Sashe 13
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa tayi ta kalli aadil saura kadan tasaka kuka, girgiza mata kai yayi,
"Kar kiyi kuka pherty na, na tabbata su mama suna nan suna addu'a Allah ya dawo dake garesu, domin duk abinda ya faru sun san kaddara ne"
"Nagode yaya, hakika kai nadabanne acikin mutane sannan kana da abubuwan da ba kowanne mutum ne yake dashi ba"
"Nagode pherty na wannan Kalmar taki tayi min zaki kamar sugar, oh no ba sugar ba kamar Zuma zakinta yake agareni,kin san zuma tafi sugar zaki"
Dariya tasa amma gabanta sai faduwa yake, saboda bata san yadda zata samu gidan nasu ba ko su mama na nan ko sun tashi oho.
Tafiya kadan suka shiga cikin garin kumo nan ta fara bin ko ina da kallo har suka isa unguwarsu, komai ya canja amma gidajen suna nan yanda suke in banda yan sauye sauye da aka samu "Allah sarki hawyn mama kawata ko tana nan ko bata nan" haka ta fada acikin zuciyarta daidai lokacin da suka zo kofar gidansu hawyn,
Akofar gidansu yayi packing ta fito, unguwar shiru kamar babu kowa, tsayawa tayi ta kasa shiga gidan sai aadil ne ya wuce gaba tana biye dashi a baya, lokacin da suka shiga gidan abbanta yana kishingide a tsakar gida akan tabarma yana jin radio ita kuma mama tana kitchen tana girki, sallama aadil ya rangada, tashi abbanta yayi daidai lokacin da yake amsa sallamar, zumbur ya mike,
"Hajiya Adama, Adama, Adama kina ina?
Maza fito kigani yau Allah ya amshi addu'armu ya dawo mana da yarmu" abbanta ya fada cikin farin ciki
Da gudu mama ta bazamo ta fito, tana fadin "malam me naji kunnuwana suna fada min?
Me nakeji malam?" Idanuwanta ne suka kai kan pherty ai da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta.
Kuka suka fara yi ita da maman nata
"Assha meye kuma na kukan?
Tunda ta dawo ai bukatarmu ta biya" abbanta ya fada
Wuri aadil ya samu ya zauna kusa da abbanta, bayan sun nutsune aka gaggaisa nan aadil ya fara yiwa iyayenta bayani "baba ba tone tone za ayiba, ga pherty nan dai yau ta dawo sai dai ayi addu'ar Allah ya kiyaye gaba"
"Amin dannan, amin amin, wallahi ko lokacin da ta tafi nayi bakin ciki mutuka domin abinda ya faru kaddara ce kuma shima yaron da yayi mata cikin yazo ya nemi afuwarmu" juyawa yayi ga pherty "phertyma kiyi hakuri kinji nasan nabaki tarbiyya iya iyawata kuma kinyi aiki da ita kawai wata kaddara ce da jarrabawa ta samu rayuwarki"
Ita dai pherty itada mamanta basu ce komai ba in banda kukan da suke yi,
"Ba kuka za ayi ba mama godewa Allah za ayi" aadil ya fada yana kallonsu
"Abba bayan tafiyata daga gida wannan shine ya dauki dawainiyata yayi min komai na rayuwa ya kula dani har zuwa yanzu"
"Allah yayi masa albarka, Allah ya yi masa albarka, mun gode, mun gode madalla"
Nan aka barke da hirar yaushe gamo duk abubuwan da suka faru sai da pherty ta fadawa iyayenta abu dayane basu fada ba itada aadil maganar rashin lafiyar da take tareda ita domin bata son su tayarwa da iyayen nata hankali.
