← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acikin towel ya nadota tamkar yar jaririya yazo ya ajiyeta akan gado, mayuka ya debo zai shafa mata, nan ya shafeta da mai yayi mata kwalliya ita dai tana zaune tana kallonsa saboda yace ba zata kalli mudubi ba har sai ya gama, powder ya shafa mata ya shafa mata jan baki, wasu abubuwan ma bata san a inda yake shafa mata ba ko goshi ko kumatunta da haka har ya gama yi mata kwalliyar ya zabo mata kayan da zata saka, wata jar riga doguwa mai hannun shimi ya dauko mata, tun daga wurin cinya har kasa a yanke yake saboda haka ana ganin cinyarta guda daya gashi daga kirjin rigar anyi wata tattara kuma kirjin a bude yake dan haka ana iya hango albarkatun kirjinta, jan siririn mayafi ya dauko mata ya daura mata ya tsaya yana kallonta,
"Ya akayi?" Tafada tana kallonsa
"Kinyi kyau queen, taso ki gani" hannunta ya ja suka karasa gaban mirror, kallon kanta ta tsaya yi saboda yadda jawad ya rangada mata kwalliyar kai ka rantse wata shahararriyar mai kwalliyar amare ce tayi mata, abubuwan da bata taba saka su a fuskarta ba ma yau ya saka mata, rungume shi tayi tace,
"To sai muyi picx din tarihi ko dan wannan kwalliyar tayi kyau" hotuna suka shiga yi ita dashi tun suna dauka a daki har suka dawo falo suka ci gaba da dauka, kan kujera ya fada ta kuwa bishi tafada kan kirjinsa tana kallonsa kyatt ya dauka karbar wayar tayi ta kurawa hoton ido yayi kyau sosai duk cikin hotunan ma wannan na karshen yafi burgeta.

Tana kwance a kan kirjinsa yana shafa kanta yana yi mata dadadan kalamai kasa kasa har magrib tayi sai a lokacin suka tashi dan gabatar da salla.

Bayan sun idar da salla ta shiga kitchen, binta yayi ya tayata suka dafa indomie da kwai suka fito, a baki ya rinka bata har ta koshi.

Koda lokacin bacci yayi dakinta yazo bayan yayi shirin bacci ya rungumeta tsam ajikinsa har bacci ya daukeshi amma ita pherty duniyar tunani ta shiga har bacci barawo yayi nasarar dauketa.

Tunda wannan abun ya faru jawad bai sake kokarin kulata ba amma yana bata dukkan kulawar data dace domin kullum akoda wanne lokaci yana manne da ita yana yi mata soyayyarshi mai tsada, ko girki zata yi sai ya bita ya tayata, suna aiki suna taba soyayya.

Ta dan samu sauki babu laifi sai dai kumburin da mararta keyi yanzu shine tashin hankalinsu, gefen mararta ya kumbura kamar an hura tattali amma kuma bleeding din ya tsaya.

Tana kwance agefen gadonta daga ita sai wata yar ficiciyar riga fara mai shara shara da gajeren wando baki jawad ya shigo, a kusa da ita ya kwanta ya dauketa ya dorata a samansa ya fara yi mata cakulkuli nan ta shiga zillewa tana dariya, shima dariyar yake,
"Dan Allah ka daina" ta fada tana dariya,
"To nadaina queen, kin san wani abu?

Ya kamata muje asibiti kiga Ganny doctor akan matsalar nan taki" ya kare maganar yana shafa kanta,
"Jawad ba sai munje ba saboda tun lokacin da abun ya faru doctor din yace ba zan sake daukar ciki ba kuma dakyar idan zan iya rayuwar aure" wasu hawaye suka silalo daga idonta lokacin data gama maganar,
"Kar ki sake fadin haka queen domin babu wanda yasan gobe in banda Allah"
"Kaga jawad kawai mubar maganar nan zancen zuwa asibiti ma bai taso ba ahakura kawai"
Kallonta yayi "kina nufin haka zamu zauna da wannan lalurar ba zamu nemi mafuta ba?"
Sauka tayi daga jikinsa "to wacce irin mafuta?

Ai mai faruwa ta faru sai dai hakuri"
"Dole muje asibiti pherty saboda fadar likita ai ba fadar Allah bace"
"Ehh amma ai aikinsa ne dan haka abinda ya fada dole ayi aiki dashi" ta fada cikin tsiwa,
"To yanzu me kike nufi?

Zamu ci gaba da zama a haka ne?" Ya fada a kule,
"Eh haka zamu zauna sai dai tunda kai ba zaka iya jurewa ba sai ka nemi solution" ta fada cikin bacin rai,
"Pherty, ke pherty wai meyasa ku mata kuke da karancin tunani ne?"
"Malam nidai inada tunani na, kawai ka fito fili ka cemin kai dai ba zaka iya zama dani ba tare da kana samun biyan bukatar ka ba, tunda yanzu ni ba mace bace shiyasa ba zaka zauna haka ba, dole ka nemo mai daukar dawainiyarka"
"Ta yaya da zan zauna ahaka?

Ni dutse ne ko kuma ni ba mutum bane?

Idanma kika yi tunanin zan iya zama a haka kin yaudari kanki, taya zan zauna kullum daga kiss sai hugging?

Kinga ki maida hankalinki ki shirya muje muga likita"
"Eh ai sai yanzu na gano inda ka dosa, dadinta ma dai ansan ba haka nake ba tun asali kuma babu wurin likitan da zanje"
Bai sake tanka mata ba ya tashi ya fice daga cikin dakin, yana fita ta fashe da kuka saboda dama wannan ranar take gudu ranar da jawad zai bukaci mace tunda ita ba zata iya yi masa komai ba.

