← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 27

Sashe 12

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi mai kunshe da damuwa,
"Wallahi kuma ni zaki aura saboda nine nake sonki, aadil ba sonki yake ba domin nafiki sanin ko waye shi, pherty wallahi ni zan aureki mutukar ina numfashi" ya karasa maganar daidai lokacin da hawaye yake bin kumatunsa,
"Kaga malam idan kai baka da abinyi to ni ina dashi dan haka sai anjima" juyawa tayi da niyyar tafiya, cikin sauri ya janyo gefen mayafinta, tana jiyowa ta daga hannu da niyyar kai masa mari amma sai ta fasa,
"Meyasa kika fasa?

Ki mare ni mana pherty, ki mareni amma wata rana zakiji kunya saboda kin mari mijinki,sannan ki ajiye acikin ranki wlhi ni jawad nine mijinki, ki saka wannan acikin zuciyarki"
Juyawa tayi tabar masa wurin cikin tashin hankali, juyawa jawad yayi ya koma ya dauki motarsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin makarantar, daidai bakin gate din fita yaga motar aadil tana kokarin shigowa, glass din motarsa ya sauke ya dallawa aadil harara ya wuce, shima aadil din bin motar jawad din yayi da harara ya wuce ciki.

A inda ya saba tsayawa yau ma anan ya tsayawa yana jiran gimbiyar tasa, yana zaune ya hangota tana tahowa cikin tafiyarta ta nutsuwa, tana sanye da jar atamfa ta yafa jan mayafi,tausayinta yaji acikin zuciyarta saboda tunowa da yayi da lalurar da take tare da ita,
"Assalamu alaikum yayana" ta fada tana murmushi
"Wa alaikissalam pherty na, amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida" ya fada cikeda zolaya
"A'a yaya bazan ma kashe muku da ba"
"To ai kin isa ne pherty na"
Murmushi ta dan yi bata yi magana ba,
"Kin San dalilin zuwana yanzu?" Ya fada yana kallonta
"A'a sai ka fada yayana"
"Zuwa nayi naji wanne irin gado kike so?

Royal bed kikeso ko Italian bed, ko kuma dubai bed?"
Gabanta taji ya fadi tab yanzu zan kwana gado daya da yaya aadil watarana?

Tambayar da tayiwa kanta kenan acikin zuciyarta
"Baki fada min ba, wanne kike so?

Ina son zan bayar ne a siyo miki kayan dakin"
"Yaya ni duk wanda ya samu ina so" ta fada cikeda kunya
"To shikenan duk guda ukun zan siyo miki, ke ai yar gatace"
"Yaya sunyi yawa, dayanma ya isa"
"No,guda uku zan yi miki pherty na"
Murmushi ta kakaro dakyar tayi , "nagode yayana" ta fada idonta cikeda kwalla
"Kar kiyi kuka pherty na, kinfi haka a wurina"
"Nagode yaya".

Bayan sun dan taba hira ne ya yi mata sallama ya tafi ita kuma ta koma hostel.
******
Gudu aosai jawad yayi daga makarantar su pherty zuwa gidansu, kai tsaye side dinshi ya wuce, kansa ya dafe tare da fadawa saman kujera domin jin kan nasa yake kamar zai rabe gida biyu dan tsabar zugin da yake masa, zunbur kuma ya tashi zaune
"What?

