← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jawad ka fita daga harkata rayuwar data faru can abaya tsakanina da kai ka barshi a matsayin mummunar kaddara kuma jarrabawa a gareni"
Kallonta yayi a raunane, "tayaya zan barki bayan zuciyata tana sonki?" Ya fada cikin harshen turanci
Dan murmushin takaici tayi "sanin kanka ne bazan taba aurenka ba har abada"
Cikin daga murya ya mayar mata da amsa "dole sai kin aureni kuwa, kuma wallahi bazan hakura dake ba"
Hankulan jama'a tuni suka daddawo Kansu saboda yanda jawad yayi maganar da karfi,
"You kid your self jawad, pherty will not marry you,idan mafarki kake to ka farka, dan bazan aureka ba ko ka zata na manta waye jawad?

To har yau ina sane da kai, kai macuci ne, mayaudari, maha'inci sannan babban mazinaci"
Da sauri A'isha ta jiyo ta kalleta, yayinda daliban wurin suka shiga mamakin wannan wulakanci da ake yiwa wannan kyakkyawan saurayi dan ya hadu tako wanne bangare,
Shi kuwa jawad wata kunya yaji ta rufeshi a wurin saboda yanda mata da maza suke turarreniyar kallonsa, wani bacin rai yaji ya ziyarci zuciyarsa,
"Marar tsoron Allah mai raba "yayan mutane da MARTABAR su..!"
Bata karasa maganar ba sakamakon janyeta da A'isha tayi suka nufi bayan wani hall shima jawad juyawa yayi ya shige motarsa ya fizgeta da karfi yabar wurin,
"Haba pherty wannan wulakancin da kike yiwa gayen nan yayi yawa,idan wani abu yayi miki ai ya kamata ace kin yafe masa, idan kuma ramawa kike son yi to bai kamata ki rama ta wannan hanyar ba domin kin ci mutuncinsa mutuka"
Cikin masifa pherty ta kalleta,"naci mituncin nasa idan yanada zuciya daga yau kar ya sake zuwa wurina" tana gama fadin haka ta juya ta nufi hostel ba tareda ta jira Aishan ba.

Bin bayanta A'isha tayi tana yi mata magana "ai so baya zama ki, wulakanci bai kamata ba" juyowa pherty tayi "sai kiyi tayi kuma"
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna fada har sukaje hostel, suna shiga daki suka samu Sadiya zaune tana shirya musu kayan sawarsu cikin akwatinansu
Nan suka ci gaba da fada har Sadiya tasa baki "indai gayen nan na rannan kika yiwa rashin mutunci gaskiya baki kyauta ba" nan pherty ta sake harzuka,kawai sai ganinta suka yi tasa kuka, harararta Sadiya tayi "ace mutum bashida wani aiki sai na kuka?"
"Um ai kin san gaskiya wuya ne da ita" A'isha ta fada lokacin da take kokarin tashi domin rage kayan jikinta, jin maganganunsu yaki karewa yasa pherty ta tashi tabar musu dakin ta tafi wani dakin.

Tun daga lokacin ta fita harkarsu har ana igobe zuwan yayanta, shi kansa bata fada masa ba, ganin tanata fushi yasa A'isha da Sadiya lallashinta har ta sauko suka koma harkokinsu kamar da amma basu sake tayar mata da batun jawad ba.
******
A bangaren jawad kuwa yaji bakin cikin wulakancin da pherty tayi masa acikin mutane domin har kwalla ya zubar amma yayi alqawarin jure duk wani wulakancinta har sai ya cika burinsa na mallakarsa a matsayin mata, daren ranar bai iya bacci ba saboda bacin rai.

Yau itace ranar da Aadil zaizo daga Abuja, tunda sassafe su pherty suka je kasuwa suka iyo cefanen da zasu yiwa Aadil kayan sauka,
Fried rice da hanta suka yi masa wadda tasha cabbage da su carrots da sauran tarkacen kayan lambu, ga lemon kwakwa da aka hada masa.

