← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 27

Sashe 27

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarinyar da zan aura itama sunanta pherty"
Wayar hannunsa ta warce tafara kuka mai tsuma zuciya,
"Queen ba laifina bane laifinki ne saboda yanzu kin daina bani kulawa kinga kuwa dole na kara aure gudun kar nafada sabon Allah"
Ledar kifinta ta dauka tafice daga motar ta tafi tana kuka tana ji jawad na kiranta amma taki ko juyowa, kafin ta shiga hostel tayi kokarin tsayar da kukan ta shiga daki duk kifin ma jitake ta tsaneshi, agefen gado ta zauna ta bawa su Sadiya kifin ta fara binciken wayar jawad, ga text din budurwar tasa nan burjik, morning massages, good night, juma'at massages duk gasu nan amma shi bata ga nashi ba sai guda daya wanda ya tura mata shima thanks kawai ya rubuta, ta inda taji dadi number yarinyar yayi saving da pherty amma ita kuma tata ya rubuta my queen ko anan tasan yafi bata matsayi fiyeda waccan amma duk da haka dai haushinsa take ji, wayar tasa ta ajiye agefen pillow dinta ta dauki wayarta tafara chtn da hawy tana fada mata jawad yana neman aure, ido hawy ta zaro tareda fara bata hakuri, nan ta zayyanewa Hawy abubuwan da suka faffaru, shawara Hawy tabata sosai ta yanda zata sake siye zuciyar mijinta, taji dadin shawarwarin hawy kuma ta daura aniyar yin aiki dasu,
Karar shigowar text cikin wayar jawad ne yasata yin sallama da hawy ta kashe wayarta, ta dauki wayar ta bude sakon nan taga daga budurwarsa ne ta rubuto masa "sleeping is a thing line btw life and death......" Da sauri ta goge text din ta lalubo picx din jawad tafara kallo daya bayan daya ita kanta tasan mijinta ya hadu kuma babu dama ne a fagen soyayya dan haka ya zama dole tayi duk iya iyarwata dan ganin ta mantar dashi kowacce mace acikin zuciyarsa face ita guda daya tilo.

Daren ranar sai bacci barawo ne yayi gaba da ita amma kasa bacci tayi, gari yana wayewa dama ya kama ranar friday duk su ukun basuda lectures, dan haka tace yau ranar aikinta ce,da A'isha tafara,
"A'isha yau ki kure basirarki ki tsara min jan lalle,Sadiya ke kuma kiyi min kitson da baki taba yiwa wata maceba agashinta"
Shewa suka saka su duka "tafiya zakiyi haka" A'isha ta tambayeta
"Babu inda zanje kawai zan yiwa mijina kwalliya ne"
Dariya Sadiya tasa tace "yau soyayyar jawad ta tashi kenan?"
"Kudai kawai kuzo kuyi min pls".

Hadadden jan lalle A'isha ta tsattsarawa pherty wanda ya kama yayi dau yazama maroon, ita kuma Sadiya tayi mata kitso mai tsananin kyau wanda ni kaina ummi aisha sai da naso ace kainane, yamma tanayi ta shirya ta nufi gidanta.

Lokacin da taje gidan jawad baya nan dan haka ta shiga tayi wanka ta sake sabuwar kwalliya cikin riga da skirt bakake marassa nauyi bata daura dankwali ba haka ta fito falo, tana zama jawad yana shigowa shima ya hade cikin kananan kaya, cikin mamaki yake kallonta kamar ba itaba tasha kwalliya cikinta ya dan fito kadan,
"Queen saukar yaushe, kai queen yau ke baturiya ce ko balarabiya" karasowa kusa da ita yayi ya fara kallon kunshin da aka rangada mata da kitson kanta,
"Queen dan Allah kar kiyi min irin na rannan, kar ki hanani kanki pls" yafada a sululuce,
Murmushi tayi ta kama hannunsa tana fara masa fararen idanuwanta tuni ya sunkuceta yayi bedroom dinsa da ita.