Impossible, Xarah hakan ba zai taba faruwa ba" ya fada shi kadai kamar wani zautacce, tashi yayi ya fito ya nufi side din Ummi, yana zuwa ya tarar da ummin zaune ga tulin akwatuna masu kyau da tsada a gabanta, kallon akwatunan yayi cikin faduwar gaba, guda bakwai ne kalarsu pink colour,
Zama yayi dabas a gaban Ummi, "Ummi wannan kayan fa?" Ya fada cikin dar dar
"Kayan auren aadil ne da aka hado masa, kasan bikin nashi ya taho saura lokuta kadan ya rage"
Kafin yayi wata magana aadil ya bude kofa ya shigo, tashi jawad yayi ya tunkareshi yana zuwa yafara kokarin cin kwalarsa
"Sai yau na yarda kai ba dan uwana bane, ayau nagane cewa kai ba jinina bane, ko kadan bamu hada jini dakai ba aadil, kai ba dan uwana bane domin shi dan uwa yana taimakon dan uwansa ne a duk lokacin da ya bukaci taimako, ba irinka ba mai son zuciya da son kansa ba, ba irinka ba mai kokarin raba naka dan uwan da tashi rayuwar ba"
Wani mugun kallo aadil ya watsa masa sannan ya fara kokarin banbare hannun jawad din daga rikon da yayiwa rigarsa
"gaka nan mai son zuciya mai son kansa, yarinyar da kagama wulakantawa a baya sai yanzu zaka dawo kace ita kake so saboda kaga yanzu ta zama cikakkiyar mutum, to wlhi baka isaba ko bazan auri pherty ba bazan taba barinta ta aureka ba, gara nabawa bare aurenta akan nabaka, banza mayaudari kawai"
Ai jawad najin haka ya sake tunzura tare da fara wujijjiga wiyan rigar dake jikin aadil, da sauri Ummi ta taso ta fara kokarin rabasu,
"Kai jawad sa'anka ne?

Cikashi, ka cikashi nace" ta fada cikin harshen fullanci
"Ki kyaleshi Ummi na koya masa hankali yau" jawad ya fada cikin karaji
"Idan kai baka koya min ba to ni zan koya maka, dama can kawai saurara maka nake yi" aadil ya fada shima a harzuke
Nan suka kaure da fada Ummi tayi tayi ta rabasu ta kasa, tun suna yi a falo har suka karasa dining area,sai naushi suke kaiwa junansu, wani wawan naushi aadil ya kaiwa jawad cikin sa'a ya sameshi a fuska, take jini ya fara fita daga hancin jawad
"Haba aadil kashe kanku zakuyi?

Akan me?" Kuka Ummi ta fara, da sauri ya saki jawad ya nufi Ummi shikuwa jawad durkusawa yayi agun hancinsa yana ta zubar da jini.