Aadil ya dade agidan Kafin yayi musu sallama ya fita, bin bayansa pherty tayi suka tsaya a soron gidan,
"Pherty na sai munyi waya, gobe zan koma abuja"
"Allah ya kiyaye hanya yayana,sannan banda kallon yanmata, gashi zaka tafi baka ga kawata hawwa ba"
Murmushi yayi "idan nazo next time zan ganta, ki gaishe min da ita"
"Zata ji"
"Yawwa amarya ta" ya fada yana dariya
"Kaima ai ango ne" itama tafada tana dariyar
"Idan na biya ta taki zan kwana anan, sai munyi waya pherty na, bye bye"
"Bye bye yayana".
Tafada lokacin da yake shiga cikin motarsa,
Hannu ta fara daga masa har ya fice daga cikin layin nasu ta juya ta koma gidan nanfa suka cigaba da hira ita dasu mama ananne ma taji cewar yan unguwar basu san abinda ya faru ba kawai dai ance ta b'ata ne amma basu sanar da kowa abun kunyar da tayi ba, dad'i taji ya rufeta lallai naka sai naka,
"Mama ina hawwa?" Ta tambayi mama
"Hawwa dazun nan ma ta shigo, tana nan, ta kusa kammala karatunta itama a jami'ar tarayya dake garin katsina"
"Mama bari naje naganta, nayi missing dinta over"
Zuruf ta mike ta fice daga gidan ta nufi gidansu hawy, tana shiga ta hangota tsugunne tana wanke wanke,
"Sannu da aiki yanmatan mama"
Dasauri hawyn ta jiyo wa zata gani?
Dagudu ta tashi taje suka rungume juna,
"Phertyn mama kece?
Muje daki" hannunta taja ko ta kan mama basu biba domin tana daki, wanke wanke kuwa tuni anmanta dashi, zama sukayi suka fara bawa juna labarin duk abun da ya faru bayan rabuwarsu, nan pherty ta bata labarin aadil,
"Phertyn mama ko kin san cewar jawad yazo rannan kuwa?
Har kirani yasa akayi na rakashi wurinsu mama, sannan yace shi yanzu aurenki zaiyi domin yana son gyara kuskuren da yayi a baya"
"Hmm hawy kenan ai jawad bashida aikin yi ne, domin nafada masa ni yanzu bazan aure shi ba yayansa zan aura"
Ido hawy ta zaro "wai dama shi aadil din yayansa ne?"
"Uwarsu daya ubansu daya"
"Tofa wannan abu akwai mamaki amma"
Hannun hawy ta kama ta dora akan mararta "hawy taba kiji fa, kiji yanda gefen marata yayi tauri kamar dutse, gashi doctor yace ba lallai ne na haihu ba, ko sex dinma dakyar idan zan iya, taya zan auri jawad?
Aadil zan aura domin ko babu komai shi dama ba jikina yake so ba sannan kuma zai iya hakura ya zauna dani koda kuwa bazai samu wani abu awurina ba"
"Pherty kaddarar da kika hadu da ita kenan?" Hawy tafada idonta taf da kwalla,
"Kar kiyi kuka pls, ai ko jiya ma saura kiris na mari jawad wlhi"
Girgiza kai hawy tayi
"Gara da baki mareshi ba, jawad yayi nadama pherty kuma wlhi yanzu dagaske yake sonki, kamar yadda nasan kema kina sonsa, kawai kyautatawar da aadil yayi miki ne take hanaki nuna soyayyar jawad, amma ni nasan kina sonshi, to ga shawara ki daina bacci ki yawaita tsayuwar dare kina kai kukanki wurin ubangiji kan ya zaba miki abinda yafi alkairi, nima kuma zan tayaki da addu'a"
"Nagode hawy dama nasan ke ta dabance a gareni"
Murmushi tayi ta goge hawayen kan fuskarta
"Sannan magana ta gaba itace kar kisake yiwa jawad wulakanci pherty saboda kinga baki san abinda Allah zaiyi ba ta yiyu shine mujinki idan kuma ba mijinki bane sai a rabu salin alin, nasan abunda yayi miki da ciwo to amma kaddara ce babu yadda za ayi"
"Shikenan hawy nagode zan kiyaye insha Allah"
Mikewa tayi "zan koma wurin mama domin ban gama ganinta ba"
"To muje nima ina nan shigowa"
Ummi A'isha🏻
[5/11, 12:36 PM] Ummi A'isha🏻: [5/11, 7:59 AM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
55-60
~~~ Dakin maman hawy suka je, itama kamar a mafarki ta ganta nan aka gaggaisa sannan ta koma gidansu.