Washe gari da safe bayan tasha kwalliya cikin shadda kalar shanshanbale riga da zani tafito tanata faman kamshi, kitchen ta shiga ta hada lafiyayyen breakfast ta zo ta shiryashi bisa dining table, kitchen ta koma tana duba guntun kanzonta da ta tafi tabari agidan amma bata gani ba, fitowa tayi fuskarta a turbune daidai lokacin shima jawad ya fito cikin kananan kaya wanda suka yi mutukar yi masa kyau shagwaba tafara yi masa harda buga kafafu a kasa,
"Wlhi ka nemomin kanzona duk inda ka kaimin"
"Kanzo queen" da sauri ya shiga kitchen din a cikin store ya samo ya kawo Mata yana tsokanarta.

Bayan sun kammala breakfast yaya aadil ya iyo waya anty salima ta haihu yan biyu suna asibiti, nanfa pherty aka shiga murna suka garzaya sai asibiti, yara kyawawa masu tsananin kama da aadil farare tas dasu, nan asibiti ya cika da yan uwan salima dasu ummin jawad kafin daga bisani aka sallamesu suka rankaya suka koma gida gaba daya pherty ta dadume jariran ta rikesu bama kamar namijin har saida jawad ya tsokaneta yace itama ta kusa samun nata.

Tunda akayi haihuwar kullum suna gidan maijego har ranar suna inda yara sukaci suna jawad da phertyma, murna wurin pherty ba a magana nan sukaje supermarket suka jibgowa jarirai kaya kamar bada kudi suka siyo ba, satin anty salima biyu da haihuwa suka bar garin gombe suka nufi kasa mai tsarki.

Irin kulawar da pherty ke bawa jawad a halin yanzu tasashi mantawa da kowacce mace sai ita kadai, cikinta ya girma ya shiga wata na takwas a lokacin bikin kawarta hawy ya taso ahaka ta kokarta taje kumo bikin, itace babbar kawar amarya haka ta zage tayi dukkanin abubuwan da babbar kawa keyi, kwanta biyar har saida takai hawy dakinta sannan ta jirgo nata ya nata ta dawo gida, damma yanzu bata zuwa sch hutu suke nan jawad yaci gaba da kulawa da ita da babynsu har ta shiga watan haihuwa nan ta haifo santalelen danta namiji lokacin yaran yaya aadil sun girma Xarah da jawad,murna wurin jawad kamar ya taka dan shege, nan aka shiga bidiri yayiwa maijego da baby kaya na garari, tun ana igobe suna Sadiya da A'isha da hawy suka zo, ranar suna yaro yaci suna aadil suna kiransa da junior, hhh nasan masu karatu har natuno muku da junior din kuluwa ko, washe garin suna su hawy da A'isha da Sadiya da Anty Salima ne suka yi mata aikin komai.

Aranar kowa ya baje aka barta da babynta sai wata yar tsohuwa da mamanta ta kawo mata mai suna iya ladi, nan suka shiga ganin gata ita da junior awurin jawad da dukkanin dangi har sukayi arba'in lokacin ansa date din bikin Sadiya da A'isha, shi kam jawad yanzu bashida damuwa dan haka ya cire kowacce mace cikin ransa sai iya queen dinsa.

Awatan may su pherty suka sha bikin Sadiya da A'isha kwaccensu an kaita gidanta anan cikin gombe, yanzu junior har yayi wayo domin watansa 11 yana gudunsa ko ina pherty kuwa sun kammala karatunsu.

Yau tana kwance cikin kujera tasha wani lafiyayyen leshi orange colour hannunta da kafarta kuma sunsha jan lalle ta gyara gashin kanta yayi yalo yalo ta kafa dauri tana waya da mama jawad ya shigo hannunsa rikeda junior wanda yake mutukar kama da jawad yana sanye cikin blue din riga da jan wando kafarsa sanye da combos fari yana yi mata albishir da cewar anty salima tasake haihuwa, da sauri ta ajiye wayar tana murmushi,
"Allah ya raya wancan karon sunyi min takwara nida mijina yanzu kuma kila su Ummi zasu yiwa"
"Kece zakiyiwa Ummi takwara" jawad ya fada yana kallonta rai ta bata
"A'a ni salim dina zan yiwa takwara tsohon saurayina" tafada cikeda zolaya
Hancinta ya lakuce yace "that salim is not your true lover,i jawad am your true lover here and for the hereafter"
Murmushi sukayi gaba dayansu shima junior da bai san abinda suke fada ba sai da ya dan dara Kadan, to nima dai Ummi Aisha murmushin nayi domin Allah ya nufeni da kammala wannan story.