Ummi A'isha
[5/10, 9:04 PM] Ummi A'isha🏻: [5/10, 9:02 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA 👑
Na
UMMI A'ISHA
53-55
~~~Da sauri aadil ya saki jawad ya nufi wurin Ummi, "aadil kashe kanku za kuyi?

Ko lokacin da kuke yara kanana ba kuyi kuruciyar fada ba kai da dan uwanka, sai yanzu da kuka girma kowa ya mallaki hankalin kansa" Ummi tafada tana kuka,
"Yi hakuri Ummi mun daina ba zamu sake ba" aadil ya fada kamar zaisa kukan shima,
Mikewa ummi tayi ta nufi wurin jawad wanda duk ya babbata wurin da jini jini ne yake fita a hancinsa sosai, hannunsa ummi taja ta nufi dakinta da shi daidai lokacin mahaifinsu ya shigo, ganin abinda ya faru ya sashi fara tambayar meke faruwa, ko kadan aadil bai iya bude bakinsa ba yana nan tsaye gaban dining area din yana ganin yadda jinin jawad ya zuba da yawa,
Jim kadan sai ga ummi tafito itada jawad din ta wanko masa fuskarsa amma har a lokacin jinin yana fita kadan kadan,
"Hajiya Fatima wai me ya faru ne?" Mahaifinsu ya tambaya cikeda mamaki
"Kagansu nan fada sukayi sai kace kananan yara gashi nan harda zubar da jini" Ummi tafada fuskarta cikeda hawaye,
Cikin mamaki mahaifin nasu ya dubi aadil "aadil fada?

Kai da kaninka?

Duk duniya kanada wanda yafi shi ne?

To yanzu da ace ka haihu yaronka ya girma da agabansa zaka yi haka?

Aadil kai fa ba yaro bane, shekarunka talatin da wani abu, ace har yanzu ba kayi hankalin da zaka rike dan uwanka ba?

Meya hadaku?

Tambayarka nake meya hadaku fada?"
Shiru sukayi daga aadil din har jawad babu wanda yayi magana,
"Ba zaku fada min abunda ya hadaku fadan ba sai na sassaba muku?" Mahaifin nasu ya sake fada cikin fada,
"Daddy babu komai" aadil ya fada kansa a sunkuye
"Kai jawad me ya hadaku"
"Dady babu komai" jawad ya fada shima
"Kaji zancen banza, babu komai kawai zaku kama fada harda fasa jikin juna?"
"Alhaji akwai abinda ya hada su dan daga jin musayar yawun da suka yi nasan fadan nasu akan yarinyar da aadil din zai aura ne" ummi ta fada tana kallonsu
"Meya samu yarinyar?

Akanta suke fadan?

To in babu dama ahakura da auren indai zai jawo fitina a tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya ya fice daga cikin falon,
Yana fita ummi ta kallesu "ban taba ganin sakarkaru irinku ba, fada akan mace?

Cikinku daya fa ko kun manta?

Kai aadil yanzu ko wani kagani zai cuci dan uwanka ai bai kamata ka barshi ba balle kai da kanka, sanin kanka ne tun jawad yana karami ba a dukansa a fuska dan ko marinsa akayi hancinsa ya rinka jini kenan amma shine dan rashin tausayi yanzu kazo ka dake shi a hancinsa"
Dukar da kai aadil yayi sannan yace "ummi kiyi hakuri,hakan ba zai sake faruwa ba"
"Shikenan kaje maganar ta wuce" ummi tafada tareda ficewa daga cikin falon itama,
Tana fita jawad ya fara harararsa "wlhi har yanzu ban hakura da pherty ba kuma yanzune ma nasake jin sonta acikin raina"
Kallo aadil ya bishi dashi "kaje ka aureta ga wurin nan" yana gama fadin haka ya juya ya fice daga falon.
*******
Bayan faruwar haka da kwana biyu aadil ya shirya yaje makarantar su pherty, ita sam bata san abinda ya faruba, bayan ya fito sun gaisa ne dai take ganin kamar yana cikin damuwa,
"Pherty na wani wuri za muje, kije ki debo kayanki kamar kala biyar dan sai kinyi 2 weeks sannan zaki dawo dan haka sai kiyiwa su Sadiya da Aisha sallama"
"To yaya" haka kawai tace ta juya ta koma hostel, tana zuwa ta dauki trolley ta fara hada kayanta aciki tana fadawa su Sadiya zasuyi tafiya da yaya aadil,
Bayan ta gama shirya kayanta ne suka rakata har wurin motar aadil suka yi musu Allah ya kiyaye hanya, kallonsa ta juya tayi lokacin da suka fara tafiya
"Yayana meke damunka ne?" Tafada tana kallonsa
"Pherty na lfy lau nake kawai dai bana jin dadin jikina ne"
Murmushi tayi sannan ta sake kallonsa "to yanzu dai ina zaka kaini?"
Murmushi shima yayi "gidan sayar da mutane"
"Ah yaya yaushe ka fara yanka kai?"
"Ai nadade ina yanke kan raguna pherty nace bata saniba"
Dariya ta fara harda buga kafa amma sai dariyarta ta tsaya ganin sun nufi hanyar kauyensu,
"Yaya aadil wai ina muka nufa?"
"Gidanku" ya fada agajarce
Shiru tayi bata iya cemasa komai ba illa tunani da tafara yi, yau shekararta hudu rabonta da garinsu, komai ya canja na tsarin garin tun daga kan tituna har zuwa kan gine ginen dake cikin garin.
Chapter 12 · 0% Book details