Tana zuwa ta dale jikin mama suka fara hira irinta d'a da uwa, daren ranar sun dade a zaune suna hira har sai wurin 2 sannan suka hakura, wayarta ta jawo saboda jin mama tayi bacci, tana budeta taga kiran yaya aadil babu adadi, agogo ta kalla anya kuwa ya kamata ta kirashi yanzu, kiransa ta fara yi ringing biyu ya dauka yana murmushi
"Pherty na yau nayi fushi, wato dan kin samu mama shine zaki manta da yayan ki ko?"
"Ni na isa yaya aadil?
Na isa mantawa dakai, ban isa ba gaskiya hirace tayi yawa shiyasa ina fata kaje gida lfy"
"Lfy lau amarya"
Dariya tayi
"Yaya aadil kana son kirana da sunan nan alhalin kuma kaima angone"
Murmushi shima yayi, bayan sun dan taba hirane sukayi mata sallama domin gobe jirgin asuba zai bi zuwa abuja.
Washe gari da safe bayan ta tashi tayi wanka ta shirya tana zaune a tsakiyarsu mama da abba tana yin breakfast suna hira sai ga hawy ta shigo, kallonta tayi tana murmushi
"Ta mama har antashi?"
"Eh Allah ya nufa" hawyn ta fada tana dariya
Daki suka shige bayan hawy sun gaisa dasu mama,
"Hawy ina labari?"
"Labari ai yana wurinki kawata, ina aadil?"
"Yau banyi waya dashi ba amma dai nasan ya koma abuja yabar gombe"
"Oh Allah ya taimaka, inasu Sadiya da A'isha?"
"Ai ina tashi da asuba bayan nayi salla dasu na fara waya"
"Allah sarki, Allah dai yabar zumunci"
"Amin" hira suka fara har suka gangaro ta kan hirar jawad amma ita pherty yanzu sam bata son taji an ambaci koda sunansa ma haka dai suka dade adaki suna hirar.
******
Satin pherty biyu a kumo sannan ta koma gombe, taji dadin wannan zama sosai domin bata fuskanci wata matsala daga iyayenta ba ko kadan, tana shiga hostel su sadiya da A'isha sukaje suka rungumeta nan aka shiga hira har tsawon wani lokaci.
Soyayyarta da aadil kuwa sai karuwa take domin kullum suna nan makale a waya, bayan sati uku da tafiyarsa aka harhada komai aka kai gidansu pherty, harda Salima matarsa a yan kaiwa kayan,nan aka bar rana kamar yadda yasa afarko, komai yaji a kayan jama'a sai yabawa suke yi.
Nacin jawad kuwa bai hakura ba saboda yanzu kullum sai yazo makarantar wurinta duk da cewa ba wani sauraronsa take ba, da haka akwana a tashi har biki ya rage saura sati biyu nanfa su Sadiya da A'isha suka fara shirye shiryen biki, hawy tayiwa waya tazo sch dinsu dama aadil ya turo musu da kudade dan haka kasuwa suka shiga su hudun suka iyo siyayyar kayan biki harda kayan da amaryar zata saka.
Ana biki saura kwana tara suka tattara suka koma kumo, shikuma angon sai saura sati daya biki zai zo daga abuja, ranar da sukaje aranar sai ga jawad kamar mahaukaci yazo gidansu, tana fitowa taga shine,
"Pherty bakida imani ashe?
Bakida hankaline pherty?
Wannan abun da kike shirin aikatawa wlhi mugunta ce tsantsarta, danme zaki auri aadil?