← Book details Martabata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Martabata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar juma'a da misalin karfe 2 jama'a suka taru domin shaida daurin auren pherty, bayan karfe biyu da rabi suna zazzaune agida adakin mama amarya tasha kyau saboda gyaran jikin da kunshin da akayi mata, wayar yaya aadil ce tashigo tana dauka yace tazo yana soron gidan, tashi tayi ta fita ta sameshi yasha farar shadda da jar hula wato kwankwasiyya sai kamshi yake
"Sannu yaya aadil"
"Yawwa pherty sannunki ya hidima?"
Murmushi tayi bata amsa ba,
"Pherty ayau ina mai farin cikin sanar dake cewa na cika miki burinki na aura miki wanda kike so"
Kallonsa tayi "ban ganeba yaya aadil"
"Ina nufin yau kin zama matar jawad"
Kwalalo ido tayi "haba yaya gaskiya ni bana sonsa kai nake so ni gaskiya bazan zauna dashi ba, awarware auren nan cikin gaggawa"
"Ni ina sonsa saboda dan uwana ne, pherty kenan nasan jawad kike so ni kawai kina yimin alkunya ne saboda abunda nayi miki na taimako, ina so kiyiwa jawad biyayya ki kulashi kamar yadda zaki kulani sannan ki sani jawad yana tsananin sonki fiyeda tunanin mai tunani, yanzu jirgi zanje nabi nida Salima domin gano halin da yake ciki sannan kuma nayi masa albishir da kin zama mallakinsa, pherty jawad dan uwana ne uwa daya uba daya duk duniya banida kamarsa tun Muna yara mun taso da son junanmu nasan abunda yake so nasan wanda baya so, kayan dakinki suna nan zuwa anjima nabar komai a hannun baba maigadi shine zaiyi muku jagora zuwa gidanki, sannan ina so kici gaba da kallona a matsayin yayanki ba yayan mijinki ba kamar yadda kike kallona ada, ko wani abu jawad yayi miki kar ki kunyar sanar dani, ban yarda ki kai kararsa wurin kowa ba sai wurina, ni nayi masa walinci nabada sadakinki Dubu Dari biyu da hamsin, Allah ya sanya albarka acikin aurenku, Allah ya baku zuri'a dayyaba"
Wasu hawaye ne suka fara bin kumatunta
"Nagode yaya aadil, hakika kai wani mutum ne mai mutukar muhimmanci a rayuwata nagode yaya aadil Allah ya saka maka da mafificin alkairi"
"Pherty tun farko nasan jawad kike so, kamar yadda shima ke yake so, Allah ya barku tare"
Yana fadin haka ya juya ya fita ya nufi airport inda Salima ke jiransa domin jirginsu ya kusa tashi.

Gida ta juya ta koma tana ta kuka "zaki fara sana'ar taki ne?" Sadiya ta fada tana kallonta
"Kibarta kukan farin ciki ne" hawy ta fada tana dariya
"An auri jawad ai dole ayi kukan farin ciki" inji A'isha domin dama su sun san da jawad aka daura mata aure itace bata sani ba nan suka shiga tsokanarta ita dai sai kuka take.
******
Misalin karfe 4 na yamma su aadil suka sauka akasar chairo, asibitin da su jawad suke suka nufa shida salima, lokacin da suka shiga dakin da jawad din yake yana kwance idanuwansa a rufe, inda yake aadil ya karasa ya kama hannunsa
"Jawad bude idonka kaji, ka bude idonka, pherty ta zama matarka, wlhi dama ban taba sonta ba kamar yadda itama bata sona kai take so, ni kawai taimakon da nayi mata ne yasa take girmama ni, haba dan uwana taya zan so abunda kake so, wlhi duk abinda ya faru nayi shine domin na kubutar dakai daga rasa abunda kakeso domin ba dan na rike maka pherty ba da tuni ta shiga uwa duniya kuma ba lallai ka iya gano inda take ba gashi kana fama da ciwon sonta, sannan ba don na nuna ina sonta ba da tuni yanzu wani ya gama siye zuciyarta kuma koda ka koma ba zata saurareka ba, duk taimakon da nayi mata nayi shine saboda kai dan uwana, ka saki ranka wlhi ban taba son abunda kake so ba"
Bude ido jawad yayi, idanuwansa cikeda kwalla, sake damke hannun aadil yayi,
"Meyasa baka aureta ba?

Kai kafi cancanta da aurenta saboda kaine ka taimaketa a lokacin da take bukatar taimako,Kaine ka zaba gatanta a lokacin da bata da gata, nikuwa ban yi mata komai ba a rayuwarta face zalunci shiyasa Allah ya kamani"
"Kayi shiru dan uwana kar su Ummi suji, kayi hakuri ka rigada ka zama ango amma wani hanzari ba gudu ba, tanada matsala a mararta, buguwar da tayi lokacin da tasamu miscarriage dinnan taji ciwo a gefen mararta"
Daga kai jawad yayi yana hawaye "Allah ya saka maka da alkairi dan uwana, nagode nagode, banida bakin yi maka godiya"
Cikin kankanin lokaci jawad har ya fara samun sauki, jikinsa ya danyi kyau gashi kumburin nan na fuskarsa ya sabe domin jininsa ya sauka ya koma normal, ciwon zuciyar ma tuni ya lafa sai dai har yau baiji muryar amarya ba.
******
A Gida Nigeria kuwa an gama gabatar da shagulgulan biki lafiya, anyi yini anyi walima sannan kawayen amarya sun shirya sisters night, mama kuwa ta dage ta gyara yarta tsaf ciki da waje, yau ake sa ran kaiwa amarya gidanta.

