← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 27

Sashe 2

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta dade a zaune tana faman kuka sannan ta tashi taja kafarta dakyar ta nufi hostel fuskarta cikeda damuwa,
Tana zuwa daki ta samu Sadiya tana yiwa A'isha kitso, ko kallonsu bata yi ba tafada kan gadonta ta fara wani sabon kukan, dukkaninsu tsayawa suka yi suna kallonta domin a yan kwanakin nan kusan kullum sai tayi kuka wanda su basu san dalilinsa ba.

Cikin damuwa A'isha tayi magana "pherty menene?

Me ya ke damunki?" Shiru bata bata amsa ba kafin ta sake wata maganar tuni wayar phetyn ta soma ruri, cikin kuka ta daga wayar "yayana" tafada tana share hawayen fuskarta, "yanmata na me yake faruwa?" Cikin kuka tace"yunwa nake ji kuma ina jin ba suyi mana girki ba" da sauri ya katseta "suna ina?" "Gasu nan" tafada tana kuka "oya bani A'isha"
Mikawa A'isha wayar tayi takoma ta kwanta
"Hello yaya aadil" cikin sauri yace "haba A'isha ya zaki bar pherty na da yunwa har tana kuka?"
Cikin murmushi A'isha tace "yaya aadil wallahi girkinta ne yau kuma bata yi ba nikuma nace zanyi to yanzu kitso Sadiya take yimin shine nake son da zarar ta gama min sai na dora mana girkin, muma wallahi bamu ci komai ba, amma ga cornflakes nan tasha kafin ayi girkin"
Murmushi yayi "naji wannan to amma me ya hadasu fada da Sadiya dazu kafin ta tafi lecture?"
"Yaya aadil fati bata son aiki duk ranar girkinta sai sunyi fada da Sadiya saboda batayi ita kuma Sadiya itama sai tace bazata dafa ba"
"To shikenan daga yau ku daina girki ku rinka zuwa captaria kuna cin abincin in yaso duk end of month zan rinka biyan abincin, shikenan?

Girgiza kai A'isha tayi "a'a yaya aadil kabari kawai ni nayi maka alkawarin kullum zan rinka yin girkin in yaso fati sai ta rinka wanke wanke ko cefane"
"Phertyn nawace yar wanke wanke?

No gaskiya ki sake mata duty"
Murmushi Aisha tayi "to yaya aadil zan sake mata, sai anjima"
Mikawa Sadiya wayar tayi "ungo yaya aadil zakuyi magana"
Karbar wayar tayi tana dariya "yaya aadil ina wuni?" "Bazan amsa ba saboda kin yi mana laifi nida pherty na"
"Tuba nake yayanmu"
Murmushi ya saki a hankali "to na yafe miki amma kar na sake ji" "baza a sake ba"
"To sai anjima"
Mikawa pherty wayar tayi tana yi mata dariya,cikin haushi pherty ta fusgi wayar tareda karata a kunnenta
"Hello yayana" tafada a hankali
"Yanmata kiyi hakuri komai ya wuce kinji?

Ki daina kuka kinji pherty na, ina nan zuwa ganinki"
Cikin doki tace "dagaske?

Yaushe zaka zo?"
"Sai kin daina kuka sannan zan fada miki", "nadaina yayana fada min" murmushi yayi mai dan sauti "to yi dariya naji" dariya ta fara harda kyakyacewa ahankali yace "zanzo upper week, me kike so na taho miki dashi?" Cikin farin ciki tace "ni kai kadai nake son gani"
"Ki fadi abunda kike so pherty na", "wallahi bana bukatar komai yayana" murmushin jin dadi yayi "to shikenan yanzu ki zauna ki huta sannan anjima zan turo miki 20 thousands ta account dinki, saboda nasan akwai abubuwan da budurwa irinki take da bukatarsu amma kunya ba zai barki ki tambayeni ba"
"Yaya aadil inada kudi fa, kabarshi kawai"
"Nidai anjima zan turo miki"
"Tom, nagode Allah ya saka da alkairi, Allah ya kara budi, Allah ya...!"
Katseta yayi ta hanyar dora dan yatsanshi akan lebenshi "shiiiiiii godiyan ya isa haka pherty na, nasha fada miki duk abunda nayi miki cancantar kice ta sani yi miki, nidai kawai addu'ar da zaki yimin kwaya daya ce, cewar Allah ya bani ke"
Cikin murmushi tace "amin"
"Bari na kyaleki zan kira antynki bata jin dadi tana fama da mura, kema ki kirata kiyi mata sannu kinji, and expect my call later"
"Zan kirata, sai najika yayana, bye bye" tafada tareda zare wayar daga kunnenta, cikin sauri ta danna number Salima ta fara kiranta, ringing uku ta daga,
"Hello kanwata" aka fada daga can bangaren
"Anty yajiki?

