya bashi arziki mai tarin yawa ta sanadiyyar sayar da goro, tun lokacin da aka haifi jawad aka yayeshi ya tafi saudiyya acan yayi rayuwarsa baya zuwa sai lokaci lokaci, nikuwa nadade ina tare da mahaifinsu tun da kuruciyata muke tare, amma maganar gaskiya jawad bashida niyyar yin aure yanzu"
Hankalina ne naji ya tashi mutuka, tabbas salim mayaudarine kuma marar gaskiya tunda gashi harda boye sunansa na gaskiya,
"Mun gode baba" Hawy ta fada tareda jan hannuna muka fara tafiya, "kinji dai da kunnenki sunansa jawad ba salim ba,muje gida kafin musan abin yi gobe" nidai kasa magana nayi binta kawai nake har muka je gida, gidansu ta shiga bayan tayi min gargadin na kwantar da hankalina gudun kar mama ta gane.
Ina shiga gida na iske wani tashin hankalin domin ashe bayan tafiyarmu kasuwa principal din sch dinmu yazo ya samu abba ya sanar dashi cewa ina dauke da juna biyu na wata biyu dan haka sun dakatar dani zuwa makaranta.
A falo nasamu mama tayi jugum fuskarta sharkaf da hawaye abba kuwa sai fada yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
"Dama ni tunda naga yaron nan naji ban yarda dashi ba, gashi nan kin zuba musu ido yaje yayi mata cikin shege, to wallahi bari kiji, ni bazan zama mutumin banza ba, bazai yiyu ina na'ibin limami aga wannan danyen aiki agida ba, dan haka dole ne phertyma tabar min gidana ayau, kuma wallahi ban yarda taje gidan wani nawa ba, ke ko wurin wanda nasani taje ya taimaketa Allah ya isa ban yafeba"
Kalaman dake fita daga bakin abba kenan, da sauri na juya na nufi dakina na dauko wayar da jawad ya bani nafice daga gidan, tashar mota na nufa ko gidansu Hawy ban shiga ba, lokacin da na shiga tasha karfe 8 na dare, ina zuwa nabayar da wayar aka bani dubu uku alhalin kudinta yafi haka kawai dan sunga a matse nake ne amma ni nasan mai tsada ce, dakyar na samu motar da zata je gombe saboda babu passenger da yawa, saboda tsabar tashin hankali ko kukan ma yaki zuwa.
Karfe Tara da wani abu lokacin da muka je cikin gombe ana saukemu nasamu mai keke napep nace ya kaini sabuwar g.r.a koda naje unguwar shiru take baka jin motsin kowa, sauka nayi na biya mai keke napep kudinsa sannan nafara tunanin yadda zan lalubo gidansu jawad, a karkashin wasu fulawoyi dake shuke akofar wani gida na makale, sai a lokacin naji kuka ya subuce min take nafara kukan bakin ciki.