← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 27

Sashe 3

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Part din mahaifiyarsa suka shiga an kawata komai akan table, abinci ne iri iri daban daban na alfarma, sai kamshin kanumfari da tafarnuwa ne ke tashi, idan da sabo to ya saba domin ko farar shinkafa aka dafa a gidan sai an sa mata kanumfari wannan yana daya daga cikin al'adar mahaifiyar tasu kasancewarta balarabiya usul,
Kadan ya zuba abincin ya fara ci yana ci yana tunanin hanyar da zai magance matsalar da ta kunno kai gareshi, daga karshe ya yanke shawarar ci gaba da farautar zuciyar pherty har Allah yasa ya dace.
****************
Yau ta kama ranar weekend dan haka gaba daya hostel din cike yake da hayaniya, pherty da A'isha kowacce tana kan gadonta a kwance, Sadiya ce ta shigo cikin dakin
"To yan hutu sai ku tashi aje ayi wanki"
Juyi A'isha tayi tareda dago kanta ta kalli Sadiya
"Dan Allah ki bari ajima sai ayi"
Harararsu tayi su duka
"Wallahi ko ku tashi ko kuma na debi iya kayan da nasa na wanke na bar muku naku"
Juyi pherty tayi sannan ta tashi zaune
"Meye" ta fada tana hararar Sadiya
"Ba asani ba" Sadiya ta fada tana hararar ta itama,
"Wanki za ayi wai yanzu da sanyin safiyar nan" A'isha ta fada tana kallon pherty
"Tab babu wankin da zanyi wallahi, daga tashina ko muryar yayana banji ba", wayarta ta dauka ta fara kokarin kiran yayan nata,
"Kun san halina ai, kowaccenku tayi duk abinda take so yanzu" Sadiya ta fada lokacin da take kokarin ficewa daga cikin dakin,
"Yayana ko baka tashi ba?" Pherty ta fada a hankali, ita kam A'isha kwanciya tayi tafara sauraron hirar pherty da aadil, ita dai a duniya bata taba ganin masoyan da suke burgeta ba kamar pherty da Aadil,
Yana daga kwance akan makeken gadonsa yayi murmushi tareda yin juyi "natashi tun dazu antynki ce ta tasheni ma, badon haka ba sai 11 zan tashi"
Murmushi tayi "ai kuwa dai ta kyauta dan da bata tasheka ba da bazan ji muryarka ba yau sai nan da 11?"
"Eh mana" ya fada yana kokarin bude laptop dinshi wacce ke ajiye a kan bed side drawer dinshi,
Yana budewa hoton pherty ne ya mamaye kan screen din, hoton ya tsaya yana kallo,
"Kinyi kyau pherty na" ya fada lokacin da yake shafa hoton,
"Kaima ai kullum kana yin kyau yayana"
"To yaushe kika tashi?"
"Yanzun nan Sadiya ta tada mu wai zamu yi wanki, nikuma wallahi yaya na tsani wanki bata min rai yake yi"
"Shine baki taba fada min ba?

Ina sadiyan?"
"Tafita"
"A'isha fa?"
"Gata"
"To bani ita"
A'isha ta mikawa wayar, "ungo yayana zai yi magana dake" karbar wayar A'isha tayi ta kara a kunnenta
"Hello yaya aadil"
"A'isha daga yau na soke yin wanki, babu ku babu wanki, ku rinka kaiwa shago ana wanke muku kinji?

Wadanda zaku iya wankewa kawai na yarda Ku wanke"
"To yaya aadil zamu kiyaye" A'isha ta fada tana kallon pherty tareda mika mata wayar
Karba tayi ta juya suka ci gaba da hirarsu da aadil har Sadiya ta shigo ta fara aika musu da harara,
"Albishirinki?" Inji A'isha
"Goro" Sadiya ta mayar mata da amsa
"To yayan pherty ya hanamu wanki yace sai dai muna kaiwa shago inners wears kawai ya yarda mu wanke, zama Sadiya tayi "ai yaya aadil dinnan yana shagwaba yarinyar nan ina jin idan sunyi aure babu abinda zata rinka yi"
Dariya A'isha tayi "ai kuwa ya kyauta danni wallahi hakan burgeni yake"
Mikewa Sadiya tayi ta nufi risho tana fadin "eh ai keda ita duk halinku daya na rashin son yin aiki".

Ranar Monday da wuri dukkaninsu suka shirya domin zuwa lecture kowaccensu taci kwalliya ajin karshe, atare suka fito suka nufi area classes, a ta gaban wani babban hall pherty ta hangoshi zaune acikin motarsa kirar KIA kalarta ja yana sanye da bakin face a fuskarsa,
"Jawad ko kai maye ne sai haka" tafada acikin zuciyarta, yana hangosu ya fito ya nufo inda suke, kasancewar basu sanshi ba sai suka tsaya kallon gun wacce zai zo,
Agaban pherty ya tsaya yana mayaudarin murmushinsa dake sace zuciya wanda pherty ke ganinsa tamkar hayaki dan baki, "morning my queen" ya fada a hankali,
Kanta ta juyar, yayinda A'isha taja hannun Sadiya dan su dan basu waje, suna matsawa ya dubi fuskarta wadda tasha kunu murtuk a hankali ya furta "ki saki fuskarki, wannan bata ran da kikayi bai kamaci kyakkyawar fuskarki ba pherty na"
Dam,dam gabanta ya fadi, saboda wannan sunan yayanta ne kadai ke kiranta dashi,
Gabanta ya dan sake matsowa "don't break d heart that love you pherty, love can neva being hate, and you know..!"
Hannu ta daga masa, "kai jawad, kai macuci ne, kai azzalumi ne, kai marar imani ne, wai me na tare maka a rayuwar duniya da kaketa burin sai ka ga bayana?