ALHAMDULILLAH!

Anan na kammala wannan labari ina fata ya fadakar, ya nishadantar kuma ya wa'azantar, inda nayi kuskure agafurceni kuma ina addu'a Allah ya yafe mana gaba dayanmu dani daku masu karatu.

Na sadaukar da wannan littafi gareku kawayena
PHERTYMA XARAH (d writer of Xarah)
SADIYA LAWAL BALA (d writer of Ballagaza)
MISS A'ISHA
HAWWA SULAIMAN(HAWY)
Ina muku fatan alkairi akoda yaushe, Allah ya sanya albarka acikin rayuwarku.

Kin cancanci yabo babbar kawata, aminiya sahiba CWT KAUSAR LUV,mai bani shawarwari akoda yaushe, Allah ya barmu tare, ina alfahari dake kawata.

Jinjina gareki uwar dakina
HAWWA M JABO nagode da kulawarki agareni,Allah ya kara miki kaifin basira.

Kina raina
ADDA BENAXIR nagode miki much
Na yaba miki kawata KHADIJA SIDI Allah yabar zumunci.

Ban manta dakeba ta hannun damana
MIEMIE BEE
Fatan alkairi agareki
ANTY BEBEELO Allah ya raya mana iman.

Dominku ne kawayena
HUMAIRA (yarjejeniya)
A'ISHA (Maman Shakur)
FIDDAUSI SODANGI
A'ISHA (chuchun gaye)
A'ISHA DANSABO LEMU
UMMI HAMBALI
Na gaisheki
SA'ADATU DANTIYE babu shakka kinfi kowa son martabata
Masoya nagode sosai hakika kun kaunaci martabata, ina kaunarku fiyeda yadda kuka kaunaceni, yan groups dina da sauran groups duk Allah yabar zumunci,wanda na ambaci sunansu dama wanda ban ambata ba duk kuna cikin raina idan hali yayi zaku jini cikin littafi nagaba, Allah yabar soyayya,masoyan Ummi A'isha aduk inda kuke Ummi A'isha tana sonku sosai, nagode
Recommend this on Google
Comment as:
Publish Preview
No comments:
Post a Comment
aisha ummi
a teenager who loves to read and writes. here are some of my writeups I will like to share with you people enjoy!!

View my complete profile
About Me
▼ 2017 (24)
▼ January (24)
RUWAN KASHE GOBARA..64
RUWAN KASHE GOBARA.. 61-63
RUWAN KASHE GOBARA.. 51-60
RUWAN KASHE GOBARA.. 41-50
RUWAN KASHE GOBARA.. 31-40
RUWAN KASHE GOBARA..21-30
RUWAN KASHE GOBARA..! 11-20
RUWAN KASHE GOBARA..! 11-20
RUWAN KASHE GOBARA..,! 6-10
RUWAN KASHE GOBARA..,! 6-10
RUWAN KASHE GOBARA..! 1
RUWAN KASHE GOBARA..4-5
RUWAN KASHE GOBARA.. 2
RUWAN KASHE GOBARA.. 3
WANI HASKE...! 62-END
RUWAN DARE..

WANI HASKE...! 62-END
MARTABA TA 1-50
MARTABA TA 51-End
MARTABA TA 1-50
MACE GUDA DAYA TILO
SANADIN GATA 1-End
SANADIN GATA 1-End
KWARYA TABI KWARYA 1-End
► 2016 (6)
Blog Archive
Watermark template.

Powered by Blogger .
0 More Next Blog» Create Blog Sign In
Chapter 27 · 0% Book details