Sashe 11
Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Satinmu uku acan aka sallame mu babu laifi sunyi kokari domin nadan ji sauki da taimakon Allah amma sun bawa yaya aadil tabbacin cewa kila idan anci sa'a zan iya daukar ciki idan kuma aka yi rashin sa'a to ko rayuwar auratayyar ma bazan iya ba, haka dai muka tarkato muka nufo Nigeria tunda na dan ji sauki domin bleeding din da nake yi yanzu ya tsaya sannan ciwon marar ya dan lafa sai dai yana dan damuna daga lokaci zuwa lokaci.
Kafin mu baro kasar sai da yaya aadil yayi min siyayya mai tarin yawa sannan muka taho, tun acikin jirgi yake jana da hira yana son jin meya faru tsakanina da kaninsa jawad, dakyar na iya fada masa duk abinda ya faru daga farko har karshe,
"Kiyi hakuri phertyma, jawad bai kyauta ba sannan kuma wallahi agida ba asan cewar ya na neman aurenki ba, wannan kawai wani salon yaudara ne ya bullo dashi yaje ya nemo wasu suka kai kaya gidanku, amma kiyi hakuri insha Allah hakan zai zame miki alkairi"
"Allah yasa yaya aadil" nafada ina share kwallar data cika min ido
"Bana son ki rinka kukan nan kinji?"
Kaina na daga ba tare da nace komai ba.
Wurin karfe 3 na yamma muka sauka nan driver yazo ya dauke mu ya nufi unguwar riyal damu, wani madaidaicin gida muka shiga yafito yace mushiga ciki, wata yar dattijuwa muka samu zaune a falo tana kallo, "dada kin ganmu sai yanzu" ya fada yana murmushi,
"Ayya sannunku da zuwa, lale lale" tafada cikeda fara'a, wuri nasamu na zauna aka kawo mana abinci muka ci sai hirarsu suke da wannan matar, bayan yayi sallar la'sar ne yayiwa Dada sallama yace zai tafi nikuma ya kirani nabi bayanshi,
Adaidai bakin gate din gidan ya tsaya yana kallona "pherty zanje gida ke anan zaki zauna wurin dada amma insha Allah kullum zan rinka zuwa ganinki kafin nakoma abuja wurin aikina, yanzu zan tafi saboda naga antynki sai damuna take da waya kamar wanda na bata"
Kallonsa nayi "kanada mata ne?"
"Yes, shekarata biyu da aure haihuwa ce dai ban samu ba har yanzu, may be uwar yayan nawa ta kusa zuwa"
"Ayya Allah ya baka masu albarka yaya aadil, Allah yabaka masu jin kanka"
"Amin pherty na, nagode"
Sai da naga tafiyarsa sannan nakoma wurin dada, haka zamana ya ci gaba da tafiya a wannan gida, kullum yaya aadil na zuwa safe da yamma hakanne ma yasa nayi mutukar sabo dashi muka shaku mutuka, bayan kamar dawowar mu da sati biyu ranar da yamma sai gashi yazo yana sanye da t shirt ja da bakin wando yasha turare, ina zaune a falo ina kallon wani Indian film a tashar zee aflam ya shigo film din ya tafi dani sosai musammam ma saurayin cikin film din (Luv story 2015) shine sunan film din,
"Sannu mai kallo" haka ya fada yana dariya,
"Lah yaya aadil sannu da zuwa" nafada nima ina dariya"
Zama yayi a kan kujerar dake kusa dani "ina dadan?"
"Tana kitchen tana yimana tuwo" nabashi amsa, sai ga dadanma ta shigo bayan sun gaisa ne ta koma kitchen,kallona yayi
"Dada fa kanwar babar dady ce uwa daya uba daya dan haka ki saki jikinki da ita kinji?"
Kai nadaga wlhi dama nagama sakin jiki da ita saboda bata da matsala ko kadan
"Yawwa to ni sallama nazo muyi saboda gobe abuja zan tafi, amma ya jikinki babu wata matsala ko?