Yanzu yayana yake fada min bakida lafiya"
Murmushi Salima tayi
"Ai yayan nan naki ya cika surutu, bafa wani ciwo bane mai yawa ba, just mura ce fa, kuma naji sauki ma"
"Ayya, Allah ya baki lafiya, gasu Sadiya da A'isha zasu gaisheki"
Wayar ta mika musu kowaccensu ta gaisheta sannan suka yi sallama,
A'isha ce ta mike ta janyo risho ta kunna ta fara kokarin dora musu girki, kallon pherty tayi, "oh da haka mata suke da an zauna lafiya aduniya, wallahi nikam anty saliman nan tayi min, tana burgeni babu ruwanta"
Sadiya ce ta karbi zancen ta hanyar cewa "ai shiyasa shi kansa yaya aadil din yake darajata saboda bata nuna irin wannan kishin haukan ba, domin daga lokacin da mace ta zubar da kimarta wai dan mijinta yana neman aure to wallahi daga ranar ta rasata har abada"
Baki A'isha ta tabe "ai kuwa yawancin matan yanzu haka suke, basu san Kansu suke ragewa daraja ba,wata ma dan tsabar rashin aji har budurwar take yiwa waya ta zaga dan tsabar bada kai"
Sai a lokacin pherty tayi magana "ni wallahi dan mijina yana neman aure banda time din kiran budurwar, aure ai hajace tazo kowa ya baje tasa mai rabo sai ya siyar"
"Banda matan yanzu, matan yanzu mugunta da son kai sunyi musu yawa kowa sai tace ita kadai zata zauna a gidanta, alhalin kuma tana da kanne, idan kannenta ne tana son su auri mijin wata amma ita bata son a auri mijinta" A'isha tafada lokacin da take dora tukunya akan rishon data kunna
"Allah dai ya rabamu da sharrin zuciya" inji Sadiya
"Amin" suka amsa dukansu, pherty kuwa hoton aadil ta kurawa ido, yana tsaye yasha bakaken suit wanda suka yi tsananin yi masa kyau, yanata murmushi ya dafa wani karfe a bakin wani tafkeken kogi da alama hotonma a kasar waje yayi shi, murmushi ta fara yi ita kadai saboda tunowa da tayi yace zai zo nan da sati biyu masu zuwa.
**********************
A bangaren jawad kuwa koda ya fita daga makarantar su pherty gidansu ya nufa cikeda kunar zuciya saboda kiyayyar da pherty take nuna masa yanzu tayi yawa alhalin shi kuma yanzu a duniya idan da wacce yake so to itace.

Cikin tsananin gudu ya isa gidan nasu yana zuwa bai jiraba ya kutsa kan motarsa zuwa harabar gidan wanda yake katoton gaske, a fusace ya kashe motar ya zare key din ya nufi side dinsa,yana shiga bedroom dinsa ya shige yaje ya fada kan gado take zuciyarsa ta fara tafarfasa, idanuwansa kuwa tamkar gauta dan ja,
Zaraf ya tashi zaune kamar wanda aka tsikara "Xarah, Xarah wallahi sai na aureki, mutukar ina numfashi bakida mijin da ya fini, nine mijinki ko kinki ko kin so, wallahi babu mai aurenki sai ni, haba Xarah!" Ya fada tamkar wani zautacce,
"Kai jawad kai da waye?" Wata mata fara tamkar balarabiya ta fada cikin harshen fillanci kana kallonta zakaga tsananin kamarsu da dan nata jawad, kamar kara aka tsaga, shekarunta zasu kai 45 a duniya,
Cikin damuwa ya jiyo ya kalleta "Ummi babu komai" yabata amsa cikin harshen fillanci shima,
"Kowa ya kalli fuskarka yasan kana cikin damuwa jawad, ka fada min abunda yake damunka",
Tamkar zaiyi kuka yace "Ummi wata budurwa ce bata sona, ta tsaneni nikuma ita nake so ummi, wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba idan ba itaba, she's the part and parcels of my life, i can't do without her, my life without her is just like a car without fuel, i can't survive without her"
Ya karashe maganar cikin rawar murya
Cikeda tausayawa mahaifiyar tashi ta karaso gabansa ta zauna kusa dashi tareda dafa kafadarsa, kayi hakuri jawad hakika kai ba kayi kamada irin mazan da mata suke tsana ba domin ka mallaki komai, wannan kar ya daga hankalinka zaka aureta zata soka fiye da yanda kake sonta".

Ummi A'isha🏻
[5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha: [4/25, 6:23 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
Pg 11-15
~~~Fuskarsa da damuwa ya kalli ummin tasa yace
"Ummi Xarah daban take acikin mata, sannan kuma duk abunda ta aikata a gareni daidai ne saboda....!" Kasa karasa maganar yayi, yai shiru da bakinsa,
"Saboda me jawad?" Mahaifiyar tasa ta bukata, "jawad anya kuwa babu wani abu wanda kake boye min?"
Kallonta yayi da jajayen idanuwansa
"Ummi babu abinda nake boye miki, nidai ki tayani da addu'a kan Allah ya saukaka min al'amura na musamman ma dangane da pherty saboda idan har ban aureta ba to bazan taba gafartawa kaina ba"
"Saboda me?" Ta tambayeshi tana kallonsa
"Ummi saboda zuciyata tana sonta"
Hannunsa ta kama "ka tashi kazo muje kaci abinci, dan uwanka ma yana nan zuwa nan da wani dan takaitaccen lokaci",
Sai da gabansa ya fadi jin an anbaci cewar dan uwansa zai zo, shidai a halin yanzu idan da wanda yake jin haushi a rayuwarsa ta duniya to bai wuce dan uwan nasa ba domin ya fahimci yana yi masa shisshigi a gonarsa,
"Katashi muje jawad"
Muryar Mahaifiyar tasa ta dawo dashi cikin hayyacinsa, dan haka dole ya mike ya bita ba dan yaso ba.
Chapter 2 · 0% Book details