Karfe 12 daidai ya iso cikin makarantar, pherty ansha kwalliya cikin brown din doguwar riga mai tsananin kyau ga make up data tsarawa fuskarta tasha turarruka kala kala, kallonta suka yi kawayen nata "kinyi kyau yanmata" murmushi tayi "nagode, bari naje in yaso kwa kawo abincin ko?" Dariya Sadiya tayi "irin wannan kwalliyar kam bai kamata ki dauki kwanukan abinci ba" dariya suka yi su duka ita dai pherty juyawa tayi ta fita yayinda su kuma suka fara kokarin shisshiryawa.

A karkashin wata bishiya ta hangoshi ya shimfida katuwar darduma yana zaune cikin manyan kaya farar shadda goggagiya mai tsada yasha hula mai adon fari da baki hannunsa daure da agogon azurfa yana yin waya da alama da matarsa yake wayar,
Da murmushi a fuskarta ta karasa, shima murmushin yake yi, a hankali ta zauna can dan nesa dashi kadan tana jiran ya gama wayar, "yau ko zaki ganni sai dare dan daga nanma gidan Ummi zanje" haka taji ya fada lokacin da yake ajiye wayar.

Yana ajiyewa ya juyo ya fara aika mata da tsadadden murmushi, "pherty na" ya fada yana murmushi
"Yaya na sannu da zuwa, ya hanya?

Yaka sauka?"
"Alhamdulillah pherty na, antynki tana gaisheki tace kuma karki cika mun cikina da daddadan abincinta gudun kar nakasa cin nata abincin idan nakoma gida"
Murmushi tayi ta kalleshi "ai kuwa sai dai tayi hakuri dan yau cikinka iya abincina zai dauka, gobe sai ya dau nata"
Kallonta yayi cikin farin ciki "kinyi kyau pherty na" hannunta tasa ta rufe fuskarta tana murmushi
"Haka ma agida zaki rinka yimin wannan kunyar?"
Dakyar ta iya kallonsa, "ya aiki?

Ina fata yanmatan abuja basa kallon yayana?"
"Yayanki nakine keda antynki kawai, ki kwantar da hankalinki"
"A'a ka fada ne fa kawai" tafada kamar zatayi kuka
"Haba pherty na, yau bakya son wakar?"
"Ina so" tafada tana dariya
Daidai lokacin Sadiya da A'isha suka karaso dauke da kwanukan abinci a hannunsu
"Sannu da zuwa yaya Aadil" suka fada dukkaninsu atare tareda ajiye abincin a gabansa, bayan sun gaisa suka juya suka tafi,
Abincin ta zuzzuba masa ta tura masa gabansa,kallonta yayi "duk wannan abincin a cikina zan sa?"
"Eh mana yayana"
Murmushi yayi "pherty na kenan"
Kallonsa ta tsaya lokacin da yake cin abincin ita dai bata taba tunanin zata auri namiji mai mata ba sai gashi ashe mai mata ne mijinta, taso ta more rayuwarta da saurayi ashe da bazawari zata yi,
"Ya akayi ne kika tsaya kinata kallona"
Murmushi tayi babu komai kawai kayi min kyau ne shiyasa"
"Fadi gaskiya dai"
Hira suka yita yi har ya gama cin abinci yayi alwala ya tafi sallar juma'a ita kuma ta koma hostel ta sake wani sabon wankan ta sake shiga cikin wata atamfa kalar ruwan kwai tasha dauri su A'isha da Sadiya sai tsokanarta suke, gurin Aadil ta sake komawa bayan ya dawo daga masallaci,
"Yau dai zaki barni natafi kuwa?" Ya fada yana kallonta "naga sai kyau kiketa zubawa"
"Yaya banda zolaya dai"
"Babu wani zolaya" ya fada yana yi mata murmushi.