Kin daina bleeding din ko kinayi?"
Shiru nayi ban bashi amsa ba saima rufe fuskata da nayi da dan kwalina,
"Bazaki bani amsa ba?
Shikenan Allah ya sawwake"
Haka muka fara hira tsilla tsilla har magrib tayi lokacinne yayi mana sallama ya tafi.
Washe gari kawai sai nasamu kaina cikin damuwa saboda rashin ganin yaya aadil sai kawai nafara kuka, dada tayi rarrashin duniya naki daina kuka, da haka har yayi sati daya da tafiya kullum cikin kuka nake ganin haka yasa dada yi masa waya ta fada masa, aranar sai gashi da yamma.
Ina daki bayan naci kuka na koshi ko ruwa bansha ba bare abinci ya shigo ya sameni "haba pherty na"
Haka ya fada lokacin da yake shigowa cikin dakin,
Tashi zaune nayi nafara murmushi "sannu da zuwa yaya"
"Bazan amsa ba, tashi ki shirya nakaiki gurin antynki yau kuga juna"
Zumbur na mike na shiga wanka shi kuma ya koma falo, kwalliya nayi sosai nafito na sameshi shida dada zaune a falo, "ja'ira mai kuka kawai" dada ta fada tana dariya, muma dariyar muka yi yayi mata sallama muka tafi.
A unguwar Federal low cost gidan yaya aadil yake, gidane tsararre wanda kana ganinsa kasan naira tayi kuka, lokacin da muka shiga cikin tamfatsetsen falon nasu daidai lokacin wata kyakkyawar mata ta fito daga cikin wani daki,
"Ko kanwar tawa ce yau tazo?" Matar ta fada tana fara'a
"Kamar kuwa kin sani itace, yau zakiga pherty na"
Murmushi tayi tazo ta kama hannuna shikuma yaya aadil ya shige dakinsa, zaunar ni tayi ta cikani da kayan cima kala kala,
"Kinga amaryarki yau ko?" Yaya aadil ya fada daidai lokacin da yake fitowa daga cikin dakin,
"Naganta kuma gaskiya ka iya zabe, she's very beautiful, cute, pretty and amazing" ta fada tana dariya, filitanci ya fara yi mata, itama tana mayar masa suna dariya har naji na tsargu,
"Ko zaki zauna da ita Gida daya pherty na?
Nace ke abuja zan tafi dake tace wai a'a tafi son ku zauna tare"
Murmushi nayi a zuciyata nace au dama filatancin da kayi mata ce mata kake dani zakaje abuja,
"Ai muna nan tare da ita sai dai kai ka nemi ta tafiya abujanka" ta fada tana dariya,
"Ai kuwa wasa kike dan kafata kafar pherty na"
Abunsu gwanin sha'awa har dare nakai a gidan sai wurin 8 sannan yaya aadil ya daukeni muka koma wurin dada, washe gari sai gashi da kaya niki niki ya kawo min ciki harda wayar hannu mai tsada wai gashi nan sai mu rinka yin waya idan baya nan basai nayi kuka ba, haka yayi kwana biyu ya tafi tunda ya tafi na sake shiga damuwa danma dai muna waya.
Haka naci gaba da zama da dada duk karshen sati yaya aadil yana zuwa ganina, da haka yaci gaba da yi min hidima acikin rayuwata har yayi min cuku cukun karatu ya sama min admission a wannan university din bayan nasake paper, idan baku mantaba, ranar farko da nafara zuwa makarantar nan yaya aadil ne ya kawo ni karewa ma shine ya hadani daku lokacin da kuka fito daga hostel, yaya aadil yayi min komai na rayuwa yanzu kuma daidai lokacin da zai aureni sai ga jawad kaninsa kwatsam ya dawo da soyayyata wai shi zai aureni saboda shine first love dina"
Hmm tayi murmushin takaici ta dubi Sadiya da A'isha tace "yanzu ya dace naki aurar yaya aadil na auri kaninsa jawad?