Misalin karfe takwas na dare aka dauketa akayi cikin gombe da ita bayan iyayenta sunyi mata nasiha daidai gwargwado, wani tamfatsetsen gida aka kaita wanda indai bata manta ba to nanne gidan da jawad ya kaita, amma an sake gyara gidan an zuba masa sababbin funitures komai blue, hatta gadajen blue ne, dakuna uku da faluka biyu ga dining area da kitchen da store aciki, anan kawayen nata zasu kwana tunda ango baya nan.

"Masha Allah gida yayi kyau Allah ya kawo yan uku" inji hawy
"Yan Hudu dai ya kamata ki rokar musu" Sadiya ta fada tana dariya
"Kai duk ba wannan ba gaskiya ba zaku kwana akan gadon ma'aurata ba kuzo mu koma falo mu kwanta acan" A'isha ta fada tana kifta musu ido
Ita dai pherty tashi tayi ta shige toilet ba tare da tace musu uffan ba.

Ummi A'isha🏻
[5/12, 11:48 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑
Na
UMMI A'ISHA
61-63
~~~ Kwana suka yi suna hira sai tsokanarta su A'isha suke, sai da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci.

Kwanansu biyu sannan suka koma sch suka barta da iya hawy kawai, tana kuka suna kuka haka suka rabu dasu Sadiya, ranar da suka tafi da yamma suna zaune ita da hawy a falo jawad ya kirata a waya kamar ba zata dauka ba sai ta dauka
"My queen" ya fada a hankali
"Ina jinka" tafada cikin gatsali
"Kinji yadda al'amari ya sauya ko?"
"Eh naji amma ai ni dole aka yi min domin ba sonka nake ba"
Harara hawy ta wurga mata itama ta rama,
Shiru yayi ya rasa abin da zai ce mata can ya daure yace
"Ko jikin nawa ba zaki tambaya ba Queen?"
"Banida alaka da shine shiyasa kaji ban tambaya ba"
"Ok to nagode sai munyi waya"
Kashe wayar tayi sai kuma taja tsaki "mtsww"
"Mijin naki kike yiwa tsaki pherty?

Wlhi kiyi ahankali tom" hawy ta fada tana hararta,
"Anki ayi ahankalin kuma anyi masa tsakin sai me?"
"Sai ya gyara miki zama idan ya dawo"
"Ya gyara din"
"Yarinya kenan, round biyu zai yi miki kwarara zaki shiga hankalinki"
"Yayi round goma ba biyu ba" ta fada tare da ficewa daga bedroom din ta nufi dayan.

Kwanansu biyar tareda hawy agidan amma kullum sai sunyi fada akan jawad da haka har pherty ta fara shirin komawa sch aranar itama hawy ta koma gombe.

Kayanta ta harhada cikin trolley ta nufi sch nan kawayen nata suka fara yimata oyoyo,tunda ta koma kuma ta watsar da jawad duk da cewar tasan tana sonsa amma haka take basarwa watarana ma da saninta zata kashe wayarta dan kar ya kirata ya sameta, sai dai har lokacin basu yi waya da aadil ba amma takanyi masa text ta gaida shi lokaci lokaci.
******
Acan kasar chairo kuwa tuni jikin jawad yayi sauki garau kamar bai taba jinya ba har an bashi sallama nan suka fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria amma shi aadil da Salima zasu wuce kasar London domin hutawa to sai muce adawo lafiya.

Ranar asabar da yamma ranar su jawad suka sauka a Nigeria yayi fresh yayi kyau saboda yanzu bashida wata damuwa gashi yana samun kulawa sosai wurin ummi sai dai har yau su Ummi basu san dalilin aadil nakin auren pherty ba sun rasa dalilinsa na aurawa jawad phertyn.

Washe garin ranar da suka dawo Sadiya da A'isha suka matsawa pherty kan lallai dole sai ta shirya sunje duba jawad, fada sukayi sosai kafin ta yarda ta shirya cikin lace blue ta yafa mayafinta kashka shima blue,sarka ta saka silver mai kyau tasa farin takalmi flat,fita suka yi suka nufi unguwarsu jawad din domin yana gidan ummi, keke napep suka hau har unguwar.

Kallon gidan take tayi tana tuna ranar da tazo lokacin da jawad yayi mata ciki,
Part din ummi suka shiga suka sameta zaune tana duba wani littafi idonta sanye da medical glass, pherty tana baya Sadiya agaba, sai A'isha, sallama sukayi ta dago ta amsa musu,
"A'a pherty sannunku da zuwa" tafada cikin hausarta wadda bata fita sosai,
Zama suka yi ita kuma tafita taje da kanta ta hado musu kayan marmari ta kawo musu, pherty dai bata iya hada ido da ita ba kanta yana sunkuye suka gaisa,
"Jiya ai munje gidan naku munyi godiya, angama biki lafiya ko?"
"Lafiya lau" tafada cikeda kunya
Zama suka yi shiru har na yan mintuna sai daga baya su sadiya suka tambayi jawad tace yana side dinsa tun dazu yafita, tashi suka yi suka nufi side din nasa.
Chapter 15 · 0% Book details