Tun daga wannan rana ta dauki fushi kamar yadda shima yaketa faman fushi, ganin zaman gidan yayi mata zafi ya sata tunanin komawa sch, a falo ta sameshi kwance kan kujera yasha kananan kaya kusan ita bata ma taba ganinshi da manyan kaya ba.

"Ina son zan koma sch gobe sannan kuma provision dina ya kare" tana gama fadin haka ta juya ta koma dakinta ba tare da ta kalleshi ba, bin bayanta yayi da kallo yayi kwafa ya tashi ya fita, wani provision store yaje ya iyo mata siyayyar komai da komai na duk abinda zata bukata ya kawo ya jibge mata a falo yayi ficewarsa ya tafi gidan aadil bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha.

Koda ta fito taga kayan barinsu tayi a wurin sai washe gari wurin karfe 11 ta shirya tasa mai gadi ya nemo mata mai keke napep ta kwashe kayan tayi tafiyarta sch lokacin ko tashi daga bacci ma jawad din bai yi ba sai tashi yayi yaga bata nan hakan ba karamin sake kular dashi yayi ba ya fuskanci yanzu yarinyar nan wata rashin kunya take ji da ita amma zai bata mamaki.

Tunda pherty ta koma sch tayi watsi da tunanin jawad duk da cewa tasan hakan ba mai yiyuwa bane, yau ma kamar kullum tana kwance akan gadonta a dakinsu hannunta rike da waya tana kallon hotunan da suka yi ita da jawad ranar da yayi mata kwalliya suna tsaka da soyewa hotunan sukan sata nishadi duk lokacin da ta kallesu, murmushi kawai take yi ita kadai domin hotunan sun burgeta musamman ma wadanda suka dauka a falo, wani yana kissing din wuyanta, wani kuma bakinsa kan kumatunta amma wanda take kwance kan kirjinsa duk yafi burgeta,
"Baiwar Allah lafiyarki kuwa?" Sadiya ta fada tana yiwa A'isha signa,
"Tambaye ni dai" ta bata amsa tana sake kallon hoton, sai kuma ta tashi zaune ta ajiye wayar ta fita da sauri, shaf ta manta da lecture note dinta a room 1 da taje hira can dazu dan haka ta tafi daukowa da sauri.

Tana fita sadiya ta dauki wayar ita da A'isha suka fara ganin hotunan,
"Kai wato yarinyar nan kawai sha'aninsu taje suka yi babu wata rashin lfy da jawad yayi" inji A'isha,
"Ai mu suka mayar garori amma luv dinsu kawai suka sha" Sadiya ta fada tana budo wani hoton, shigowar pherty ce ta katse musu hirar,
"Kut kuban wayata malamai, waye yasa ku kallar min sirrina nida mijina?" Hanata wayar suka yi suka gudu nan ta hakura ta kyalesu har sai da suka gama ganin picx din sannan suka dawo mata da wayar.

Ranar tana zaune yaya aadil ya kirata yayi mata fada saboda jawad ya fada masa ya sata abu taki yi kuma sai faman fushi take yi dashi, nasiha yayi mata sosai sannan suka yi sallama aranar da daddare sai ga jawad din yazo wurinta.

"Shine zaka wani je ka hadani da yaya aadil ko?" Ta fada a shagwabance tana kallonsa,
"Eh ai naga kinfi jin maganarsa ne fiyeda tawa saboda har yanzu nasan shi zuciyarki take so"
Kallonsa tayi sai kuma tayi murmushi,
"Ni wlh ba sonsa nake ba kawai ina girmama irin halaccin da yayi min ne kamar yadda nake girmama irin son da zuciyata take yi maka"
Murmushi yayi yakai ma goshinta kiss, "to yanzu yaushe za muje asibiti?

Koda yake nasamu wani likitan mata nayi masa bayanin matsalar ki to sai yake nuna min kawai gara muje kasar saudiyya sai aduba ki acan tunda abin yayi worst amma ya kika gani?"
Cikin jikinshi ta shige domin tayi missing dinshi sosai,
"To amma abari nagama exams dina tunda kaga next week zan fara"
"Ok to babu damuwa, i wish u all d best my queen" kwantar da kanta tayi acikin kirjinsa tana shakar daddadan kamshin da yake futarwa.

Akwana atashi yau har pherty ta kammala exams dinta tanata shirin tafiya gida duk jinta take babu dadi saboda zasu rabu da mutanen nata sai bayan dogon hutu sannan zasu dawo sch, rungumesu tayi tana kuka suna kuka ta tafi gida.

Tunda ta koma gida jawad ya fara yi musu shirin fita kasa mai tsarki, kwananta biyar da dawowa suka daga ko kumo bata je ba sai waya tayi ma su mamanta tace zasu tafi umara, haka hawy ma tayi mata wayar ta fada mata.

Karfe 4 na yamma suka sauka a kasa mai tsarki a wani hotel mai suna ALAM TOWA acikin unguwar markaziya, aranar suka halacci asibiti suka ga likita, an dorata akan magani sannan zasu yi mata aiki, dan haka tunda suka zo kasar ta dage da ibada tana addu'ar Allah yasa ta samu lfy, cikin ikon Allah akayi aiki a sa'a kwananta biyu a asibiti aka sallameta da tulin magunguna.

Daga nan yawo jawad yajata zuwa gidajen danginsu da sauran wurare, har sch din da yayi duk sai da ya kaita ta gaggani, yanayin kasar ya karbi jikin pherty nan tayi lukwikwi da ita tayi fes saboda in banda shakatawa babu abinda suke yi acikin wannan kasa duk da cewar suna ibada sosai.
Chapter 23 · 0% Book details