Ko kuwa ya dace na auri aadil nabar jawad fitina ta kunno kai cikin zuri'arsu?
Ni pherty naga wani abu wai shi rayuwa"
Ajiyar zuciya Sadiya da A'isha suka yi atare "ina labarin gida,ina su mama da hawy kawarki?" Sadiya ta tambayeta
"Tun lokacin da na baro gida har yanzun nan da nake yi muku magana ban sake jin labarin gida ba"
"Hakane amma ni ina ganin auren jawad agareki shine alkairi" A'isha ta fada tana kallonsu
"Hmm A'isha kenan, Allah dai ya bamu mafita" pherty ta fada a hankali..
MARTABA TA 51-End
🏻: 👑 MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
51-52
~~~Hmmm A'isha kenan Allah dai ya bamu mafita pherty ta fada ahankali,
"Amma ni sai nake ganin yaya aadil yafi cancanta da aurenki pherty, duk da cewar nasan ke jawad kike so acikin ranki" Sadiya ta fada tana kallonta,
"Tabbas idan nace muku bana son jawad nayi karya, amma ahalin yanzu son da nake yiwa yaya aadil ya danne wanda nake yiwa jawad"
"Pherty nikuma idan nice ke jawad zan aura, saboda shi saurayi ne bashida mata, matashi mai karancin shekaru, zaku rayu sosai zaku ci soyayya, sannan kuma zaku more rayuwar aurenku fiyeda ace kin auri yaya aadil domin shi ko babu komai shekarunsa sunyi wa naki nisa, sannan kuma kinga yana da mata dole matarsa zata rinka kawo miki cikas fa" A'isha ta fada kamar zata saka kuka,
"A'a A'isha yaya aadil yayiwa pherty alkairi mai yawa kinga bai kamata tayi masa butulci ba, kuduba zancen nan nawa fa" Sadiya ta fada,
"Ya isa haka, time for prayer" pherty ta fada tana kokarin mikewa.
Daren ranar babu wacce tayi bacci acikinsu haka suka kwana suna hirar jawad da aadil har gari ya waye, kowaccensu shiryawa tayi suka fita lectures bayan sun yi breakfast,
Karfe 11 daidai pherty ta fito daga lecture din da tayi amma kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar tana cikin damuwa.
Hango jawad tayi tsaye jikin motarsa yana yi mata kallon kurulla, kallonsa ta danyi ta fara kokarin barin wurin da sauri yabi bayanta
"My queen" ya fada cikin tausashasshiyar murya,
Juyowa tayi ta kalleshi "jawad kayiwa Allah ka rabu dani dan Allah"
"Pherty kin san kuwa abinda kike fada?
Taya zan iya rabuwa dake?
Rabuwa dake tamkar rabuwa da numfashi nane pherty, kece rayuwata, wlhi bazan iya rabuwa dake ba"
Kallonsa ta tsaya yi ba tare da tace komai ba, yana sanye da riga da wando bakake abinku da farar fata sai kayan suka yi mutukar karbarsa,
Karasowa gabanta yayi ya tsaya,
"Pherty karki manta soyayyar mu, karki manta da jawad dinki pherty"
"Dama ta yaya zan iya mantawa da kai jawad?
Ai bazan manta dakai ba tunda kayi sanadiyyar rabuwata da iyayena, kayi sanadiyyar rashin lafiya agareni, kayi sanadiyyar rushewar MARTABA TA, sannan kayi sanadiyyar....!"
"Ya isa haka pherty, ya isa dan Allah, wai pherty so kike na mutu ne?
Eye?
Nace so kike na mutu?" Gabanta ya karasa
"Ki kasheni pherty, nace ki kasheni tunda bakya sona"
"Ni bazan kasheka ba amma dai abinda nasani shine bazan taba aurenka ba, ko maza sun kare a duniya jawad bazan taba aurenka ba"
"Kika ce ba zaki aure ni ba?".