Har yamma suna tare sai wurin 5 sannan ya tafi bayan ya firfito mata da shopping din da ya siyo musu, kaya kamar a shago kama tun daga kayan makulashe har zuwa turarruka da hadaddun mayuka, yana fita daga school dinsu pherty gidansu ya wuce wato gidan iyayensa.

Lokacin da ya shiga gidan nasu mahaifiyarsa da kaninsa suna zaune a tsararren falon ummin tasu, cikeda fara'a ummin ta fara yi masa sannu da zuwa amma shi dan uwan nasa kau da kai yayi tamkar bai ganshi ba,
Kusa da ummin yaje ya zauna "sannu da hutawa Ummi".

"Yawwa Aadil barka da sauka" da sauri ta tashi ta nufi kitchen domin hado masa kayan motsa baki,tashi yayi ya nufi inda kanin nasa yake ya mika masa hannu "Assalamu Alaikum ya Aki" "wassalam" jawad ya fada tareda dauke kansa ya tashi ya fice daga cikin falon ba tareda ya bashi hannu sunyi musabaha ba, bin bayansa da kallo Aadil yayi wannan wacce irin kaddara ce take kokarin kutso kai tsakaninsa da dan uwansa, yana nan zaune Ummi ta dawo dauke da faranti wanda ta doro kayan motsa baki a kai, akan dan table din gabansa ta ajiye, nan ta zauna ta fara hira da dan nata har tsawon wani lokaci daga bisani yayi sallama da ita ya nufi sashen mahaifin nasa.

Lokacin da yafito ya shiga part din abbunsu a lokacin shi kuma jawad yana kokarin fitowa, wata harara jawad ya aika masa da ita ya dauke kansa ya wuce, wucewa ciki Aadil yayi yanata jajanta wannan lamarin acikin zuciyarsa, a babban falon mahaifin nasa yayi ya tarar dashi yana kishingide yana wuridi da casbaha a hannunsa,
Da sauri yaje ya duka a gaban mahaifin nasa bayan sun gaisa ne yake sanar masa da cewa yana so zai kara aure,kallonsa mahaifin nasa yayi "aure Aadil?

Lafiya zaka kara aure?" "Lfy lau abbu, kawai dai akwai dalili ne, ina son taimakon yarinyar ne abbu, domin inada halin iya rike mata hudu tunda Allah ya bani arzikin da zan iya yin haka shiyasa nake son yin amfani da wannan damar wurin taimakon yarinyar" kada kai mahaifin nashi yayi "Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya albarkaci rayuwarka, dama nayi tunanin ko dan saboda matarka bata haihu bane shiyasa zaka kara aure to amma tunda ba haka bane to Allah ya tabbatar da alkairi"
"Amin abbu"
"Nan da yaushe zaka kara auren?"
"Abbu nan da watanni hudu"
"To Allah ya kaimu"
"Amin abbu,a huta lfy"
Tashi yayi ya fita ya koma yayiwa mahaifiyarsa sallama ya fito ya nufi gidansa inda matarsa ke zaman jiransa.

Koda yaje ya samu Salima cikin kyakkyawar shiga tasha kwalliya tayi kyau sosai, nan ta tarbeshi cikeda kisisina, wanka ta kaishi yayi ta shiryashi cikin kayan shan iska.

Bayan wani dogon lokacine Aadil ya shafo gashin kanta yace "Salima kiyi hakuri da abinda zakiji daga gareni"
Dam gabanta taji ya fadi amma sai ta daure tace ina jinka
"Salima bikina da phertyma nan da watanni hudu masu zuwa za ayishi, dazun nan muka gama maganar da abbu"
Duk da hankalinta ya tashi amma sai ta dake tayi murmushi ta riko hannunsa "Allah ya nuna mana lokacin, Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu"
Hannunta ya damke "amin baby, hakika ina jin dadin yanda kuke mu'amula keda pherty tun kafin tashigo gidan"
"Babu komai dear ita kishiya ai yar uwace"
"Allah yayi miki albarka, nikuma nayi alaawarin kulawa dake har karshen rayuwata".
Chapter 4 · 0% Book details