Jawad har yau ina tareda bakin cikin da kunsa min koda wannan ka barni kayi wa MARTABA TA babbar illa, kayi hakuri ka kyaleni ka barni da abinda nake ji, kai maha'inci ne nasan duk maganganunka na yaudara ne, yanzu nasamu mai kare MARTABA TA dan haka kayi nesa dani"
"Impossible" ya fada cikin daga murya
"Ni jawad nine mutumin da zan dawo miki da MARTABAR KI nine zan aureki zan nuna miki soyayya sannan na kare miki MARTABAR ki, wallahi kinji na rantse mutukar ina rayuwa to sai na aureki pherty, indai kika ga ban aureki ba to mutuwa nayi" yana kaiwa nan ya juya ya nufi motarsa, sai a lokacin tabi bayanshi da kallo yana sanye cikin dark blue din jeans da yellow din t shirt mai gajeren hannu.

Kamar ta fashe da kuka take ji saboda ta rasa yadda za tayi da jawad ya fita daga cikin rayuwarta,
Su A'isha da Sadiya ne suka karaso inda take "yau yaya aadil ya samu abokin takara kenan" A'isha ta fada tana dariya,
"Kuma fa kinga shima ya hadu" Sadiya ta bata amsa, ai pherty na jin haka hawaye ya fara sulalowa daga cikin idonta dama kamar jira take,
Cikin mamaki dukkaninsu suka fara magana
"Allah ya baki hakuri daga wasa?" Wasu hawayen ne suka gangaro mata ba tareda ta basu amsa ba,
"Kiyi hakuri pherty mun san yaya aadil kike so, to amma shi masoyi bai taba zama makiyi ba dan haka shima wannan din ki lallabashi ku rabu lafiya" Sadiya ta fada tana kallonta, jan hannunta A'isha tayi "muje mu shiga lecture pherty zamu tattauna daga baya" inji A'isha.

Koda suka fito daga lecture ma bata sauya zani ba in banda kuka babu abunda pherty take yi lallashin duniya suka yi mata amma taki yin shiru ganin haka yasa Sadiya Kiran aadil a waya ta sanar dashi, cikin rudu yace
"Bani ita" bata wayar Sadiya tayi "ga yayanki zaku yi magana"
Karbar wayar tayi cikin kuka ta fara magana.

Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [4/27, 6:12 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
Pg 16-25
*** Cikin kuka hadeda shagwaba pherty ta fara magana
"Yayana"
Arude ya amsa mata
"Pherty na me ya sameki?

Ki fada min pls"
Hawayen fuskarta ta goge
"Yaya Aadil kaina ke ciwo amma yanzu ya daina"
"Um um fa phertyma ki fadi gaskiya"
Murmushi tayi itama
"Wai yaya Aadil baka kunyar fadin sunana bayan kuma sunan umminka ne"
Yar dariya yayi mai dan sauti
"To ai ba sunan Ummi na fada ba sunan matata na fada kuma sunan first born dina"
"Anty saliman mace zata haifa?" Ta tambayeshi cikeda zolaya
"Ke dai, kece zaki haifi mai sunanki insha Allah"
Shiru tayi, can kuma tayi zakal tace
"To ai babba shine ya kamata ya fara haihuwa,in dai ba tsari ake yi ba"
"Babu wani tsari ita kanta antyn naki tana son haihuwa nima kuma ina mutukar kokarina kawai dai Allah ne bai kawo ba"
"Wanne kokari kake?

Babu wani kokari"
"Haka kikace?

To bari muyi aure zaki ga rashin kokarin nawa"
"Allah ya baka hakuri wasa nake ai nasan kai mai kokari ne ako ina"
Murmushi yayi "matsoraciya, har kin tsorata?

To albishirinki?"
Cikin doki da murna tace "goro"
"Nafasa zuwa next week, this week zanzo naganki, so ki daina kuka kinji?"
Cikin murna tace "ranar yaushe?"
"Ranar juma'a zaki ganni domin wurinki ma zan fara zuwa"
"Woooh" ta fada cikeda murna "yeeeeh" ta sake sakin yar kara "zanga yayana"
Dariya ya soma yi mata daga karshe yace "tunda naga kinata murna to bari na barki anjima zan kiraki"
"To yayana, bye"
Tsalle ta daka ta dale jikin Sadiya da A'isha "yaya Aadil zaizo this Friday, me zan dafa masa?

Yeeeh fried rice zanyi in hada masa coconut juice"
Sadiya da A'isha dai kawai dariya suke suna kallonta kamar ba itace take kuka dazu ba amma yanzu gashi tanata dariya, haka suka rankaya suka nufi hostel.

Tun daga ranar pherty kullum cikin lissafi take na zuwan yayan nata, yau ta kama ranar laraba a lissafinta saura kwana biyu yayanta yazo, ko kwalliya ta daina yi sai ranar da zai zo zatayi.

Shiryawa tayi ita da A'isha suka nufi class yayinda suka bar Sadiya kwance tana bacci saboda ita bata da lecture, yau ma kamar kullum yana tsaye inda ya saba tsayawa, wani kululun bakin ciki taji ya tokare makogaronta amma yau tayi niyyar yi masa abinda indai yana da zuciya ba zai sake zuwa gareta ba.

Kanta ta dauke tareda kama hannun A'isha suka wuce,shima bai yi kasa a gwiwa ba ya bi bayansu yana kiran pherty,
Juyowa tayi ta dubeshi fuskarta a daure ga dalibai fal kowa yana harkar gabansa,
"Tsaya ki saurareni queen"
"Me zan saurara?

Karya ko yaudara?

Aciki wanne kake son na saurara?
Chapter 3 · 0% Book details